Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Afirka

    Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta duniya reshen Afirka ta ce ana samun karuwar yaduwar coronavirus a nahiyar.

    Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter ya ce ya zuwa yanzu mutum 795 ne suka kamu da cutar a kasashe 36. Kasashen su ne: Algeriya (82), Benin (2), Burkina Faso (27), Kamaru (16), Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (1), Chadi(1), Congo(1), Ivory Coast (6), Djibouti (1), Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo (14), Masar (256).

    Sai kuma Equatorial Guinea (4), Eswatini (1), Habasha (9), Gabon (3), Gambiya (1),Ghana (7), Guinea (2), Kenya (7), Liberiya (2), Mauritius (7), Mauritaniya (2), Maroko (63), Namibiya (2), Nijar (1), Najeriya (12), Rwanda (11), Senegal (38), Seychelles (6), Somaliya (1), Afrika ta Kudu (150), Sudan (1), Tanzaniya (6), Togo (1), Tunisiya (39), da kuma Zambiya (2).

    Kazalika hukumar ta ce akwai kasashe takwas da aka samu wadanda suka warke daga cutar. Kasashen su ne: Algeriya(32), Kamaru(2), Masar (28), Morocco 2), Najeriya(2), Senegal(5), Afirka ta kudu (12), da kuma Tunisia(1).

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. An samu mutum na farko mai dauke da coronavirus a Chadi

    Shugaban Chadi ya ce wa 'yan kasarsa su kwantar da hankalinsu bayan da aka samu mutum daye dauke da cutar coronavirus a kasar ranar Alhamis.

    Shugaba Idriss Deby ya ce "Dole ne mu bi dokokin tsafta da sauran matakai da ya kamata," a shafinsa na Twitter:

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    A daren Alhamis ne Chadi ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a kasar tsawon kmako biyu, amma ban da jiragen dakon kaya. Haka kuma za ta rufe wasu iyakokinta na kasa.

    Sannan an hana taron mutane sama da hamsin a wuri guda.

  3. An dakatar da fasto saboda ya ce coronavirus ba gaskiya ba ce

    Wata coci a Kenya ta dakatar da wani fasto saboda ya ce coronavirus ba gaskiya ba ce sannan ya yi shagube kan umarnin da hukumomin kiwon lafiya suka bayar na wanke hannu domin kauce wa kamuwa da cutar.

    A farkon makon nan ne fasto Nathan Kirimi na Cocin Jesus Winner Ministry da ke Meru, a tsakiyar Kenya, ya caccaki wasu coci-coci saboda sun rufe wuraren ibadarsu sakamakon fargabar kamuwa da coronavirus.

    Ya ce an kirkiro cutar ne domin a yaki Kiristoci, yana mai yin kira ga mabiyansa su ci gaba da zuwa coci domin yin ibada.

    Sai dai shugabannin cocin sun yi alla-wadai da kalaman nasa sanan suka dakatar da cocin.

    Shugaban rukunin cocin Fasto Edward Mwai ya ce kalaman da fasto Kirimi ba ra'ayin cocin ba ne, sanna ya ce za su yi biyayya ga umarnin gwamnati na dakatar da tarukan jama'a.

    Coci-coci da dama da suka dakatar da ibada ta jam'i sun ce za su yi wa'azi ga mabiyansu ta hanyar intanet.

  4. Philippines ta haramta wa baki shiga kasar saboda coronavirus

    Ma'aikatar sufurin Philippines ta ce daga daren ranar Lahadi ba za a sake bari wani wanda ba dan kasar ba shiga cikinta.

    Tuni aka dakatar da jirage daga tashi daga babban birnin kasar Manila zuwa wasu kasashen ko kuma shiga cikinta, sannan an rufe makarantu yayin da aka bai wa sojoji da 'yan sanda umarnin sanya ido a wuraren killace wadanda suka kamu da cutar coronavirus.

    Kazalika an sanya dokar hana fita ba dare ba rana.

    Yanzu haka mutum 217 aka tabbatar sun kamu da coronavirus a Philippines ko da yake masana kiwon lafiya sun ce alkaluman sun fi haka.

    An tura jami'an tsaro cibiyoyin killace masu fama da cutar

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Coronavirus: Mutanen da suka mutu sun zarta 10,000 - Jami'ar Johns Hopkins

    Mutanen da suka mutu a fadin duniya sakamakon kamuwa da coronavirus sun zarta 10,000, a cewar Jami'ar Johns Hopkins.

    Jami'ar da ke Amurka. - wacce ta soma tattara alkaluman mutanen da suka kamu da cutar tun lokacin da ta barke a karshen shekarar da ta wuce - ta ce yanzu alkaluman mutanen da suka kamu da cutar sun kusa kai wa 250,000.

  6. Coronavirus: An rufe Masallacin Annabi SAW da Masallacin Harami

    Hotunan Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina da kuma Masallacin Harami wadanda hukumomin Saudiyya suka wallafa a shafukan sada zumunta ranar Juma'a.

    Kamar yadda kuke gani, babu kowa a cikinsu.

