Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Mutum 70 sun sake kamuwa da coronavirus a Saudiyya

    Saudiyya

    Asalin hoton, Saudi Gazzette

    Mutum 70 sun sake kamuwa da cutar Covid-19 a Saudiyya, a cewar rahoton kamfanin dillancin labaran kasar na Saudi Press Agency (SPA).

    Ma'aikatar lafiya ta Saudiyya ta ce mutanen sun hada da wasu mutum 11 da suka shiga kasar daga kasashen Morocco da Indiya da Jordan da Birtaniya da Philippines da Daular Larabawa (UAE) da kuma Switzerland.

    An kai wadanda suka kamu asibiti nan take daga filin jirgin sama domin killacewa. Mutum 58 ne suka yi mu'amala da mutanen, wasunsu ta hanyar haduwa a wurin shagalin aure, wasu kuma a taron iyali.

    Jumullar mutum 344 ne suka kamu da cutar a Saudiyya zuwa yanzu, wasu takwas suka warke ba tare da an samu rasa rai ba.

  2. Ministocina na aiki ba dare ba rana kan Coronavirus – Buhari

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya ya ce yana da "cikakken kwarin gwiwa" kan ministoci da jami'an lafiyar kasar a yakin da Najeriya ke yi da cutar coronavirus.

    Wannan magana ta shugaban na zuwa ne yayin da wasu ke sukarsa kan yadda ya yi gum da bakinsa a lokacin da sauran shugabannin duniya ke yi wa 'yan kasarsu bayani kan yadda suke yaki da cutar a kasashensu.

    Tun da aka fara fama da wannan cuta a Najeriya Buhari bai yi wa kasa bayani ba amma mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya bayyana dalilin da ya hana shi yin maganar.

    "Kare hakkin 'yan Najeriya na cikin kudirin wannan gwamnati," Buhari ya wallafa a Twiiter. "Muna da hukumar yaki da yaduwar cutuka ta NCDC da Ma'aikatar Lafiya da ke aiki ba dare ba rana."

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Ya kara da cewa: "Ina da cikakken kwarin gwiwa kan ministocina da ke da alhakin abin da kwamiti na musamman da na kafa kwanan nan da kuma jami'an hukumar NCDC, wadanda suke bayar da bayanai a-kai-a-kai da kuma shawarwari."

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  3. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutum 627 sun mutu a Italiya a rana guda

    Wadanda suka mutu a Italiya sakamakon cutar coronavirus sun karu da 627, in ji hukumomi.

    Wannan ne adadi mafi yawa na rana guda da aka samu a kasar tun da aka fara annobar.

    Adadin wadanda suka mutu jumulla ya kai 4,032.

  4. Iraniyawa sun yi bikin Nowruz duk da coronavirus

    Iran

    Asalin hoton, AFP

    Diuk da yadda annobar coronavirus ta addabi kasar Iran, jama'a sun yi bikin sabuwar shekarar Nowruz a kasar.

    Mahukunta sun shawarci mutane da su guji ziyarce-ziyarce yayin da ake shirin fara bikin na mako biyu, wanda shi ne mafi muhimmanci a kalandar Iran.

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Sai dai a babban birnin kasar Tehran mutane sun yi watsi da gargadin, inda suka fita domin sayen kyautuka ga 'yan uwa da masoyansu.

    Iran

    Asalin hoton, AFP

    Iran

    Asalin hoton, AFP

  5. Coronavirus: Gwamnatin Ekiti ta ce ma'aikata su zauna a gida

    Gwamnatin Ekiti a Najeriya ta ce duka ma'aikatan gwamnati da za su iya iaki daga gida su yi hakan daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris.

    Sanarwar da aka yi a shafin Twitter ta ce ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa kasa za su iya yin aikinsu daga gida amma ban da ma'aikatan lafiya da 'yan kwana-kwana da masu gadi da dai sauransu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Gwamnatin ta kuma bukaci jami'an gwamnati su bar wayoyinsu a kunne domin za a iya bukatarsu.

