Sauyin yanayi: Yadda matsalar ke janyo guntule wa jama'a kafafuwa

Yankin Sahel na daya daga cikin yankuna mafiya fama da talauci a duniya
Bayanan hoto, Yankin Sahel na daya daga cikin yankuna mafiya fama da talauci a duniya
    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Mali
  • An wallafa

Kasashen yankin Sahel na Afirka na daga cikin mafiya rauni da kuma fuskantar illar sauyin yanayi, duk da cewa hayakin masana'antu da suke fitarwa wanda ke gurbata muhalli bai taka kara ya karya ba - manyan kasashe ne suka fi fitar da irin wannan hayaki.

A bangare guda kuma kasashen na yankin Sahel na fama da matsalar tabarbarewar tsaro inda ake samun rigingimu tsakanin al'ummomi da kuma hare-haren kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi irin su Boko Haram da IS da kuma Al-Ka'ida.

Wannan matsala ta tsaro na cakuduwa da matsalar sauyin yanayi suna kuma kara jefe jama'a cikin mawuyacin hali.

"Ana guntule wa mutane kafafuwa da hannaye"

Da na ziyarci wani asibitin kashi ne a wajen birnin Mopti da ke tsakiyar Mali, muraran, na ga Illar tashin hankali da rikice-rikice wadanda sauyin yanayi ke rura wutarsu.

Galibin marasa lafiya da ke asibitin mutane ne da aka gugguntule masu gabobi. Dalili kuwa shi ne an ji masu munanan raunuka a tashin hankali tsakanin al'umomi ko kuma a hare-haren 'yan bindiga.

Wasu daga cikin marasa lafiyar, maza da mata da kananan yara an sa masu kafafuwan roba - ma'aikatan lafiya kuma na koya masu yadda za su rika tafiya da motsa gabobin.

Abdulkarim Poudjougou mai shekaru 31, na daga cikin wadanda aka yanke wa gabobi. Shi da abokansa suna gona lokacin da tashin hankali ya barke tsakanin makiyaya da manoma a kauyensu a harbe shi sau da dama a gwiwarsa ta dama. Yanzu kafar roba aka sa masa.

Ya ce wasu daga cikin abokan nasa sun yi kokarin tare jinin da ke zubowa da wani tsumma sannan suka dauke shi daga gonar.

Amma lokacin da suka isa asibiti, sai likitoci suka shaida masa cewa raunin nasa ya yi tsanani, kuma yana bangaren jiki ne mai wuyan sha'ani.

Likitocin sun shaida mani cewa ''ko da ya ke za su iya cire albarusan, amma fa ba zan rayu ba. Mafita daya tilo ita ce a yanke kafar tawa. Suka nemi izinina, kuma na yarda.''

Abdulkarim Poudjougou

Ba Abdulkarim Poudjougou ne kadai irin wannan matsala ta shafa ba.

Cikin watanni shida da suka gabata, mutane fiye da 90 da aka yanke wa gabobi sanadin munin raunuka da suka samu a tashe-tashen hankali, aka yi wa magani a wannan asibiti.

Kungiyar Red Cross ta kasa da kasa ce ke tafiyar da asibitin kashin. Dr. Timothee Pakouyowou, shugaban asibitin, ya ce galibin wadanda matsalar tsaron gamin da sauyin yanayi ke shafa, talakawa ne daga sassa daban-daba na kasar ta Mali da ma wasu kasashen yankin Sahel.

Ya ce ''muna samun marasa lafiya daga dukkan yankuna - kama daga tsakiyar Mali zuwa arewacinta - wasu ma daga kasar Burkina Faso.''

Matsalar ta zama ruwan dare

Tashe-tashen hankali gami da tasirin sauyin yanayi sun daidaita rayuwa.
Bayanan hoto, Tashe-tashen hankali gami da tasirin sauyin yanayi sun daidaita rayuwa.

Yankin Sahel na daya daga cikin yankuna mafiya fama da talauci a duniya. Ana yawan fuskantar fari a yankin, yanayin ruwan sama bai da tabbas, sannan kasar noma ta yi mummunar lalacewa.

Yanzu mutane kimanin muliyan 30 ke fuskantar karancin abinci, miliyan shida daga cikinsu na bukatar agajin gaggawa, a cewar kungiyoyin agaji.

Tashe-tashen hankali gami da tasirin sauyin yanayi sun daidaita rayuwa.

Wasu daga cikin mutane da na zanta da su sun shaida mani cewa a shekarun baya, ana zaman lafiya tsakanin al'umomi, amma a shekarun baya-bayan nan musamman cikin shekaru goma da suka gabata, sai lamura suka sauya.

