Manyan bala’i 10 da sauyin yanayi ya haddasa a 2021

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Matt McGrath
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent
- An wallafa
Bala'o'i iri-iri da ke da alaka da sauyin yanayi sun tagayyara rayuwar miliyoyin mutane a fadin duniya a wannan shekara ta 2021, a cewar wani sabon rahoto.
Rahoton, wanda kungiyar ba da agaji ta Christian Aid ta fitar, ya bayyana manyan bala'i 10 da kowannensu ya haddasa asarar da ta wuce ta dala biliyan ɗaya da rabi.
Bala'in da ya janyo asarar kudi mafi girma shi ne Mahaukaciyar Guguwa da aka yi wa lakabi da Ida wadda ta auka wa Amurka a watan Agusta da kuma ambaliyar ruwan da ta fada wa Turai a watan Yuli.
A yankuna matalauta da dama, ambaliyar ruwa da tsawa sun raba miliyoyin mutane da gidajensu sannan sun jefa su cikin mawuyacin hali.
Ba kowanne babban bala'i ne ya faru sakamakon sauyin yanayi ba, kodayake masana kimiyya sun jaddada cewa akwai alaka tsakanin faruwar bala'an da kuma sauyin yanayi.
Daya daga cikin masu binciken, Dr Friederike Otto, ya wallafa sako a Twitter a farkon shekarar nan da ke cewa duk wani yanayin matsanancin zafi da ya faru a duniya a yanzu "akwai yiwuwar ya ta'azzara ne" sakamakon sauyin yanayi da dan Adam ya haddasa.
Game da tsawa da mahaukatan guguwa, akwai karin shaidu da ke nuna cewa sauyin yanayi yana tasiri kan aukuwarsu.
A watan Agusta, kwamitin da gamayyar kasashe ta kafa kan Sauyin Yanayi ya wallafa kashin farko na rahotanni shida game da binciken da ya yi.
A game da mahaukatan guguwa da ambaliyar ruwa, masu binciken sun ce suna da "yakini" cewa ayyukan dan Adam sun ta'azzara aukuwarsu.
"Karfin gudun mahaukaciyar guguwar ya yi daidai da karfin iska, kuma karfin gudun iskar na karuwa ne a fadin duniya a yayin da dumamar yanayi take karuwa," a cewar binciken.
Mahaukaciyar guguwar Ida ta ragargaji Amurka ne makonni kadan bayan fitar da binciken.

Asalin hoton, Getty Images
A cewar Christian Aid, guguwar ita ce bala'in da ya fi haddasa asarar kudi a wannan shekarar.
Mahaukaciyar guguwar wadda ta rika tafiya a hankali ta sa an kwashe dubban mutane daga gidajensu a Louisiana da ke kan hanyarta.
Ta yi sanadin saukar ruwan sama kamar da bakin-kwarya a jihohi da birane da dama, har ta kai ga a karon farko an ayyana yiwuwar faruwar mamakon ruwan sama da zaftarewar kasa a New York.
Kusan mutum 95 ne suka mutu yayin da aka yi asarar kimanin dala biliyan 65.
Bala'i na biyu da ya fi haddasa asarar kudi shi ne ambaliyar ruwan da ta faru a yankunan Jamus da Faransa da kuma sauran kasashen Turai a watan Yuli.
Karfi da kuma saurin ambaliyar ruwan sun sa katangun da aka gina don kariya sun fadi kuma mutum 240 sun mutu. An kiyasta cewa an yi asarar kusan dala biliyan 43.
Binciken ya nuna cewa akasarin bala'o'in sun faru ne a kasashen da suka ci gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Hakan ya faru ne saboda abu ne mai sauki a kiyasta asarar kudin da aka yi a can ta hanyar kamfanonin inshora kuma ana samun yawancin wannan kididdiga a kasashe masu arziki, inda mutane za su iya yi wa gidajensu da harkokin kasuwancinsu inshora.
A cewar kamfanin inshora na Aon, akwai yiwuwar shekarar 2021 ta kasance shekara ta hudu cikin shekaru biyar da bala'o'in da ke da alaka da sauyin yanayi suka janyo asarar fiye da $100bn.
Rahoton ya bayyana sauran ba bala'o'in da zai yi wahala a kiyasta girman asarar kudin da suka haddasa, amma kuma tasirin da suka yi a rayuwar jama'a yake da girma.
Ambaliyar ruwan da aka yi a Sudan Ta Kudu ta raba mutum fiye da 800,000 daga muhallansu yayin da mutum 200,000 suka tsere daga guguwar Tauktae wadda ta auku a India, Sri Lanka da kuma the Maldives a watan Mayu.
"Wannan babban lamari ne da ya shafi dan adam," a cewar mutumin da ya wallafa rahoton Dr Kat Kramer daga Christian Aid.
"A fili yake cewa rasa gidanka, da sana'arka, da komai da komai ba tare da samun kudin da za ka sake gina su ba abu ne me tayar da hankali.
Ko da yake idan kana da inshora, za ka samu hanyar sake gina rayuwarka."
Rahoton ya jaddada bukatar mayar da hankali wajen rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli domin rage aukuwar bala'o'i masu alaka da sauyin yanayi nan gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Za ku iya samun rahoton a nan.
Kuna iya bin Matt a Twitter.









