Abin da muka sani kan gagarumin sabon makami mai linzami na Koriya Ta Arewa

Asalin hoton, Reuters
Kori ta Arewa ta ƙaddamar da wani makamin roka da hatsarinsa ya bai wa masana harkokin makaman ƙasar mamaki.
Melissa Hanham ta yi bayani kan yadda makamin yake da kuma yadda aka yi ya zama barazana ga Amurka.
Yayin bikin cika shekara 75 na jam'iyyar Workers' Party a Koriya ta Arewa, an gudanar da wani faretin sojoji da tsakar dare.
An gudanar da dukkanin abin da ake tsammanin gani daga ƙasar ciki har da wani jawabi da Shugaba Kim Jong-un ya yi mai sosa zuciya, inda ya riƙa zubar da hawaye.
A ƙarshe kuma aka gabatar da wani gagarumin makami mai linzami mai cin dogon zango mafi girma da ta mallaka zuwa yanzu.
Ga wasu abu uku da muka sani game da makamin mai linzami.

Asalin hoton, Reuters
Alƙawarin Shugaba Kim na 'makami na musamman'
A ranar 1 ga watan Janairun 2020, Mista Kim ya yi jawabin Sabuwar Shekara, inda ya sanar da cewa Koriya Ta Kudu "na ƙirƙirar wasu makamai na musamman da manyan ƙasashen duniya ne kaɗai ke da su".
Ya fayyace cewa na "musamman" - abin da ke nufin makamin nukiliya.
Kim ya alaƙanta makamin da Amurka, yana mai cewa "idan Amurka ta ci gaba da jan ƙafa a shirin gyara dangantakarta da Koriya to za ta ci gaba da fuskantar barazana daga Koriya Ta Arewa wadda ke ƙara samun ci gaba".
Sabon makamin na ICBM cika alƙawari ne da Kim ya yi. Yana harar Amurka ne yayin da tattaunawar gyara dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta gaza ɗorewa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Trump.
Sabuwar barazana ga tsaron Amurka
Da ma tuni Koriya Ta Kudu ke da makamai masu linzami biyu da ta gwada. An gwada The Hwasong-14 sau biyu a 2017 mai cin zangon kilomita 10,000 wanda zai iya kai wa kusan ko'ina a Yammacin Turai sannan zai kai kusa da Amurka ɗauke da bam ɗin nukiliya guda ɗaya.
Shi kuma The Hwasong-15 an gwada shi a 2017, yana tafiyar kilomita 13,000, abin da ke nufin zai iya kai wa ko'ina a cikin Amurka ɗauke da bam ɗin nukilya.

Asalin hoton, Getty Images
Ba za mu iya sanin haƙiƙanin nisan tafiyarsa ba har sai an gwada shi ko kuma an bayyana injinansa.
Sai dai hakan na nufin abu guda ɗaya: ba sai sun sake haɓaka nisan makamansu ba.
Ƙasashen da ke da manyan makamai na da motocin da ke ɗaukar bam ɗin nukiliya da yawa a mota ɗaya mai suna multiple independent re-entry vehicles (MIRV) - ita ma Koriya Ta Arewa abin da take son yi kenan.
Abin da ke jawo fargaba
Har yanzu akwai abin da ba a gama ba game da ƙirar makamin ICBM, abin da ke sa ake tambayar lokacin da za a gwada shi.
Ɗaya daga cikin abin da ke dakatar ƙasar daga shiga yaƙin nukilya shi ne ƙarancin na'urorin da ke harba shi - ana iya harba makami mai linzami ne da yawan na'urorin da ake da su na harba shi.

Asalin hoton, Reuters
Amurka ta yi hasashen cewa Koriya Ta Arewa za ta iya harba makaman ICBM guda 12 ne kawai a lokaci guda. An yi lissafin kan yawan na'urorin harba makaman da ƙasar ke da su guda shida da aka sani, ta yadda za ta harba guda ɗaya sannan ta harba na biyu kafin Amurka ta mayar da martani.
A shekarar 2010, ƙasar ta sayo na'urar WS51200 guda shida ta ɓarauniyar hanya sannaan ta gyara su zuwa na harba makaman, waɗanda kuma take nunawa a kodayaushe.

Asalin hoton, Getty Images
Da alama har yanzu ƙasar kan iya sayo na'urorin harba makamai duk da takunkumin da ke kanta.
Kazalika, tana ƙara ɗaukaka ƙarfinta na ƙirƙirar makaman nukilya da kanta.
Wannan sabon makami mai linzami, wanda aka ƙirƙire shi cikin shekara maras daɗi, na nuna wa sauran ƙasashe cewa kar su ɗauki ƙasar lakwalakwa ko shugabanta ko kuma ƙarfin ilimin kimiyyarta.










