Yadda cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka ke bunƙasa duk da annobar cutar korona

Convoys of trucks queuing outside a border post in Zambia
Bayanan hoto, Ayarin motocin da ke dakon kaya yayin da suke jira a ksa da kan iyaka a Zambia saboda dokar korona da ta hana walwala
    • Marubuci, Daga Mary-Ann Russon
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a shaa'nin kasuwanci
  • An wallafa

A bara wasu kasashen Afirka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka kafa domin bunkasa kasuwanci tsakaninsu. Idan aka yi nasarar aiwatar da yarjejeniyar, suna ganin za a iya samar da wata katafariyar kasuwa mai fiye da mutum biliyan ɗaya.

Tsarin wannan yarjejeniyar shi ne a samar da hanyar da kayayyaki za su rika shiga kasashen da ke cikin shirin ba tare da shingaye ba, wanda zai mayar da nahiyar ta zama irinta mafi girma a duniya.

Wannan yarjejeniyar na iya samar da kasuwar da darajar ta ya kai dala tiriliyan 3 inji kamfanin Brookings na Amurka.

A halin yanzu Afirka na bayan sauran yankunan duniya a fagen kasuwancin cikin gida. Bankin raya Afirka (ADB) ya ce kashi 16.6 na cinikayyar duniya ne kacal Afirka ke mora.

Amma abin damuwar shi ne yarjejeniyar ACTFA da kasashen Afirka suka samar domin yin kasuwanci babu shingaye tsakaninsu bai fara aiki ba ranar 1 ga watan Yuli saboda annobar korona, amma akwai wasu dalilan.

Trudi Hartzenberg, babbar shugabar cibiyar da ke sa ido kan dokokin kasuwanci (Tralac) da ke Stellenbosch a Afirka ta Kudu na ganin tattaunawa kan batun na tafiya sannu a hankali amma an ci karo da wasu batutuwa.

"Tataunawar na da sarkakiya matuka saboda kasashen da ke ciki za su rasa wani bangare na kudadewn shigan da suke samu. Rage haraji na nufin za su rasa yawancin kudaden shiga kamar yadda suka saba samu a da." inji ta.

A woman shopping in a retail store in the Republic of Congo
Bayanan hoto, Saboda annobar korona, dan kasuwa kamar Petra a Jamhuriyar Kongo sun koma ga kaya daga China maimakon sayo su daga makwabtan kasar

Karamar rigar da aka sayo daga China zuwa wata kasar da ke cikin kungiyar cinikayya ta kasashen kudancin Afirka za a iya saka ma ta harajin kashi 45, kuma babu wata hanyar maye gurbin wannan harajin idan aka koma ga sayen kayan daga kasashen cikin nahiyar, inji Ms Hartzenberg.

Amma duk da haka jami'ai daga kasashen nahiyar sun jurewa wadannan jerin kalubalen.

Tattauanwar da ake yi yanzu ta koma ta intanet, inda ake amfani da na'urar Zoom domin tattaunawa kai tsaye, kuma a watan Mayu aka fara tattaunawar. Sai dai akawai matsalar samar da sabis mai kyau.

Matsalar sufuri a lokacin korona

Ban da rashin ingancin hanyoyin sadarwa da hanyoyin sufuri wadatattu tsakanin kasashen Afirka, isowar annobar korona ta dagula lamurra matuka.

"Yawancin cinikin da ke wakana tsakanin kasashen Afirka ta hanyoyin mota ake yin su, wanda yake haifar da jinkiri mai tsawo a kan iyakokin kasashen musamman a wannan yanayi na cutar korona," inji Ms Hartzenberg.

Truck driver Likando Mwiya
Bayanan hoto, Direban mota Likando Mwiya ya ce matsalar ratsa iyakokin kasashe da kuma annobar korona na kawo cikas matuka ga kokarin shigar da kayayyaki kasashen Afirka

Inganta hanyoyin biyan kudade

Wani kalubalen shi ne inganta hanyoyin biyan kudade na zamani kan kayan da akae shigar wa kasashen Afirka.

Kevin Njiraini, regional director of International Finance Corporation (IFC), the World Bank's private sector arm
Bayanan hoto, Kevin Njiraini na kamfanin IFC ya ce inganta hanyoyin biyan kudade na zamani kan kayan da akae shigar wa kasashen Afirka

Kevin Njiraini, daraktan yanki na International Finance Corporation (IFC), wanda reshe ne na Bankin Duniya ya ce inganta hanyoyin biyan kudade na zamani kan kayan da akae shigar wa kasashen Afirka

Wani dan kasuwa daga Najeriya mai suna Shola Akinlade ya kafa kamfanin Paystack tare da wasu a 2016 domin samr wa 'yan kasuwan da ke cin kasuwa a Ghana da Najeriya iya karban kudadesu daga ko ina a duniya.

Paystack ya bunkasa, domin shi ne ke sarrafa fiye da kashi 50 cikin 100 na dukkan kudaden da ake biya ta intanet a Najeriya, kuma akwai kamfanoni fiye da 60,000 ciki har da FedEx, da UPS da kamfanin sadarwa na Afria ta Kudu wato MTN.

Paystack founders Ezra Olubi and Shola Akinlade

Asalin hoton, Paystack

Bayanan hoto, Masu kamfanin Paystack Ezra Olubi da Shola Akinlade sun kafa kamfanin ne a 2016

Akwai sauran matsalolin da tilas a magance kafin kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar Afirka ya bunkasa, kamar bukatar nan ta kasashen su rika fitar da kayansu maimakon shigarwa kawai.

"Sannu a hankali komai zai bunkasa - yarjejeniyar cinikayya babu shingaye ta ACFTA na iya janyo masu zuba jari daga kasa da kasa domin su rika samar da kayayyaki a cikin kasashen Afirka," inji ta.

"Afirka na bukatar bunkasa yawan kayan da ta ke samarwa, kuma wannan na cikin darussan da aka koya musamman a wannan lokaci na annobar korona."