Tonga volcano: Sabbin hotunan yadda Tsunami ta lalata Tonga

.

Asalin hoton, Consulate of the Kingdom of Tonga

An wallafa

Wasu sabbin hotuna sun fito daga Tonga, inda suka nuna irin ɓarnar da guguwar Tsunami ta yi wadda aman dutse na ƙarƙashin teku ya haddasa.

Hotunan sun nuna yadda toka ta rufe tsibirin Pacific, haka kuma a gaɓar teku, tsunamin ta kayar da bishiyoyi da kuma lalata gidaje.

Tsunamin da aka yi a ranar Asabar ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum uku - ciki har da wani ɗan ƙasar Birtaniya, haka kuma Tsunamin ta jawo yankewar sadarwa.

An bayyana cewa an dawo da hanyoyin sadarwar wayar salula na ƙasa da ƙasa sai dai wasu rahotanni na cewa wayoyin sadarwa da suka bi ta ƙarƙashin ƙasa za su iya ɗaukar makonni kafin a gyara su.

Hakan na nufin Tonga ta zama saniyar ware daga sauran ƙasashen duniya ta fuskar sadarwa.

Sai dai wasu hotunan da ofishin jakadancin Tonga na Tarayyar Turai ya fitar, an nuna motoci da hanyoyi da gine-gine a Nuku'alofa babban birnin ƙasar lulluɓe da toka.

Ƙurar da ke da akwai a wurin ta hana jiragen kai agaji sauka da kuma kai kayayyakin abinci masu yawa da ruwan sha.

.

Asalin hoton, Consulate of the Kingdom of Tonga

Hotunan sun kuma nuna yadda wurare suka kasance bayan guguwar Tsunami wadda gwamnatin Tonga ta ce bala'i ne da ba a taɓa gani ba, a gaɓar teku da kuma Tsibiri.

Akwai tarkace a baje a bakin teku bayan da aka samu Tsunami.

.

Asalin hoton, Consulate of the Kingdom of Tonga

Wasu hotuna da rundunar sojin sama ta ɗauka daga sama sun nuna yadda ƙauyuka da dama suka tarwatse a tsibirin waɗanda ba a kai musu ɗauki ba.

Zuwa kai ɗauki

Ayari daban-daban na ta aiki ba dare ba rana domin kai kayan ɗauki a yankin da kuma gyara wayoyin ƙarƙashin teku da suka lalace.

An kammala ƙoƙarin da ake yi na kwashe toka mai kauri daga babban filin jirgin Tonga a ranar Laraba kamar yadda kafar watsa labarai ta AFP ta ruwaito.

An kawar da tokar ne bayan masu aikin sa kai sun yi aiki ba dare ba rana domin kawar da tokar ta hanyar amfani da baro da kuma shebur.

Jam'ian ƙasar na sa ran samun saukar jiragen agaji ba da daɗewa ba.

Presentational grey line

An ɗan samu sadarwa kaɗan tun bayan da aka yi Tsunamin, inda wayoyi kaɗan waɗanda ke amfani da tauraron ɗan adam waɗanda mazauna ofisoshin jakadanci suka yi amfani da su.

Ƴan ƙasar Tongan da dama da ke zaune a ƙasashen ƙetare na ta jira su ji daga masoyansu.

Wani kamfanin sadarwa mai suna Digicel a ranar Laraba ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin buɗe hanyar kiran ƙasashen waje, duk da cewa BBC ba ta samu kowa a Tonga ba bayan ta tuntuɓe su ta waya.

A ranar Laraba, ƙungiyar Red Cross ta bayyana cewa ta tuntuɓi ma'aikatanta a karon farko waɗanda ke zaune a Tonga tun bayan faruwar Tsunamin.

"Abin takaicin shi ne an samu labari mai tayar da hankali daga Tonga inda aka lalata gidaje," kamar yadda shugabar tawagar da ƙungiyar ta aika yankin Pacific wato Katie Greenwood ta shaida wa BBC.

Ms Greenwood ta ƙara da cewa ma'aikatan Red Cross na ta aiki domin rarraba ruwa mai kyau haka kuma ƙungiyar tana wani shiri na wayar da kan mutane su rufe tankunansu da ruwan sama ke shiga domin kare su daga tokar.

.

Asalin hoton, Consulate of the Kingdom of Tonga

Ana sa ran jiragen farko na agaji daga New Zealand da Australia za su isa a ranar Juma'a.

Ministan tsaron New Zealand Peeni Henare ya shaida wa BBC cewa jiragen kawo sama da lita dubu 250 na ruwa mai kyau da kuma kayayyakin da za a ware gishiri daga ruwa.

"Abin da aka fi damuwa wanda aka fi shaida wa gwamnatin Tongan shi ne buƙatar tsaftataccen ruwa," in ji shi.

.

Sai dai jami'an Tongan sun nuna damuwa kan cewa muddin idan aka kai agajin ruwa, hakan zai iya taimakawa wajen bazuwar korona, inda ƙasar ta samu wanda ya kamu da cutar a karon farko a watan Oktoba.