Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan taurari masu ban sha'awa da wani dalibi ya dauka
Wani ɗalibi ɗan ƙasar Scotland ya ƙaddamar da hotunan sararin samaniya da ya ɗauka ta hanyar amfani da na'urar hangen nesa a bayan lambunsa.
Bryan Shaw, dalibi a Jami'ar West of Scotland, ya shafe sa'o'i da yawa yana kallon taurari da tattara hotuna da bidiyo don wani shiri na ƙarshen shekara.
Dalibin da ke ajin karatu na hudu ya sami nasarar ɗaukar cikakkun hotuna na gungun taurari da waɗanda ke da haske a shekaru da yawa, kamar Pleiades, Andromeda da Orion Nebula.
Mr Shaw - wanda ya fara ɗaukar hotunan sararin samaniya a bara - yakan sadaukar da darensa kan burinsa, na ɗaukar hotunan taurari a wajen gidansa da ke c New Cumnock, gabashin Ayrshire.
Ya ce: "Yana cin lokaci, amma ina matuƙar so wannan. Ina shirin samun babbar na'urar hangen nesa domin faɗaɗa ilimi na, kuma don na iya ɗaukar wasu abubuwan da ba zan iya ɗauka ba a yanzu."
Ina son na ɗauki hotunan na duniyoyi da wata - abin da nake tsarawa kenan.
"Babban burina shi ne na ɗauki taurarin nebula."
Dr Sheona Urquhart, malamin kimiya a Open University, ya shaida wa BBC cewa hotunan da aka ɗauka "abubuwa ne da ke nuna yanayin duniyarmu."
"Abin da nake tunani ya fi ban sha'awa shi ne yadda ya ba sai ka je kasa da kasa ba, ka samu hotuna masu ban sha'awa - daga gida za ka iya samun abin da kake so," in ji shi.
Dukkanin hotuna haƙƙin mallakar Bryan Shaw ne.