Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya faru a Karbala lokacin da aka kashe Hussaini bn Ali?
- Marubuci, Ahmed Abdullah
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A ranar 10 ga Muharram na kowace shekara, miliyoyin mabiya Shi'a a faɗin duniya kan tuna da labarin abin da ya faru na kisan jikan Annabi Muhahammad - Hussaini bn Ali.
Lamarin ya faru ne a wani wuri da ake kira Karbala a shekarar miladiyya 680, wato kimanin shekara 1,300 da suka gabata.
Don haka ne mabiya shi'a ke taruwa a kowace ranar 10 ga watan Muharram domin tunawa da baƙin cikin abin da ya faru na kisan Hussaini.
Suna ganin abin da ya faru a matsayin zalunci ga iyalan Annabi Muhammad (SAW).
Don haka ne suke tunawa da ranar Ashura wato 10 ga watan Muharram ta hanyar yin abubuwa na nuna alhini da baƙin cikin abin da ya faru a Karbala.
Mene ne ya faru a Karbala?
Domin fahimtar haƙiƙanin abin da ya faru a Karbala, akwai buƙatar komawa tarihin Musulunci da yadda shugabancin Musulmi ya biyo bayan wafatin Manzon Allah.
Malaman tarihi sun ce bayan rasuwar Annabi Muhammad (SAW), saɓani ya kunno kai tsakanin al'ummar Musulmi dangane da batun wanda zai gaje shi a jagoranci.
Manyan Sahabbansa da ake yi wa laƙabi da ''Khulafa'urrashidin'' (Abubakar, Umar Usman da Aliyu), sun jagoranci Musulmi kowane, bayan mutuwar wani.
Duniyar Musulunci ta shiga wani gagarumin rikici da aka fi sani da ''Babbar Fitna" a ƙarshen shugabancin Kalifa na ƙarshe wato Aliyu bn Abi-Ɗalib, mahaifin Hussani.
Bayan rasuwar Aliyu an samu saɓani kan wanda zai gaje shi, inda a Madina aka naɗa ɗansa Hassan bn Aliyu, wato ɗan'uwa ga Hussaini.
To sai dai naɗin nasa ya gamu da turjiyya daga wasu sahabbai, musamman da suke Sham, inda suka naɗa Mu'awiya ibn Abi Sufyan a matsayin jagoran Musulumai mai shalkwata a Damascus.
Samun shugabannin biyu a lokaci guda ya riƙa haifar da ruɗani tsakanin al'ummar Musulmi na wancan lokaci, lamarin da ya sa Hassan bn Ali ya yanke shawarar sauka daga mulki ya bar wa Mu'awiya domin samun maslahar al'umma.
Wasu litattafan tarihi sun bayyana cewa Hassan ya sauka ne bayan wata yarjejeniya da aka cimma cewa idan Mu'awiya ya rasu za a riƙa zaɓen magajinsa ne maimakon gado.
To sai dai wasu malaman tarihi na cewa a lokacin mulkinsa, Mu'ayiwa ya yi duk mai yiwuwa don ganin ɗansa Yazid Bin Mu'awiya ya gaje shi, inda har ya naɗa shi matsayin Yarima mai jiran gado.
Wannan matsayi da Mu'ayiwa ya ɗauka bai yi wa wasu da dama cikin manyan sahabbai daɗi ba, ciki har da Hussaini bn Ali.
Bayan rasuwar Mu'awiya sai aka naɗa ɗansa, Yazid matsayin jagoran Musulmai, lamarin da bai yi wa Hussaini bn Ali da wasu daga cikin sahabbai daɗi ba, abin da kuma ya sa ya ƙi yi wa Yazid mubaya'a.
Malaman tarihi sun ce Hussaini ya ƙi yin mubaya'a ne saboda yadda Yazid ya zama shugaba ya saɓa da yarjejeniyar da aka cimma, kuma yin mubaya'a gare shi tamkar amincewa ne da abin da aka yi, wanda yake ganin sauka daga ƙa'idar da aka cimma NE.
A wancan lokaci sahabbai da dama daga Kufa da a yanzu ake kira Iraqi, sun riƙa aika wa Hussaini wasiƙu cewa ya je can, domin su mara masa baya.
Don haka ne Hussaini ya fice daga Makka tare da iyalinsa da wasu sahabbai marasa yawa, domin yin tafiyar mai cike da hatsari, amma a gare shi hakan ne ya dace.
Sai dai a kan hanyarsu ta zuwa Kufa, mayaƙan Yazid sun tare su don gudun kada su isa Kufa su kuma zame masa barazana.
Lamarin da ya tilasta musu yin zango a wata hamada da ake kira ''Karbala'' a kusa da tekun Euphrates.
Malamai sun ce a nan ne aka yi musu ƙawanya shi da sahabbansa da iyalansa, lamarin da ya haifar da ƙazamin yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.
A ranar 10 ga watan Muharram ne aka gwabza yaƙin, kuma kasancewar ɓangaren Hussaini ba su da yawa idan aka kwatanta da na ɗaya ɓangaren, an ci nasara a kansu.
An kashe Hussaini da wasu da dama cikin mutanen da ya taho da su, ciki har da iyalansa.
Haka kuma a yaƙin an kama wasu mata da ƙananan yara da ke cikin tawagar a matsayin bayi.
Me ƴan Shi'a ke yi na tausaya wa Hussaini?
A kowace ranar Ashura, mabiya Shi'a kan taru a wasu wurare da suke kira ''Majalisun Imam Hussaini''.
A waɗannan majalisun sukan riƙa tunawa da bayar da labarin abubuwan baƙin ciki da suka faru ga Hussaini bn Ali a Karbala.
Sukan yi kuka domin nuna tausayawa ga Hussani da iyalansa.
Don haka ne suke yin kuka da bugun ƙirji tare da rera waƙoƙin alhini da tunawa da Hussaini.
Sukan kuma rika ɗaga baƙaƙen tutoci a kan tituna, da kuma yin tattakin alhini yayin da suke tafiya tare suna rera waƙoƙin alhini.