Tuvalu: Ƙasar da sauyin yanayi ke shirin shafe ta daga doron ƙasa

Simon Kofe con el agua hasta las rodillas durante su mensaje grabado a la COP26

Asalin hoton, Min. de Relaciones Exteriores de Tuvalu

An wallafa

Yi tunani na ɗan lokaci game da gidanku, tarihinku, wurin da kuka fi so a wannan duniyar.

Kuma yana da wuya a yi tunanin cewa wannan sashi zai ɓace gaba ɗaya daga fuskar duniya.

Ga yawancin mazauna tsibirai wannan fargabar ta gaske ce.

Tumbatsar da tekuna ke yi saboda sauyin yanayi ya riga ya haddasa asarar filaye da ƙarancin ruwan sha a waɗannan tsibiran.

BBC ta yi duba kan halin da ake ciki a wata karamar kasa ta Pacific, Tuvalu, da take ta yin kira ga kasashen da suka fi gurbata muhalli da su rage hayaki mai gurbata muhalli.

Wannan kasa na kuma shiryawa kan abkuwar al'amari mafi muni: nutsewar kasar cikin ruwa.

Ita ma wannan kasa tana shirye-shiryen fuskantar mafi munin yanayi: na rugujewar yankunanta gaba daya.

Ministan shari'a, sadarwa da harkokin waje na Tuvalu, Simon Kofe, ya aike da sako mai karfi ga taron sauyin yanayi na COP26, wanda aka gudanar kwanan nan a birnin Glasgow na kasar Scotland.

"Muna ɓacewa, amma hakan zai faru ga kowa,'' ya ce.

Franja de territorio de Tuvalu con el océano a un lado y una laguna al otro

Asalin hoton, Getty Images

Yawan ruwan teku, barazanar da ta dade tana wanzuwa

Tuvalu tana da tsibirai tara kuma tana da nisan mil 4,000 daga Ostiraliya da Hawaii. Maƙwabta mafi kusa su ne Kiribati, Samoa da Fiji.

Kasar tana da fadin murabba'in kilomita 26, tana da yawan jama'a kusan 12,000.

Kamar Kiribati da Maldives da sauran su, Tuvalu karamar tsibiri ce, don haka tana fuskantar babban hadarin dumamar yanayi. " na kasar sashin tsibirin," in ji Kofe.

Mapa que muestra la ubicación de Tuvalu en el Pacífico

Tuvalu na kuma fuskantar gawurtattun mahaukaciyar guguwa da kuma lokutan fari, ministan ya kara bayyanawa. Kana ma'aunin zafin tekun mafi girma ya busar da halittu da tsirran bakin tekun, wadanda ke da matukar muhimmanci waken kariya da kuma hayayyafar kifaye.

"Yawanci muna samun ruwan sama, amma a wasu tsibiran kuma suna haƙa rijiyoyi don samun ruwa daga ƙasa.

"Hakan ba zai yiwu ba saboda shigar ruwan teku, don haka mun dogara ga ruwan sama kawai."

Kutsawar ruwan teku mai gishiri ya kuma lalata amfanin gonakin noma.

A halin yanzu gwamnatin Taiwan tana ba da tallafi da jagorantar aikin samar da abinci don kula da muhalli a Tuvalu.

Palmeras caídas por la erosión del suelo en la costa

Asalin hoton, Getty Images

Damuwar kasashen tsibirin

Kasashen tsibirai kamar Tuvalu sun yi kira da a dauki tsauraran matakai kan sauyin yanayi sama da shekaru 30.

A shekarar 1990, kasashen da ke Tekun Pasifik suka ƙulla ƙawancen diflomasiyya daga yankin Caribbean, wadanda suka hada da kasashe irin su Antigua da Barbuda, da na Tekun Indiya kamar Maldives.

Manufar ita ce ƙulla ƙawance don tattaunawa kan sauyin yanayi.

Joven examinando papayas en la granja Fatoaga Fiafia

Asalin hoton, Getty Images

Mene ne masana kimiyya suka ce?

Hukumar kula da sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya (IPCC) ta bayyana a wani rahoto da ta fitar a ranar 9 ga watan Agustan bana cewa, yawan ruwan teku a duniya tsakanin shekarar 1901 zuwa 2018 ya kai mita 3.7 a shekara.

Duk da haka, "al'amarin ya fi muni a cikin tsibirai na Pacific," Dr. Morgan Wairiu, ƙwararre kan sauyin yanayi ya shaida wa BBC daga tsibirin Solomon.

"A Kudancin Pasifik matsakaicin hauhawar matakin teku ya kasance tsakanin mililita 5 da 11 a cikin lokacin daga 1900 zuwa 2018."

Dakta Wairiu ya ce, ƙarfin ruwa a tsibiran Pasifik zai ragu da kashi 25% da maki 1.5 a ma'aunin celcius idan aka kwatanta da ma'aunin celcius 2.

Masana a taƙaice sun zayyana manyan haɗari ga ƙananan tsibiran da ke cikin Tekun Pasifik:

Maestra corrigiendo el trabajo de un niño en una escuela en Tuvalu

Asalin hoton, Getty Images

Wani bincike da masana kimiyya a Amurka da Netherlands suka gudanar a shekarar 2018, da dai sauransu, ya nuna cewa "yawan kasashen tsibirin mutane ba za su iya zama ba sai tsakiyar wannan karni".

Dalili kuwa shi ne "tumbatsar ruwan teku zai haifar da ambaliya".

