Najeriya: Har yanzu ba a bai wa mata yan kabilar Igbo gadon iyayensu

- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abagana
- An wallafa
Har yanzu ba a bai wa mata gadon iyayensu a yankin kudu maso gabashin Najeriya, duk da umarnin da Kotun Ƙoli ta bayar na hana nuna wannan wariyar.
Bayan mahaifin Onyinye Igwe ya rasu shekara biyu da suka gabata, sai rayuwa ta yi mata tsanani duk da cewa ya mutu ya bar tarin dukiya kamar gidaje da filaye da kuɗaɗe a banki.
Mahaifinta ya bi sahun galibin maza masu ra'ayin riƙau a ƙabilar da ba ta yarda da barin wasiyyar gado ba, don haka da ya mutu sai ƴaƴansa suka ɗauki ragamar raba gadon.
Duk da cewa Onyinye mai shekara 29 ce babbar ƴarsa, ita da sauran ƙannenta mata biyar ba su tashi da ko sisi ba - ƴan uwanta maza uku ne suka mallake komai kamar yadda al'adar ƙabilar Ibo ta tanada.
Ta shaida wa BBC cewa : "Ƴan uwana maza sun handame duk abin da mahaifinmu ya mallaka.
"Sun ce mana mu mata aure za mu yi a gidan wani don haka ba za mu gaji komi na mahaifinmu ba. Saboda haka al'adar take, mu kuma ba mu yi faɗa da su kan hakan ba."
A sakamakon hakan, ba ta samu damar zuwa jami'a ba kuma a yanzu tana sana'ar sayar da dafaffiyar taliyar indomie ne a garin Abagana da ke kudu maso gabashin jihar Anambra.
'Mazan ne ke kwashe komai'
Kusa da inda Oyinye ke zaune na haɗu da Evelyn Onyenokwalu, ƴar fari mai ƙanne uku.
Lokacin da mahaifinta ya rasu, ƙanEnta ɗaya tilo - ɗan autan gidansu - ya gaje komai da mahaifinsu ya bari, har da gidan da suke ciki.
"Mutane da yawa sun sa baki kafin ƙanina ya ba ni ɗaki ɗaya a gidan da mahaifinmu ya bari kuma ya ba ni umarnin kada in riƙa rufe ƙofar.
"Akwai lokacin da ba ni da kuɗi saboda ƙanina ya bayar da hayar wasu ɗakuna kuma bai ba ni ko taro ba daga kuɗin hayar da ake ba shi," a cewarta.
Ƙanin nata, Oscar Nonso, wani mawaƙi wanda a yanzu yake sana'ar kiwon kaji a harabar gidan da ya gada, ya ce bai yi wani laifi ba kuma al'adar iyayensa yake bi.

"A nan mazan ne ke kwashe komai, sai dai su bai wa matan abin da suka ga dama," a cewarsa.
"Wannan faɗan gadon mahaifinka kamar neman ƙari ne kan abin da kike da shi, saboda ke mace idan kika samu a gidan mahaifinki, lallai za ki samu a gidan mijinki," a cewarsa.
'Kana nufin mata ba su isa ba'
Kundin tsarin Najeriya ya haramta irin wannan nuna wariya amma ƴan ƙabilar Ibo da yawa na ci gaba da yi.
A iyalai da yawa, ana raba gadon da mahaifi a bari ne a tsakanin ƴaƴansa maza - yawan abin da za a ba ko wanne ya danganta da shekaru don haka manyan yaƴan sun fi samun kaso mai yawa - yayin da mata ba sa samun komai.
A wasu lokutan da aka ba mata kaso, sai dai a ba su abubuwan da mallakin iyayensu mata ne amma ba sa gadon filaye da gidaje.
Ƴan ƙabilar Ibo da dama sun yarda cewa bai kamata mace ta yi gadon filin da aka gada tun iyaye da kakanni ba saboda ana sa rai mace za ta bar gidan iyayenta idan ta yi aure, yayin da namiji zai ci gaba da riƙe martabar gidan.
Akwai kuma fargabar cewa idan aka bar mace ta gaji fili, wata rana mijinta na iya gadon filin da iyayenta da kakanninta suka bar mata.
Ana ganin gidaje a matsayin gadon ƴaƴa maza kawai, wanda ake bin girma wurin raba shi - kuma wannan ya samo asali ne daga lokacin da magidanci a ƙabilar Ibo ke zama ɓangare daban (wanda ake kira obi) da matansa da ƴaƴansa amma a haraba guda.
A lokacin mutuwarsa, ana miƙa kayan bautar da ke cikin obi zuwa ga ɗansa na fari.
Idan ba shi da ɗa namiji, sai a bai wa wasu maza ƴan uwansa amma ba za a bai wa matan mutumin ko ƴaƴansa mata ba.
Sai dai ba duka mata ne suka amince sa wannan al'adar ba.

