Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka ke bunƙasa duk da annobar cutar korona
- Marubuci, Daga Mary-Ann Russon
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a shaa'nin kasuwanci
- An wallafa
A bara wasu kasashen Afirka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka kafa domin bunkasa kasuwanci tsakaninsu. Idan aka yi nasarar aiwatar da yarjejeniyar, suna ganin za a iya samar da wata katafariyar kasuwa mai fiye da mutum biliyan ɗaya.
Tsarin wannan yarjejeniyar shi ne a samar da hanyar da kayayyaki za su rika shiga kasashen da ke cikin shirin ba tare da shingaye ba, wanda zai mayar da nahiyar ta zama irinta mafi girma a duniya.
Wannan yarjejeniyar na iya samar da kasuwar da darajar ta ya kai dala tiriliyan 3 inji kamfanin Brookings na Amurka.
A halin yanzu Afirka na bayan sauran yankunan duniya a fagen kasuwancin cikin gida. Bankin raya Afirka (ADB) ya ce kashi 16.6 na cinikayyar duniya ne kacal Afirka ke mora.
Amma abin damuwar shi ne yarjejeniyar ACTFA da kasashen Afirka suka samar domin yin kasuwanci babu shingaye tsakaninsu bai fara aiki ba ranar 1 ga watan Yuli saboda annobar korona, amma akwai wasu dalilan.
Trudi Hartzenberg, babbar shugabar cibiyar da ke sa ido kan dokokin kasuwanci (Tralac) da ke Stellenbosch a Afirka ta Kudu na ganin tattaunawa kan batun na tafiya sannu a hankali amma an ci karo da wasu batutuwa.
"Tataunawar na da sarkakiya matuka saboda kasashen da ke ciki za su rasa wani bangare na kudadewn shigan da suke samu. Rage haraji na nufin za su rasa yawancin kudaden shiga kamar yadda suka saba samu a da." inji ta.
Karamar rigar da aka sayo daga China zuwa wata kasar da ke cikin kungiyar cinikayya ta kasashen kudancin Afirka za a iya saka ma ta harajin kashi 45, kuma babu wata hanyar maye gurbin wannan harajin idan aka koma ga sayen kayan daga kasashen cikin nahiyar, inji Ms Hartzenberg.
Amma duk da haka jami'ai daga kasashen nahiyar sun jurewa wadannan jerin kalubalen.
Tattauanwar da ake yi yanzu ta koma ta intanet, inda ake amfani da na'urar Zoom domin tattaunawa kai tsaye, kuma a watan Mayu aka fara tattaunawar. Sai dai akawai matsalar samar da sabis mai kyau.
Matsalar sufuri a lokacin korona
Ban da rashin ingancin hanyoyin sadarwa da hanyoyin sufuri wadatattu tsakanin kasashen Afirka, isowar annobar korona ta dagula lamurra matuka.
"Yawancin cinikin da ke wakana tsakanin kasashen Afirka ta hanyoyin mota ake yin su, wanda yake haifar da jinkiri mai tsawo a kan iyakokin kasashen musamman a wannan yanayi na cutar korona," inji Ms Hartzenberg.
Inganta hanyoyin biyan kudade
Wani kalubalen shi ne inganta hanyoyin biyan kudade na zamani kan kayan da akae shigar wa kasashen Afirka.
Kevin Njiraini, daraktan yanki na International Finance Corporation (IFC), wanda reshe ne na Bankin Duniya ya ce inganta hanyoyin biyan kudade na zamani kan kayan da akae shigar wa kasashen Afirka
Wani dan kasuwa daga Najeriya mai suna Shola Akinlade ya kafa kamfanin Paystack tare da wasu a 2016 domin samr wa 'yan kasuwan da ke cin kasuwa a Ghana da Najeriya iya karban kudadesu daga ko ina a duniya.
Paystack ya bunkasa, domin shi ne ke sarrafa fiye da kashi 50 cikin 100 na dukkan kudaden da ake biya ta intanet a Najeriya, kuma akwai kamfanoni fiye da 60,000 ciki har da FedEx, da UPS da kamfanin sadarwa na Afria ta Kudu wato MTN.
Akwai sauran matsalolin da tilas a magance kafin kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar Afirka ya bunkasa, kamar bukatar nan ta kasashen su rika fitar da kayansu maimakon shigarwa kawai.
"Sannu a hankali komai zai bunkasa - yarjejeniyar cinikayya babu shingaye ta ACFTA na iya janyo masu zuba jari daga kasa da kasa domin su rika samar da kayayyaki a cikin kasashen Afirka," inji ta.
"Afirka na bukatar bunkasa yawan kayan da ta ke samarwa, kuma wannan na cikin darussan da aka koya musamman a wannan lokaci na annobar korona."