North Korea: Abin da ya sa Kim Jong-un ya dakatar da ɗaukar matakin soji kan Kudu

Kim Jong-un, Moon Jae-in and Kim Yo-jong

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kim Jong-un and South Korea's Moon Jae-in in better days
An wallafa

Koriya Ta Arewa ta dakatar da shirinta na ɗaukar matakin soji kan Kudu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

A makonnin da suka gabata an yi ta ganin irin abubuwan da Koriya Ta Arewa ta yi cikin ɓacin rai kan yadda kungiyoyin da suka gudu daga Koriya Ta Arewa zuwa ta Kudu da suke tura sakwannin farfaganda suka ringa izawa.

A makon jiya ne Koriya Ta Arewa ta tarwatsa wani ofishin hadaka tsakaninta da Koriya Ta Kudu, a garin Kaesong da ke kusa da iyakar kasashen biyu.

A wani taro da Kim Jong-un ya jagoranta ya ce an dauki matakin ne don dakatar da tura sojojin.

Kwamitin Soji na kasar ya yanke shawararsa bayan yin nazari kan yanayin da ake ciki.

Arewar ta kuma cire lasifikun da ta daddasa a makon da ya gabata, wadanda ake amfani da su wajen aike sako ga Kudu a kan iyaka, kamar yadda Yonhap ta ruwaito.

"Taron ya kuma tattauna kan takardun yadda matakan za su kasance don ci gaba da dakatar da batun yakin," in ji kamfanin dillancin labarai na KCNA.

Presentational grey line

Wasu masu sharhi sun fito da batun yiyuwar Mr Kim na iya biye wa kanwarsa ne kan wasu tsare-tsaren. Kar ku manta cewa dakatar da aike sojoji aka yi ba fasawa ba gaba daya - don haka da sauran rina a kaba.

Irin wannan rikicin na yawan bai wa 'yar uwar Kim Jong-un dama don nuna kwazonta na cewa za ta iya shugabanci, amma dai har yanzu mun san wanda ke jan ragamar mulkin.

Presentational grey line