Wata shari'a da aka kwashe sama da shekara 20 ana yi ta zo ƙarshe a 2014 inda wata mace da ta kai iyalinta kotu kan hana ta gado ta yi nasara.
Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa an nuna wariya idan aka hana ƴaƴa mata gado.
Sai dai ba a samu wani sauyin a-zo-a-gani ba duk da wannan hukunci.

Egodi Igwe (ba ta da alaƙa da Onyinye Igwe) ta wata ƙungiya mai zaman kanta ta Women Aid Collective (Wacol), mai wakiltar mata a kotu kyauta ta ce ƙungiyarta na samun ɗaruruwan mata masu shigar da ƙara duk shekara.
"Ana nan ana ci gaba da yin al'adar da ke ba da damar yin wannan mugunta sosai a al'ummar mu.
"Idan ka ce wa ƴa mace ba za ta samu gadon mahaifanta ba, kenan kana nufin ba ƴar nan ba ce kuma ba ta isa a sa da ita ba," a cewarta.
'Dole mata su fara daukar mataki'
Matan da aka hana gado na da damar zuwa kotu, amma kuɗin da za su biya lauyoyi da shekarun da za a kwashe sun yi yawa kuma wannan na iya haifar da husuma a tsakanin iyali, don haka sai su je wurin sarakunan gargajiya - waɗan dama maza ne - da kuma wurin dangi wanda da wuya su ba su goyon baya.
"Da wuya a samu sauyi muddin maza ne ke riƙe da shugabanci," in ji Egodi Igwe.
"Idan har za a samu sauyi, dole mata su shiga a dama da su hukumomin da ke iya ɗaukar wani mataki," a cewara.

Kawo ƙarshen wannan al'ada za a buƙaci taimakon sarakunan yankin masu faɗa a ji waɗanda ke iya kawo ƙarshenta, amma mafi yawansu na cewa al'ada ce da ba za a iya sauya wa ba.
Igwe Chiwendu Onuoha, sarkin Eke na jihar Enugu na ganin cewa babu nuna wariya a hana mata cin gado.
"Maza ne masu kula da filaye da al'adu," a cewarsa.
Ya ƙara da cewa gidaje da filayen gado na mazan da ke al'umma ne.
"Waɗannan mazan ne ke kula da al'ummomi. Idan akwai wani rikici, su ne suke shiga su yi sulhu.
"A al'adance ba a nuna wariya ba. Al'adarmu ce. Ni ban ga wata wariya a nan ba," a cewarsa.
'An halicci maza da mata dai-dai'
Duk da cewa har yanzu ana amfani da wannan al'ada a yankin, akwai al'ummomin da su daina amfani da ita.
Igwe Godwin Ecko na ɗaya daga cikin sarakuna ƴan tsiraru da suka kawo ƙarshen wannan al'ada a masarautar Ihe a Enugu.

"Muna ganin an halicci maza da mata dai-dai don haka hana mata wasu abubuwa ba daidai ba ne.
"A al'ummata mata na cin gadon komai har da fili. Ba ma amincewa iyaye maza su karɓe kayan gado daga matan da ba su da ƴaƴa maza," a cewarsa.
Amma kafin hawansa mulki a 1993 ba haka abin yake ba kuma ya dage wajen kawo sauyi, abin da ya ba mutane da dama mamaki.
"Mutane sun ta cewa zan jawo faɗa idan na sauya al'adar, amma babu abin da ya faru," a cewarsa.
'Ba zan iya faɗa da ƴan uwana maza ba'
Masu fafutuka na ganin cewa hana mata cin gadon iyayensu wata hanya ce ta amfani da al'ada wurin nuna wa mata wariya kamar aske wa matar da mijinta ya mutu gashi, da kaciyar mata ko kuma hana mata cin gadon filaye.
Ana iya ce filaye da gidaje hanyoyi ne na samun jari kuma idan aka ware mata, rashin samun tagomashi a ɓangaren tattalin arzƙi da aka daɗe ana yi zai ci gaba, a cewarsu.

Kuma baya ga dokar, ƙwararru na ganin cewa maza, musamman iyaye, na da rawar da ya kamata su taka don kawo sauyi.
"A wannan rikicin hana ƴaƴa mata cin gado, ina ganin ya kamata maza su fara tunanin yadda za su tabbatar cewa iyalinsu ba su faɗa cikin wannan halin ba idan suka mutu," in ji Egodi Igwe.