    Sanarwar ta ce a rufe duka kanana da manyan makarantu a jihar daga ranar Litinin din.

  6. Najeriya za ta rasa 45% na kudin shigarta saboda faduwar farashin mai

    Ministar kudin Najeriya

    Asalin hoton, @ZShamsuna

    Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta ce Najeriya za ta rasa kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarta da ta tsara za ta samu sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.

    Farashin danyen man fetur ya yi faduwar bakar tasa ne saboda kamun kazar kuku da annobar coronavirus ta yi wa manyan kasashen da suka fi sayen man irinsu China da kuma rashin cimma matsaya tsakanin Saudiyya da Rasha kan yawan man da za su rika fitarwa a kullum.

    Ministar kudin tana wannan batu ne a ranar Laraba, inda ta ce hakan ya tilasta wa Najeriya ragewa da kuma kwaskwarima ga ayyukan da gwamnatin Buhari ta tsara za ta yi.

    "Raguwar farashin man fetur daga dala 57 a kan kowacce ganga zuwa dala 30 da muka saka a kasafin kudi yana nufin cewa za mu yi asarar kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarmu," in ji ministar.

    "Saboda haka wajibi ne mu yi kwaskwarima ga wasu ayyuka da kuma kasafin kudi domin ya dace da abin da ke kasa."

    Ministar ta kuma ce shugaban kasa ya bayar da umarnin a yi shirin ko-ta-kwana kan yadda za a yi ayyuka da farashin man na yanzu kan dala 30 a kowacce ganga daya.

    "Wannan shirin gaggawa da za mu yi ya tilasta mu rage wasu ayyukan raya kasa duk da cewa muna ci gaba da duba hanyoyin habaka kudaden shigar da farashin man bai shafe su ba.

    "Saboda haka za mu tabbatar cewa an ci gaba da hako ganga miliyan 1.8 da muka yi hasashe a kasafin kudi.

    "Sannan kuma mun rage yawan kudin shigar da hukumar kwastam za ta samu daga tiriliyan 1.5 saboda mun fuskanci cewa kasuwanci zai ragu kuma idan kasuwanci ya ragu kudin shiga ma zai ragu."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Coronavirus: Mutum na farko da ya kamu da cutar a Togo ya warke

    coronavirus

    Asalin hoton, AFP

    Mutum na farko da ya kamu da covid-19 a Togo ya warke amma har yanzu yana asibiti ana ma shi ido, in ji ministan lafiyar kasar kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

    A halin yanzu dai mutum 8 ne ke dauke da cutar a kasar.

    Gwamnati ta bukaci baki ke zuwa Togo da su kula kuma su yi aiki da hukumomi don dakile yaduwar cutar, in ji ministan lafiya Moustafa Mijiyawa.

    Ya bukaci al'ummar kasar su kwantar da hankalinsu amma su bi dokoki tsare kawunansu kamar yadda gwamnati ta ce.

  8. Coronavirus 'ta kashe wani mawakin' kasar Congo

    Wani mawaki dan kasar Congo Aurlus Mabele ya mutu a asibitin Paris, babban birnin Faransa, yana da shekara 67 a duniya.

    Sakonnin da abokansa da 'yan uwa suka wallafa a shafukan sada zumunta sun ce mawakin ya mutu ne sakamakon kamuwa da coronavirus ko da yake ba a tabbatar da wannan ikirarin nasu ba.

    Masoyan wakokinsa suna kiransa da suna sarkin soukous - wato wani salon kida da ake yi a Congo wanda ya yi tashe a kasashen Afirka.

    'Yarsa, mawakiya da ke Faransa Liza Monet, ta wallafa sako a Twitter ranar Alhamis inda ta ce mahaifinta ya mutu sanadiyar coronavirus. Ta rubuta cewa: "Mutuwarsa ta gigita ni".