Gogayya da kokawar samun albarkatun kasa suka karu, zaman tankiya shi ma ya karu musamman tsakanin manoma da makiya.

Haka zalika, masu tayar da kayar baya na amfani da tsananin talauci da yunwa da wasu ke fama da su suna shigar da su cikin kungiyoyinsu.

A wani sansani na 'yan gudun hijira wadanda tashe-tashen hankali suka raba da muhallansu, na ga mata da kananan yara da kuma manya cikin mawuyacin hali ga kuma rashin tabbas kan makomarsu.

Sansanin da ke birnin Mopti, akwai mutane kimanin 2000 a cikinsa. Matan na girke-girke, wasu na daka a turmi, yayin da wasu samari da 'yan mata kuma ke wankin tufafi.

Wasunsu sun shafe fiye da shekara biyu a nan suna zaune cikin tantuna.

Daya daga cikin 'yan hijirar, Djeneba Barry mai shekaru 37 da 'ya'yanta shida sun gamu da ukuba sanadin tashin hankali da kuma tasirin sauyin yanayi.

Yayin da take daka gero ta shaida mani cewa fari ya tilasta masu kaura fiye da sau uku, daga wannan kauyen zuwa wancan, suna neman ruwan sha da inda za su yi kiwon dabbobinsu.

Ta ce ''babu ruwa, ka san mutane da dabbobi na bukatar ruwa domin su rayu. Idan babu ruwa, dabbobi za su kamu da cututtuka kuma su mutu. Tabbas dabbobi za su mutu.''

'Bisa kuskure na zauna a kan nakiya ta kuma tashi da ni'

Halin da Djeneba da danginta suka shiga ya kara muni a yanayin nan da ake cewa ana kukan targade sai ga karaya.

A kauye na karshe da suka samu matsuguni, sai aka samu tashin hakali tsakanin makiyaya da manoma inda aka kai masu hari a 2018. Sun tsere suka bar dabbobinsu, mijinta kuma an sace shi - sun ma fitar da rai yanzu suna jin ya ma mutu.

A babban asibitin birnin Mopti, na ga marasa lafiya da dama. Wasunsu da munanann raunuka na harbin bindiga. Wasunsu an daura masu bandeji. Amma marar lafiya da ya fi sosai rai shi ne wani yaro mai shekara 17.

Ya shaida man cewa shi da mahaifinsa suna hanyar zuwa gona da amalanke sai suka tsaya domin su huta a gefen titi. Zamansu ke da wuya sai nakiya ta tashi da su.

Babu tabbas ko wane ne ya dąsa nakiyar, amma yankin na daga cikin wuwaren da sojoji ke fafatawa da masu tayar da kayar baya.

Sanadin tashin nakiyar, ya samu munanan raunuka a duwawunsa, abin ba kyan gani.

Duk da cewa yankin Sahel na Afirka na daga cikin wadanda tasirin sauyin yanayi ya fi yi wa illa inda ake samu rikice-rikice kan karancin albarkatun tattalin arziki, amma mutane da dama a nan ba su da masaniya sosai kan matsalar ta sauyin yanayi bare ma hanyoyin da za su tunkareta.

'Kasashen duniya sun yi watsi da jama'ar kasashen yankin Sahel'

Shugaban kungiyar agajin Red Cross ta kasa da kasa, Robert Mardini
Bayanan hoto, Red Cross ta ce shugabannin duniya ba sa kokarin da ya kamata wajen magance matsalar.

A baya-bayan nan shugabannin duniya sun yi wani babban taro a birnin Glasgow na Scotland kan sauyin yanayi, inda suka cimma yarjejeniya kan bukatar kara daukar mataki don dakile tasirin sauyin yanayi.

Sai dai kuma yayin wata ziyara a Mali, shugaban kungiyar agajin Red Cross ta kasa da kasa, Robert Mardini, ya shaida mani cewa shugabannin duniya ba sa kokarin da ya kamata wajen magance matsalar.

Ya ce akwai bukatar a maida hankali ga masu rauni, ya kara da cewa mutane masu sauni ''su ne mutane dake yankin Sahel, da yankin kuryar Afirka wadanda ke fuskantar sauyin yanayi muraran, kana suna fuskantar tashe-tashen hankula.''

Mr Mardini ya ce duniya ta yi watsi da talakawan yankin Sahel yana mai cewa ''su ne a yau aka manta da su wajen daukar mataki da kuma samar da kudade don dakile sauyin yanayi.''

Yayin da duniya ke tafiyar hawainiya wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi, rigingimu kuma na kara ta'azzara a kasashen yankin Sahel kamar Mali da Nijar da Burkina Faso da Mauritania da kuma Chadi, ga alama rayuwar miliyoyin mutane na cikin matukar hadari.