Fuskantar hakikanin gaskiya da barazanar sauyin yanayi da kuma rashin daukar matakan da suka dace daga duniya da take fuskanta, Tuvalu na neman wasu hanyoyin nemo mafita ga makomarta.

Kofe ya shaida wa BBC cewa, "Ba shakka, abin da ya fi muni shi ne, an tilasta mana yin ƙaura, kuma tsibiranmu sun nutse gaba daya."

"Kuma bisa ga dokokin kasa da kasa, a wannan karon kasa za ta iya samun yankin ruwanta idan har tana da wani fili da za a iya jan iyaka."

"Dokokin ƙasa da ƙasa a halin yanzu kuma sun ba da damar cewa kowace ƙasa za ta iya mallakar yankin da ruwanta yake idan har tana da yankin ƙasa da za a iya yankar iyaka.

Una mujer extrae agua de un tanque de almacenamiento

Asalin hoton, Getty Images

A halin yanzu dai Tuvalu na duba yiwuwar daukar matakan shari'a da za a amince da su a duniya ta yadda ko da kasar za ta shafe, za a ci gaba da amincewa da ita a matsayin kasa da kuma samun damar samun albarkatun ruwanta, in ji Kofe.

Ba kamar Kiribati ba, Tuvalu ya sayi filaye a Fiji, ko da yake Kofe ya ce ƙasarsa "sun yi sanarwar jama'a cewa za su ba Tuvalu kyautar fili idan muka nutse cikin teku a nan gaba.

Ministan ba ya ma son yin tunanin yiwuwar ƙasar ta sauya muhalli.

Un niño camina sobre bolsas de arena apiladas para aminorar el avance del mar

Asalin hoton, Getty Images

"Ba mu san ko wace ƙasa ce za mu fi son ƙaura ba, domin mun kuma fahimci cewa za a iya amfani da ƙaura a matsayin dalilin da manyan ƙasashe za su iya cewa: 'Mun ba su fili su ƙaura kuma muna ci gaba da aikinmu na samar da iskar gas. " "Motsi shi ne zaɓi na ƙarshe."

Har ila yau, Tuvalu na son samun wani abu da kasashen da suka ci gaba suka yi kira da babbar murya kuma kasashe masu arziki sun ki ba da shi: diyya ga "lalacewa da asarar da sauyin yanayi ya haifar.

Tare da hain kan gwamnatocin Antigua da Barbuda, kwanan nan Tuvalu ta sanya hannu kan sabon kwamiti tare da Majalisar Dinkin Duniya.

"Daya daga cikin dalilan kafa wannan kwamiti shi ne ta hanyarsa za mu iya samun goyon bayan kotun shari'ar ruwa ta kasa da kasa kuma za mu iya neman shawarar neman ra'ayi game da lalacewa da asarar da muke fuskanta," in ji Kofe.

Kotun kasa da kasa ta Hamburg da ke birnin Hamburg na kasar Jamus, ita ce ke da alhakin warware tashe-tashen hankula da suka shafi yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1982 kan dokar teku.

Sabon kwamitin Tuvalu da Antigua da Barbuda zai tambayi alkalan ko za su iya neman diyya daga kasashen da suka dumama teku ta hanyar gurbatar yanayi kamar yadda wani lauya mai kare dukkan kasashen, Payam Akhavan ya shaida wa manema labarai.

Ya kara da cewa idan ra'ayin kotun ya dace, al'ummar tsibirin na iya shigar da ƙara a gaban kotun ko kuma wasu kotuna na kasa da kasa.

Funafuti, la capital de Tuvalu. El gobierno quiere seguir teniendo acceso a su zona marítima aún si todo el territorio queda sumergido.

Asalin hoton, Getty Images

A shekara ta 2009, kasashe masu arziki sun yi alkawarin bayar da dala miliyan 100 ga kasashe masu tasowa a duk shekara, don taimaka musu a lokacin miƙa mulki don rage tattalin arzikin da ke dogaro da carbon.

Sai dai a yayin taron na COP26, gwamnatin Birtaniya da kuma jakadan Amurka John Kerry tare sun bayyana cewa, za a iya cimma burin nan da shekara ta 2023.

A sakonsa na karshe ga taron kolin COP26, Firai ministar Maldives kuma ministar muhalli Aminath Shauna ta bayyana cewa, bambancin da ke tsakanin "dumamar yanayi a ma'aunin ma'aunin celcius 1.5 da ma'aunin celcius 2 a gare mu, hukuncin kisa ne."

Simon Kofe en una reunión de trabajo en Tuvalu

Asalin hoton, Min. de Relaciones Exteriores de Tuvalu

Ko bayan COP26, bincike ya yi kiyasin cewa duniya tana fuskantar zafi kuma tana fuskantar zafi na akalla digiri 2.4 a karshen wannan ƙarni.

Ga al'ummar Tuvalu, yiwuwar zama 'yan gudun hijira don sauyin yanayi yana ƙaruwa yayin da kowace shekara duniya ke fama da rashin ɗaukar matakan shawo kansa.

"Abin bakin ciki ne da ban mamaki ga kowa ya yi tunanin cewa gidajensu na iya ɓacewa nan da wasu shekaru masu zuwa, ra'ayin cewa 'ya'yansu da jikoki ba su da wurin zama," in ji Simon Kofe.

Una mujer con una niña en brazos en Tuvalu

Asalin hoton, Getty Images