    Aurlus Mabele ya mutu yana da shekara 67 a duniya

    Asalin hoton, YOUTUBE

  9. Alkalai za su daina daure mutane a Tanzania saboda coronavirus

    An umarci 'yan kasar Tanzania su rika wanke hannayensu domin kauce wa kamuwa da coronavirus

    Asalin hoton, AFP

    Alkalin alkalan Tanzania ya umarci alkalai a arewa maso yammacin kasar su guji daure masu laifi a gidajen yari ta "kowanne hali" domin hana yaduwar coronavirus.

    Mai shari'a S M Rumanyika ya kuma ba su umarni su bayar da beli ga masu laifin da suka cika sharuda.

    Wannan umarni suna cikin jerin shawarwari takwas da ya bayar a wasikar da ya aike ga kotunan gunduma domin taimakawa wurin hana yaduwar cutar a gidajen yarin kasar.

    Sauran shawarwarin da ya bayar sun hada da takaita wa mutane zuwa kotu inda ya ce daga yanzu za a bar lauyoyi da mutanen da suke karewa ne kawai su shiga kotuna.

    “Za ku ga cewa wadannan jerin shawarwari sun ci karo da yadda aka saba da ma doka. Amma ya kamata a sani kiwon lafiyarmu da ta sauran mutane yana da matukar muhimmanci,” a cewar mai shari'a Rumanyika.

    A halin da ake ciki, mutum biyar ne suka kamu da Covid-19 a Tanzania.

    Hukumomin kasar sun dauki matakai daban-daban na dakile cutar tun da aka samu bullarta ranar Litinin.

    An rufe makarantu da jami'i'o tsawon wata daya, sannan aka haramta yin taruka, kana aka hana baki zuwa gidanjen yari ko majalisar dokokin kasar.

  10. Coronavirus: Najeriya ta kara yawan kasashen da ta rufe wa kofa

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Najeriya ta kara yawan kasashe biyu da ta hana 'yan kasashensu shiga kasar a yunkurinta na kauce wa yadauwar cutar numfashi ta coronavirus.

    Kasashen da aka kara din su ne Sweden da Austria, a cewar Ministan Lafiya Osagie Ehanire a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Juma'a kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

    A ranar Laraba ne Najeriya ta haramta wa wadanda suka fito daga kasashe 13 da cutar coronavirus ta fi yi wa katutu shiga kasar, ciki har da Amurka da Birtaniya da China.

    Sauran kasashen da ke cikin jerin su ne Italiya, Iran, Koriya ta Kudu, Spain, Japan, Faransa, Jamus, Norway, The Netherlands da kuma Switzerland.

  11. Za a gudanar da zaben raba gardama a Guinea duk da coronavirus

    Guinea

    Asalin hoton, AFP

    Duk da kiraye-kirayen da Hukumar lafiya ta Duniya ke yi ga kasashen Afrika na su dauki matakan gaggawa don shirya wa coronavirus, hukumomi a Guinea sun ce za su gudanar da zaben raba gardama ranar Lahadi kamar yadda suka shirya.

    An kwashe watanni ana zanga-zangar nuna adawa da zaben raba gardamar kan kundin tsarin mulki, wanda idan aka amince da shi, zai bai wa shugaban kasar Alpha Conde mai shekaru 82 ya nemi wa'adi na uku a mulki.

    Sama da mutum 30 ne suka mutu lokacin boren.

    Babbar hukumar sadarwar kasar ta ce za a soke layukan intanet da waya a karshen wannan makon.

  12. Za a fara zagaye da wutar aci-bal bal ta Olympics

    Olympics Torch

    Asalin hoton, Getty Images

    Japan ta yi maraba da zuwan wutar aci-bal bal din wasnnin Olympic, inda gwamnati ta jaddada cewa har yanzu tana shirye-shiryen daukar nauyin wasannin duk kuwa da yaduwar coronavirus.

    Ana shirin daukar wutar a fara zagaye da ita daga makon gobe daga tsaunin Fuji zuwa Hiroshima, kafin bude wasannin a birnin Tokoyo cikin watan Yuli.

    A na kara matsawa gwamnatin Japan lamba kan ta dage wasannin a lokacin da coronavirus ke ci gaba da yaduwa.