    Ranar Alhamis, hukumomin kasar suka bayar da sanarwar rufe Masallatan suna mai cewa liman ne kawai za a bari ya yi sallah tare da wasu tsirarun mutane.

    Hasalima mahukuntan kasar sun ce ba za a yi sallar Juma'a a masallatan ba.

    Sun ce sun dauki matakin ne domin tsoron yaduwar cutar covid-19.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  7. Coronavirus: Za a rufe wasu filayen jiragen saman Najeriya

    Hukumomi a Najeriya sun bayar da umarnin rufe wasu filayen jiragen saman kasar saboda fargabar cutar covid-19.

    Sanarwar da hukumar kula da sufurin jiragen saman Najeriya ta fitar ta ce za a rufe filayen jiragen saman Malam Aminu Kano da ke Kano; filin jirgin saman Akanu Ibiam, Enugu; da kuma filin jirgin saman Fatakwal da ke jihar Ribas.

    Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan shafukan zumunta, Bashir Ahmad, ya ambato shugaban hukumar kula da jiragen sama, Musa Nuhu, yana cewa za a rufe filayen jiragen ne ranar Asabar, 21 ga watan Maris na 2020.

    A cewarsa, za a ci gaba da amfani da filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja da filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos ya zuwa wani lokaci, amma ba za a bar jiragen da suka taso daga kasashe 13 da gwamnati ta hana zuwa Najeriya su shigo kasar ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Barkamu da wanna rana ta Juma'a

    Muna yi wa masu bin mu a wannan shafi barka da warhaka. Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku a wannan safiya inda za mu kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman gae da cutar coronavirus da ta addabi duniya.

    Baya ga wanna batu, za mu kawo muku bayanai kan wasu batutuwan na daban.

    Da fatan za ku kasance tare da mu, kua za ku bi umarnin masana kiwon lafiya kan wannan cuta.

    Kuna iya komawa kasan wannan shafi don karanta abubuwan da suka faru a jiya Alhamis idan har ba ku samu karanta su ba.

  9. Sai da safenku

    Mun zo karshen rahotannin kai-tsaye ba don labaran sun kare ba. Amma za mu ci gaba da wallafa sabbin labarai a babban shafinmu.

    Mu hadu da ku ranar Juma'a idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya - kar a manta da tsaftar jiki, musamman hannaye sannan a guji mu'amalar da ba ta zama dole ba saboda coronavirus.

    Dalibai masu rubuta jarrabawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasu dalibai sanye da takunkumin kariya a daga kwayar cutar Coronavirus yayin da suke daukar jarrabawa a wata makaranta da ke garin Ahmedabad a Indiya ranar Alhamis
  10. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta bulla a Nijar

    Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a kasar.

    Mutumin dan kasar Nijar ne mai shekara 36.

  11. Za a rufe makarantun Kano daga Litinin saboda coronavirus

    'Yan makaranta

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi umarni a rufe dukkan makarantu a jihar sakamakon fargabar ci gaba da yaduwar cutar coronavirus.

    Kwamishinan ilimi a jihar Sanusi Sa'idu Kiru ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

    Kwamishinan ya ce za a rufe makarantun daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

    Ya kara da cewa iyaye su tabbata sun dauko 'ya'yansu daga makarantun kwana daga ranar Lahadi.

    "Ba a rufe makarantun ba domin saka tsoro a zukatan jama'a sai don daukar matakin kare kai daga cutar coronavirus," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar 'ya'yansu sun kasance a gida da kuma taimaka musu wurin tsaftar jiki.

  12. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta bulla Nijar

    Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a kasar.

    Mutumin dan kasar Nijar ne mai shekara 36.

  13. Labarai da dumi-dumi, Za a rufe manyan makarantu a Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarni a rufe dukkanin manyan makarantun gaba da sakandare a kasar domin yaki da yaduwar cutar coronavirus, a cewar rahoton jaridar intanet ta TheCable.

    Jaridar ta ambato babban sakatare a ma'aikatar ilimi ta Najeriya mai suna Sonny Echono yana bayar da umarnin a ranar Alhamis.

    "Mun bayar da umarnin rufe manyan makarantu a karshen makon nan. Makarantun sakandaren gwamnatin tarayya da suka gama rubuta jarrabawarsu za su rufe nan take. Sauran za su gaggauta rufewa ranar 26 ga watan Maris," Sonny Echono ya fada a wata sanarwa.

  14. Ba a samu Coronavirus a Abuja ba – NCDC

    Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta Nigeria Center for Disease Control (NCDC) ta karyata labarin da ke yawo a intanet cewa an samu mai dauke da cutar Covid-19 a yankin Apo na Abuja.

    Hukumar ta ce wasu ne suka gurbata hotunan bayan da take wallafawa a shafukanta domin yada fargaba a zukatan al'umma.

    "Mun roke ku da ku yi watsi (da labarin) sannan ku biyo mu. Duk sanda aka samu wanda ya kamu za mu sanar muku," in ji NCDC.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Gaisuwar Coronavirus tsakanin Buhari da Pantami

    Bayanan bidiyo, Gaisuwar Coronavirus tsakanin Buhari da Pantami

    Ba mu sani ba ko kun ci karo da wannan bidiyon na Shugaba Buhari na Najeriya da Ministan Sadarwar kasar Isa Ali Pantami a shafukan sada zumunta.

