Paul Pogba zai kai jaridar Sun kotu kan rahoton cewar zai bar buga wa Faransa wasa

Paul Pogba playing for France against Portugal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pogba ya buga wa tawagar Faransa Gasar Nations League a farkon watan nan
An wallafa

Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba ya ce zai dauki matakin shari'a, bayan "tsagwaron karya" da wani rahoto cewar ya bar buga wa tawagar Faransa tamaula.

An bayar da rahoton cewar Pogba mai shekara 27, zai bar buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa tamaula saboda wasu kalamai da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi kan Musulunci.

Dan wasan da ya lashe Kofin Duniya wanda kuma Musulmi ne, ya ci wa tawagar Faransa kwallo 10 a wasa 72 da ya buga mata.

''Labarin na dauke da abubuwa da 100 bisa 100 na ƙage ne da aka ce na fada ko na sanar.'' in ji Pogba.

Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na a Instagram: "Na kadu kuma raina ya baci kan inda wata kafar yada labarai kan yi amfani da labarin karya a babban game da abin da ke faruwa a Faransa har da karawa da tawagar Faransa da kuma addinina.

"Ba na goyon bayan kowanne irin tada kayar baya da rikici. Abin takaici wasu mutane ba sa yin abin da ya dace a lokacin rubuta labarai, ta inda suke cin zarafin fadin albarkacin baki ba tare da sun tantance gaskiyarsa ba.

"Suna kirkirar tsegumi ba tare da jin cewar zai shafi mutane da rayuwarsu ba.

"Zan dauki matakin shari'a kan wadanda suka wallafa da yada wannan labarin karya.