Sauyin Yanayi: Abubuwa biyar da muka sani daga rahoton IPCC

floods in Australia

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Matt McGrath
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Yanayi
  • An wallafa

Wani sabon rahoto da kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi wato Intergovernmental Panel on Climate Change (IPCC) ya duba tasiri da hanyoyn magance matsalar da sauyin yanayi ke haifarwa.

Rahoton ya bayyana alamu mafi karfi kawo yanzu, na yadda dumamar yanayi ke shafar dukkan abubuwa masu rai a duniyarmu.

Ga abubuwa biyar da muka karu da su daga rahoton.

1- Munin al'amarin ya zarce yadda muka sani

Daga narkewar shimfidar kankara a tsibirin Greenland zuwa ga lalacewar muhallan halittun ruwa a teki, tasirin sauyin yanayi na shafar duniya a matakin da ya zarce dukkan wuraren da masana ke tsammani. Sauyin na kuma faruwa cikin hanzari fiye da yadda kwamitin na IPCC ya yi nazari a kai.

A halin yanzu, rahoton na cewa kashi 40 cikin 100 na jama'ar duniya na "fuskantar" hatsarin da sauyin yanayi ke haifarwa.

Sai dai yawancin nauyin na fadawa ne kan wadanda rawar da suka taka ba ta kai ko ina ba.

Patrick Verkooijen, shugaban wata cibiya mai nazari kan sauyin yanayin - Global Center on Adaptation, ya ce "Ga Afirka, za a rasa kashi 30 cikin 100 na masarar da ake nomawa, kuma za a rasa kashi 50 cikin 100 na wake.

"Saboda haka akwai wasu yankunan duniya, musamman a Afirka da rayuwa a wuraren ba za ta yiwu ba."

2 - Mahangar kimiyya kan batun asara da lalacewar yanayi

An dade kasashe masu tasowa na kokarin jan hankulan manyan kasashe su gane cewa batun asara da lalacewa ba na wasa ne ba.

Wannan batun na magane kan tasirin sauyin yanayi da ba a iya magancewa, ko wanda ke zuwa sannu a hankali kamar tasowan da ruwan teku ke yi.

loss and damage

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu fafutuka na zanga-zanga kan rashin ci gaba a batutuwan asara da lalacewar yanayi

Yayin taron koli kan sauyin yanayi da aka yi a Glasgow -taron da Amurka da Tarayar Turai suka hana kafa wani tsarin biyan diyya kan asara da lalacewar yanayi - an kai wani matsayin rashin samun ci gaba.

3 - Fasahar zamani ba maganin matsalar ne ba

Kwamitin na ICPC na Majalisar Dinkin Duniya ta ce amfani da fasahar zamani wajen rage dumamar yanayi ko rage yawan iskar CO2 (wato carbon dioxide), na iya kara dumamar yanayin ne maimakon ya rage shi.

Akwai wata fargabar da ake yi cewa injunan da ke zuke iskar CO2 daga iskar da muke shaka za su janyo karuwar iska mai dumama yanayi ne kawai.

tree planting

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana cewa shuka itatuwa hanya ce ta rage dumamar yanayi, amma IPCC na yin kira a yi takatsantsan kan shuka su a wurin da bai dace ba

Linda Schneider ta gidauniyar Heinrich Böll Foundation ta ce "Idan ka cire iskar CO2 daga yanayi, za ka haifar da martani daga sauran nau'i iskar gas."

"Tekuna da tarin ruwan da ke kan tudu za su fitar da wasu nau'in gas. Kuma sai a mayar da iskar ta CO2 da aka zuke tun da farko."

4 - Birane masu karfafa gwuiwa

Yayin da manyan birane ke zama cibiyoyin samar da iska mai dumama yanayi, akwai wata dama garesu ta kaucewa mummunar illa daga sauyin yanayi.

Kuma yayin da biranen ke kara bunkasa, za a iya komawa ga amfani da sabbin dabaru kamar makamashin da ake iya jujjuya wa akai akai.

Lagos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Birane kamar Legas da ke Najeriya cibiyoyi ne a ke dumama yanayi, sai dai suna iya zama cibiyoyi masu karfafa gwuiwar duniya

Debra Roberts, wacce ke cikin mutum biyu masu jagorantar kwamitin IPCC ta ce "Muna cewa lallai birane na iya zama cibiyoyin gangami domin kawo sauyi.

"A wadannan biranen ne za a sami jama'a masu daraja, musamman a biranen da ke gabar teku. Ana iya hanzarta farafado da yanayi ta hanyar yin gangami a yankunan da ke gabar teku."

5 - Dan lokacin da muke da shi na kara kurewa

Yayin da lamarin ba mai karfaa gwuiwa ba ne a yanzu da ma nan gaba, mawallafa wannan rahoton na cewa lallai za a iya kaucewa tasirin dumamar yanayi - sai dai tilas mu hanzarta.

IPCC ta ce wannan dama ce ta daukan matakan da za su kai mu karshen shekaru goma na farkon wannan karnin.

Somalia

Asalin hoton, Saddam Mohamed

Bayanan hoto, Farin da ya shafi Somaliya ya raba duban iyalai da muhalansu kuma sun yi asarar dabbobin da ba a iya misalta yawansu

Inger Anderson, shugabar shirin kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce "Duniya da kanta za ta iya ceton mu."

"Sai dai fa tilas mu fara ceton ta."

Follow Matt on Twitter @mattmcgrathBBC.