    Mutanen biyu sun hadu ne yayin kaddamar da wasu ayyuka a ma'aikatar sadarwa ta Najeriya, inda suka yi gaisuwar nesa-nesa saboda coronavirus.

    Shugabannin kasashe na ci gaba da bayyana wa 'yan kasarsu halin da ake ciki game da cutar da ke ci gaba ratsa kasashe tare da halaka daruruwan mutane a fadin duniya.

    Sai dai har yanzu Buhari bai ce komai ba da bakinsa ga 'yan Najeriya. Mun duba muku dalilin da ya sa bai yi hakan ba.

    Mutum sama da 200, 000 ne suka kamu sannan wasu sama da 8,000 suka mutu a fadin duniya, inda wasu kusan 80,000 suka warke.

  16. Coronvirus za ta kashe miliyoyin mutane idan ba a farga ba – Guterres

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi gargadi ga shugabannin duniya a kan aikin hadin gwiwa domin dakile yaduwar cutar Coronvirus.

    "Idan muka bar cutar nan ta ci gaba da yaduwa - musamman a yankuna marasa galihu - za ta kashe miliyoyin mutane. Haduwar duniya wuri guda ba wai abin da ya kamata ba ne kawai, abin da ya zamar wa kowa dole ne," Mista Guterres ya fada.

    "Tsarin kiwon lafiyar da ke fuskantar barzana a yanzu ya nuna karara cewa karfinmu bai wuce na abin da muke da shi ba."

    Mista Guterres ya kuma shawarci gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa da su agaza wa marasa karfi da tallafin kudi da kuma matsakaitan 'yan kasuwa.

    Ya kara da cewa durkushewar tattalin arzikin duniya "ya kusa tabbata".

  17. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutum 427 sun mutu a Italiya a rana guda, ta zarce China

    Italiya ta tabbatar da wasu karin mutum 427 sun mutu a cikin awa 24 da suka gabata, abin da ya kai adadinsu zuwa 3,405.

    Saboda haka yanzu mutanen da suka mutu a Italiya sun fi na China yawa - kasar da cutar ta samo asali.

  18. Za a rufe makarantu a Abuja saboda Coronavirus

    Yara 'yan makaranta

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomni a babban birnin Najeriya Abuja sun ce za su rufe makarantu a fadin birnin daga gobe Juma'a domin dakile yaduwar cutar coronavirus, wadda ke haddasa Covid-19.

    Da take bayar da sanarwar a wani taron shugabannin ma'aikatu da ke karkashinta, Karamar Minsitar Abuja Dr. Ramatu Tijjani Aliyu ta yi umarni da makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da su rufe su har sai baba ta gani.

    Ministar ta kuma yi umarni da a takaita taruwar jama'a wuri guda tare da rufe wuraren addini domin guje wa taruwar mutane da zai jawo yaduwar cutar.

    Kazalika ta jaddada cewa masu shagunan da suka gaza samar da sinadarin wanke hannu da kuma sauran kayayyakin kariya daga cutar za a rufe shagunan nasu nan take.

    "Kun sani cewa wasu jihohin sun riga mu wurin rufe makarantu, mu ma a nan fadar gwamnati ba za mu rungume hannayenmu ba muna kallon lamarin," in ji Ramatu Tijjani.

    "Daga gobe Juma'a, za a rufe duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu a Abuja ba tare da wani bata lokaci ba."

  19. Za a yi amfani da kwayar chloroquine don magance coronavirus

    Kwayar chloroquine

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta sahale amfani da maganin zazzabin Maleriya na chloroquine wurin magance cutar coronavirus, a cewar Shugaba Donald Trump.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a wurin taron manema labarai da ya gudanar a yau Alhamis a fadar White House.

    "Za mu samar da wannan kwayoyi nan take kuma hukumar kula da abinci da magunguna tana aiki tukuru," Trump ya bayyana.

    "An gama gwada kwayoyin - sannan an yarda a yi amfani da su. Sun tanade su tun watanni da suka wuce. Saboda haka za mu samar da su ta yadda likitoci za su rika rubuta wa marasa lafiya."

  20. Bollywood ta dakatar da daukar fim saboda Coronavirus

    Shah rukh khan

    Asalin hoton, Getty Images

    Yadda cutar coronavirus ke yaduwa a duniya ta sa masana'antar fina-finan Indiya ta Bollywood ta dakatar da daukar duk wani fim da ake yi a yanzu har zuwa 31 ga watan Maris 2020.

    Matakin ya biyo bayan tattaunawar da masu ruwa da tsaki a masana'antar suka yi.

    An umarci dukkan masu shirya fim da su dawo daga inda suka je daukar fim ko a cikin kasar ko kuma a wajen kasar.

    Masana'antar ta ce ta dauki wannan matakin ne domin kauce wa kamuwa da yaduwar cutar.