  13. 'Yan bindiga sun kashe sojoji 29 a Mali

    Mayakan da ke ikirarin kishin Musulunci sun kai hari kan sansanin soji da ke arewacin Mali inda suka kashe sojoji 29 sannan suka jikkata soji biyar, a cewar hukumomi ranar Alhamis.

    Wannan shi ne hari na baya bayan nan da mayakan da ake alakantawa da kungiyar al-Qaeda da ISIS ke kai wa sansanin sojin.

    Mali ce kaar da suka fi karfi a yankin Saleh kuma daga can suke kai hare-hare cikin kasashe makabta kamar Jamhuryar Nijar da Burkina Faso.

    Harin wani gagarumin koma-baya ne ga sojojin Mali.

    Jami'ai sun ce an kashe sojojin ne lokacin da mayakan suka kai hari a sansaninsu da ke Tarkint wanda ke arewacin Gao.

    Tun da fari, rundunar sojin ta ce dakarunta biyu kawai mayakan suka kashe.

    Irin wadannan hare-hare na karuwa a kasar ta Mali lamarin da ya harzuka 'yan kasar.

    Irin wadannan hare-hare na karuwa a kasar ta Mali lamarin da ya harzuka 'yan kasar.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Irin wadannan hare-hare na karuwa a kasar ta Mali lamarin da ya harzuka 'yan kasar.
  14. Su waye karin mutum biyar da ke dauke da Coronavirus a Ghana?

    Ghana ta sake samun mutane biyar masu dauke da covid-19. Wata sanarwar Hukamr Lafiya ta Ghana ta ba da bayani a kan mutanen haka:

    • Mace mai shekaru 29, mazauniyar birnin Accra kuma ba ta je wata kasa da ke fama da annobar ba kwanan nan.
    • Mace mai shekaru 34, mazauniyar birnin Accra: ana tunanin ta dauki cutar ne daga abokin aikinta.
    • Namiji mai shekaru 53, mazaunin Tema kuma bai je wata kasa da ke fama da annobar ba kwanan nan sannan babu shaidar ya yi mu'amala da wani mai cutar ba
    • Namiji mai shekaru 41, ya iso Ghana da jirgin KLM ran 15 ga wannan watan na Maris kuma akwai alamun ya dau ciwon ne daga wasu 'yan uwansa a birnin Amsterdam da kuma wasu fasinjojin jirgin
    • Namiji mai shekaru 36, mazaunin birnin Paris na faransa kuma ba a tabbatar da ranar da ya shiga Ghana ba sannan babu shaidar ya yi mu'amala da wani mai dauke da cutar ba.
    • Yanzu dai yawan mutanen da suka kamu da cutar a Ghana sun kai 16 amma babau wanda ya rasa ransa.

    An tabbatar wadannan mutanen na dauke da cutar ne ta hanyar yi masu gwaji.

    An fara bin sahun mutanen da ake tunanin masu dauke da cutar sun yi mu'amala da su.

  15. Sama da mutum 200 sun kamu da Coronavirus a Afirka ta Kudu

    Coronavirus

    Asalin hoton, AFP

    Afirka ta Kudu ta sanar da cewa mutum 205 ne kawo yanzu suka kamu da cutar coronavirus.

    Yawan mutanen ya yi tashin gwauron zabi daga mutum 55 a jiya Alhamis

    Ministan Lafiya Zweli Mkhize ya ce yana sa rai yawan mutanen zai karu kuma ya yi kiyasin cewa a kalla kashi 60 cikin 100 na mutanen kasar miliyan 56 za su iya kamuwa da cutar ta covid-19.

    Ministan ya ce ciwon zai tagayyara a kalla kashi 20 cikin 100 na mutanen.

    A farkon makon nan na Shugaba Cyril Ramaphosa ya ayyana dokar ta baci kan annobar inda ya hana zirga-zirga ya kuma ba da umarnin rufe makarantu ya kuma haramta taron mutane.

