Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya ƙaddamar da aikin gina layin dogo a Jihar Kano

Asalin hoton, Facebook/Dr Isa Ali Pantami
Shugaba Muhammdu Buhari ya kaddamar da fara aikin gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna a ranar Alhamis a unguwar Zawaciki da ke jihar.
Za a shafe tsahon watanni 18 wajen gina layin dogon na Kano zuwa Kaduna
Ana sa ran sabon layin dogon zai hade da na jihar Kaduna zuwa Abuja, da wanda ya taso daga Abuja zuwa Lagos..
Aikin Kano zuwa Kaduna shi ne kashi na uku na aikin layin dogo da gwamantin kasar ke yi a na hade jihohin Lagos da Kano, baya ga kashin na biyu na hade Lagos zuwa Ibadan da aka kammala.
Jihar Kano ita ce cibiyar kasuwanci arewacin Najeriya inda 'yan kasuwa daga sassan kasar daban-daban har ma da sauran kasashen duniya ke zuwa domin yin hada-hadar kasuwanci.
Sai dai tsawon shekaru harkokin sufurin jirgin kasa a jihar sun durkushe, inda 'yan kasuwa suka fi mayar da hankali wajen dakon kayansu a manyan motoci daga jihar zuwa wata, ko kuma daga wata jihar zuwa Kano.
Yadda aikin zai shafi 'yan kasuwa

Asalin hoton, Google
Abdullahi Musa Mai siminti, wanda a baya yake dauko simunti daga Gombe da Lagos ta jirgin kasa zuwa Kano, ya shaida wa BBC cewa rashin layin dogon ya sa harkokin kasuwanci sun kara wahala kuma hakan na daga cikin dalilan da suka janyo tashin kayayyaki.
Shi ma Nasir Shehu Haske, wanda a baya yake harkar daukowa da kai kaya ta jirgin kasa, cewa ya yi layin dogon da shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari zai kaddamar zai taimaka wajen kore musu fargaba tare da saukaka musu wajen kashe makudan kudade da zummar safarar kayansu, sabanin yadda suke kashe kudi mai yawa idan da mota ce.
A yayin ziyara da shugaban Buharin zai kawo jahar Kano zai bude gadar sama da kasa dake sha-tale-talen Dangi da ke kan titin zuwa Zariya sannan yaje fadar sarkin Kano, daga bisani ya wuce Katsina inda zai kaddamar da aikin matatar ruwa a karamar hukumar Safana da ke jihar.
Buhari na Kanawa ?

Asalin hoton, KANOGOVT
Wasu daga cikin jama'ar jihar dai sun jima suna kokawa a kan yadda suke ganin kamar Shugaba Buhari ya yi watsi da Kano tun bayan hawansa karagar mulki, duk da cewar jihar ta yi ƙaurin suna wajen mara masa bayan tun lokacin da yake takarar shugaban kasa.
Yayin da mulkin shugaban ya taho gangara dai wasu masu shari na ganin cewa dasa harsashin wannan gagarumin aiki daga Kano na nuna kokarin shugaba Buhari na son ganin ya nuna wa jama'ar jihar cewa bai manta da su ba.
A yayin ziyarar shugaban dai ana sa ran zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya yi, da suka hadar da gadar sama da kasa dake sha-tale-talen Dangi.










