Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Pogba, Rudiger, Jesus, Azpilicueta, Neymar, Messi, Nunez

Pogba
An wallafa

Barcelona tana sake yunkurin daukar dan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba, mai shekara 29, bayan kungiyar da ke Sifaniya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dakar nauyin wasu tallace-tallace masu tsoka. Dan wasan dan kasar Faransa zai kasance ba si da kulob idan kwantaraginsa ya kare a Old Trafford a bazara. (Star)

Dan wasan bayan Jamus Antonio Rudiger, wanda kwangilarsa za ta kare a Chelsea a bazara, ya amince ya tafi Juventus domin yin kakar wasa hudu. (La Gazzetta dello Sport, via Mail)

Juventus na farautar dan wasan Manchester City dan kasar Brazil s Gabriel Jesus, mai shekara 24, idan kungiyar da ke Igila ta sayi dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21, daga Borussia Dortmund.(Star)

Newcastle United na sha'awar daukar dan wasan Brazil mai shekara 30, Neymar, wanda kwangilarsa da Paris St-Germain za ta kare a 2025. (Fichajes, via Teamtalk)

Kocin Barcelona Xavi ya ce "a ko da yaushe muna maraba" da tsohon abokinsa Lionel Messi, 3mai shekara 34, idan ya dawo Nou Camp. Dan wasan na kasar Argentina ya bar Barca zuwa PSG a bazarar da ta gabata. (Marca)

Messi ba shi da niyyar barin PSG kuma yana da tabbacin kammala wa'adin kwangilarsa ta shekara biyu a kungiyar ta Faransa. (Marca)

Dan wasan Chelsea Cesar Azpilicueta ya amince da fatar-baki cewa zai tafi Barcelona kuma kuma sa ran za a kammala yarjejeniyar tafiyar dan wasan mai shekara 32 a bazara, (Football Insider)

Wakilin dan wasan tsakiyar Chelsea Jorginho ya ce wata rana dan kwallon na kasar Italiya mai shekara 30 zai koma Serie A. (Mirror)

Manchester United tana duba yiwuwar dakar dan kasar Morocco da ke murza leda a Sevilla Yassine Bounou, mai shekara 30. (Mirror)

Manchester United na son daukar dan wasan Turkiya mai shekara 24 Merih Demiral, wanda ke zaman aro a Atalanta daga Juventus.(Fanatik)

Atletico Madrid ta zama kan gaba da ke fatan daukar dan wasan Uruguay, Darwin Nunez, wanda ya bai wa Benfica gudunmuwar da ta kai karawar dab da na kusa da na karshe a Champions League. (Fichajes - in Spanish)

Atletico Madrid ta mika tayin sayen Sergi Roberto, wanda ke shirin barin Barcelona, wanda kwantiraginsa da Barcelona zai karkare a karshen kakar nan. (Sport - in Spanish)

Leeds United tana da tabbacin za ta tsawaita yarjejeniyar Luke Ayling, wadda kwantiraginsa zai kare a kungiyar a karshen kakar 2023. (Football Insider)

Newcastle United za ta amince dan kwallon Ireland ta Arewa, mai tsaron baya, Jamal Lewis za ta bari ya bar kungiyar a karshen kakar tamaula ta bana, inda take bukatar fam miliyan takwas kudin da za ta sayar da dan wasan mai shekara 24. (Football Insider)