  16. Coronavirus: El-Rufai ya ba da umarnin dakatar da Sallar Juma'a

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta bi sahun wasu kasashen Musulmi ciki har da Saudiyya wajen dakatar da sallar Juma'a da sauran tarukan addini domin kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

    Wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun Gwamna Nasir El-Rufai ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Juma'a ta kuma bukaci malaman addinin Kirista su dakatar da gudanar da ibada a coci ranar Lahadi.

    Kazalika gwamnatin ta bai wa manyan makarantun jihar, irin su KASU, Nuhu Bamalli Polytechnic, College of Education da Nursing and Midwifery su rufe zuwa kwana 30.

    "A kasashen da Musulmi suka fi rinjaye irin su Saudiyya, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa, an bai wa mutane umarni su yi sallah a gidajensu kada su je masallatai saboda halin da muke ciki. Don haka gwamnatin Kaduna ta bayar da umarni a dakatar da dukkan sallolin hamsas salawati a cikin masallatai har sai an shawo kan coronavirus", in ji sanarwar.

    Ta kara da cewa "ya kamata mu yi koyi da kasashen da Kiristoci suke da yawa irin su Italiya da Faransa da Jamus domin dakatar da ibadu a coci. Muna sa ran fasto-fasto da mabiyansu su bi umarnin masana kiwon lafiya su guji taruwa a coci."

    Gwamna Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, Twitter @GovKaduna

    Bayanan hoto, Gwamna Nasir El-Rufai ya ba da umarnin rufe manyan makarantun jihar
  17. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutanen da suka mutu a Sufaniya sun zarta 1,000

    Mutanen da suka mutu a Spain sakamakon kamuwa da coronavirus sun kai 1,000 1,002, a cewar hukumomi.

    Kusan mutum 20,000 suka harbu da cutar yayin da mutum 1,588 suka ji sauki.

  18. Coronavirus: An bukaci ma'aikatan lafiyar da suka yi ritaya su dawo bakin aiki

    coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    An fara aika wa likotoci da malaman jinya 65,000 da suka yi ritaya wasiku, ana bukatar su dawo bakin aiki don taimakawa wajen dakile annobar coronavirus a Ingila da Wales a Burtaniya.

    Manyan jami'an gwmanati sun ce ana bukatar ma'aikatan lafiya da suka bar aiki su dawo su taimakawa wadanda ke aiki yanzu.

    Wannan na zuwa ne bayan da gwamnati ta sha alwashin tabbatar da samar da kayan aiki a duka asibitoci.

    A Scotland kuwa, an nemi duka wadanda suka bar aikin lafiya a shekaru ukun da suka gabata da su duba yiwuwar dawowa aiki.

    Kamfanoni da dama na gargadin cewa akwai yiwuwar za su durkushe, kuma hakan zai yi sanadiyyar rasa ayyuka yayin da aka dakatar da ayyuka a mafi yawan bangarori a Burtaniya.

    A Burtaniya, mutum 144 cutar covid-19 ta kashe kuma mutum 3, 269 suke dauke da ita kawo yanzu.

  19. 'Fiye da mutum miliyan 20 za su kamu da coronavirus'

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Filin jirgin sama na McCarran a Amurka babu kowa acikinsa

    Gwamna jihar California ta Amurka, Gavin Newsom ya shaida wa 'yan jihar cewa kada su bar gidajensu sai idan akwai wani muhimmin abu da za su yi.

    Ya yi kiyasin cewa sama da rabin mutum miliyan 40 da ke jihar za su kamu da cutar covid-19 a cikin watan biyu.

    Gwamnan ya umarci duka mazauna jihar su zauna a gida don hana yaduwar coronavirus a jihar mafi yawan mutane a Amurka.

    Cutar ta kashe mutum 205 da ke zaune a Amurka kuma ta kama sama da mutum 14,000.

    A fadin duniya kuwa mutum 250, 000 ne suka kamu da cutar ta numfashi kuma sama da mutum 10,000 sun mutu.

  20. Karin bayani kan coronavirus

    Coronavirus
    Coronavirus
    Coronavirus