Ban kwana, Tottenham 0-2 Chelsea - Watford 2-0 Man United
Nan muka kawo karshen sharhi da rahotannin kai-tsaye na wasannin mako na 18.
'Yan United sorinku, 'yan Chelsea barkanku.
Mu hadu a wasanni na gaba.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kawo maku sharhi da bayanai ka-tsaye game da wasannin Premier mako na 18.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Nan muka kawo karshen sharhi da rahotannin kai-tsaye na wasannin mako na 18.
'Yan United sorinku, 'yan Chelsea barkanku.
Mu hadu a wasanni na gaba.
Chelsea ta doke Tottenham da ci 0-2 har gida a wasan Premier mako na 18.
Dan wasan Chelsea Willian ne ya ci kwallo biyun duka, wanda hakan ya bai wa kungiyarsa damar tsira da maki uku a fafatawar.
A minti na 12 da fara wasan ya jefa kwallo ta farko cikin wani salo na kwarewa bayan ya dakko ta ta bangaren hagu kuma ya buga ta tsakanin 'yan bayan, ta fada raga.
Ana daf da juyawa hutun rabin lokaci ne Chelsea ta samu finareti, bayan wata haduwa da aka yi tsakanin golan Tottenham Gazzaniga da dan bayan Chelsea Alonso.
Ya dauki alkalin wasan kusan minti uku kafin a gama tabbatar da ko finareti ne ko akasin haka, daga karshe kuma aka gano finareti ne kuma take Willaim ya ci.
Tottenham ta dawo da karsashinta daga hutun rabin lokacin da nufin rama kwallayen da aka zira mata.
Sai dai a minti na 62 Son Heung-min ya yi ketar ramuwa ga Rüdiger, wanda hakan ya jawo aka kore shi daga wasan.
Wannan ne jan kati na uku da dan wasan ya samu a shekarar 2019, wanda rabon da a yi hakan tun 2010 da Lee Cattermole ya samu.
Yanzu dai Chelsea ta bayar da tazarar maki hudu ga Sheffield United da ke biye mata, maki shida kuma ga Tottenham da ta cinye a yau.
An samu hayaniya yayin wasan daga magoya bayan Tottenham - kalaman nuna wariyar launin fata daga magoya baya suka rika furtawa.
Hakan ya janyo an yi sanarwa har sau biyu a lasifika. Sanarwar ta ce: "Ku sani babu wata damar nuna kalaman wariyar launin fata a harkar kwallon kafa."
Wannan ce rashin nasara ta farko da Jose Mourinho ya gamu da ita a gida tun bayan karbar aikin horar da Tottenham da ya karba a watan da ya gabata.
Hayaniyar da aka fuskanta dazu a wasan sanarwa aka yi a lasifika, game da kalaman nuna wariyar launin fata daga magoya baya yayin wasan.
Abin da sanarwar ta ce shi ne, "ku sani babu wata damar nuna kalaman wariyar launin fata a harkar kwallon kafa."
Tottenham ba ta buga kwallon ci ba a kaf wasan, wannan ba karamin koma baya bane ga kungiyar.
Alonso ne ya rike Dele Alli a cikin yadi na 18 nafin a dakko kwana har sai da yakai shi kasa, sai dai alkalin wasa bai ce komi ba.
Mourinho na ta hayaniyar an hana shi damar da ya samu.
Eriksen ya buga amma Butshuayi ya fidda ita.
An cire Jan an sako Rose.
Batshuayi ya karbi Abraham, Azpilicueta ya bai wa James ya dana
Antonio Rudiger ya karbi katin gargadi, bayan tare wa Sanchez hanya da ya yi.
Ndombele ya sauya Lucas
Son shi ne dan wasa na farko da ya samu jan kati sau uku a shekara guda a Premier, tun bayan wanda Lee Cattermole ya samu a 2010.
Har yanzu da karsashi jikin 'yan wasan Tottenham kamar ba a bada jan kati ba.
An fidda Kovacic Jorginho ya shigo.
Magoya bayan Tottenham na nuna fusatarsu game da jan katin da aka bai wa Son.
An kori Son sakamakon ketar ramuwa da ya yi wa Rüdiger.
An gano nhakan ne bayan amfani da na'urar VAR, wanann ba karamin hukunci ba ne.
Sissoko ya karbi katin gargadi.
Kiris ya hana Chelsea ta kara kwallo ta uku, bayan da Abraham da Mount suka bata wata kwallo a junansu amma 'yan bayan Tottenham suka tare kwallon.
Da an ci kwallon da hankalin Lampard ya kwanta