Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Tanzania za ta rufe makarantu saboda coronavirus

    Hukumomi a Tanzania sun sanar da cewa za su rufe dukkan makarantun kasar a wani mataki na hana yaduwar cutar coronavirus.

    Za a rufe makarantun ne ranar Laraba tsawon kwana 30, a cewar Firai Minista Kassim Majaliwa.

    Ya kara da cewa an dakatar da dukkan tarukan jama'a, ciki har da wasannin kwallo.

    An dauki matakin ne bayan an gano cewa wani dan kasar mai shekara 46, wanda ya koma Tanzania daga Belgium, yana dauke da cutar Covid-19.

    An gano mutane da dama da suka yi mu'amala da shi kuma an killace su, in ji Mr Majaliwa.

    A cewarsa, ana neman sauran mutanen da suka yi mu'amala da mutumin.

    Mr Majaliwa. ya ce a shirye Tanzania take ta tunkari Covid-19 idan ta ci gaba da yaduwa a kasar.

    Mr Majaliwa. ya ce a shirye Tanzania take ta tunkari Covid-19 idan ta ci gaba da yaduwa a kasar.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mr Majaliwa. ya ce a shirye Tanzania take ta tunkari Covid-19 idan ta ci gaba da yaduwa a kasar.
  2. Coronavirus: Sadio Mane ya bai wa Senegal tallafin £41,000

    Dan wasan Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane ya bayar da gudunmawar £41,000 ga kwamitin da kasarsa ta nada domin yaki da cutar coronavirus.

    Dan wasan ya dauki matakin ne bayan da ya lura da yadda cutar ke yaduwa a kasar ta Senegal.

    A wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mane ya yi kira a dauki batun yaduwar cutar ta coronavirus da "matukar muhimmanci."

    Dan wasan ya bai wa magoya bayansa shawara kan matakan da za su dauka domi kare kansu daga kamuwa da cutar, kamar "wanke hannu tsawon dakika 30".

    Kawo yanzu, an tabbatar da mutum 27 da suka kamu da Covid-19 a Senegal, ko da yake biyu dsaga cikin su sun warke, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar.

    Mane ya bai wa magoya bayansa shawara kan matakan da za su dauka domi kare kansu daga kamuwa da cutar

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mane ya bai wa magoya bayansa shawara kan matakan da za su dauka domi kare kansu daga kamuwa da cutar
  3. Coronavirus: Likitocin Abuja sun soma yajin aiki

    Kungiyar likitocin Najeriya reshen Abuja babban birnin kasar ta soma yajin aiki duk da yake an samu bullar cutar Corbid-19 a kasar.

    Sanarwar da shugaban kungiyar likitocin, Roland Aigbovo, ta ce dukkan likitocin da ke aiki a gudunma 14 na Abuja da manyan asibitoci da cibiyoyin lafiya sun soma yajin aiki ranar 16 ga watan Maris domin tursasa wa gwamnatin birnin ta biya su albashi.

    "Mambobinmu sun fada matsanancin halin rashin kudi saboda rashin biyan su albashi kamar yadda ya kamata kuma mun jira har karshen 2019 da kuma sabuwar shekarar 2020, har zuwa makonni uku na watan Fabrairu domin a biya mu albashin watan Janairu wanda bai taka kara ya karya ba," in ji sanarwar.

    Mr Aigbovo ya ce matain da suka dauka na da wahala amma babu yadda za su yi idan basu dauke shi ba.

    Mr Aigbovo ya ce rashin biyan su albashin ne ya sa suka dauki wannan mataki

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mr Aigbovo ya ce rashin biyan su albashin ne ya sa suka dauki wannan mataki.
  4. An dakatar da wanda ya kamu da coronavirus a Liberia daga aiki

    Shugaban Liberia George Weah ya dakatar a jami'in gwamnatin kasar da ya kamu da cutar Covid-19 bayan ya koma kasar daga Switzerland, inda ya zama mutum na farko da ya harbu da cutar a Liberia.

    Mr Weah ya ce Nathaniel Blama, shugaban hukumar kare muhalli ta kasar, ya ki yarda a killace shi kamar yadda jami'an lafiya suka nemi ya yi domin gudun baza coronavirus.

    Amma Mr Blama ya musanta zargin, yana mai cewa ya bi dukkan ka'idojin da jami'an lafiya suka gindaya masa inda ya koka kan yadda jami'an "suke yada labaran karya".

    A gefe guda, Shugaba Weah ya dakatar da bude makarantu, ciki har da jami'o'i tsawon mako daya daga ranar 17 ga watan Maris, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar watsa labaran kasar ta fitar.

    Matakin zai bai wa jami'an lafiya damar sanya ido da kuma gano mutanen da suka shiga kasar a jirgi daya da Mr Blama.

      Mr Blama ya zargi jami'an lafiya da  yada labaran karya

      Asalin hoton, EPA

      Bayanan hoto, Mr Blama ya zargi jami'an lafiya da yada labaran karya
    • Trump ya fusata China kan kiran coronavirus 'yar kasarta

      Kasar China ta fusata bayan shugaban Amurka Donald Trump ya kira cutar coronavirus "'yar China".

      Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China ya gargadi Amurka a kan ta je ta ji da marsalolin da ke gabanta kafin ta tsangwami China.

      An dai fara samun bullar cutar coronavirus ne a birnin Wuhan na China a karshen shekarar 2019.

      A makon da ya gabata ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Chinan ya yada wani batu inda ake zargin dakarun Amurka da da kai cutar yankin.

      Wannan zargi ne ya sa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci China da ta daina yada abin da bata da tabbas a kansa.

      Ya zuwa yanzu dai an samu mutum fiye da dubu dari da saba'in da suka kamu da cutar a fadin duniya inda mutum fiye da dubu tamanin suke a China.

      A ranar Talata ne aka samu mutum guda da ya kamu da cutar a Beijing.

      Trump

      Asalin hoton, Getty Images

    • Matakan da Babban Bankin Najeriya ya dauka kan coronavirus

      Babban Bankin Najeriya ya sanar da wasu jerin matakai da ya dauka bayan bullar annobar coornavirus.

      Matakan sun hada da

      • Bai wa masu kanana da matsakaitan sana'o'i dala miliyan 135 da suka hada da otel-otel da kamfanonin jiragen sama da kamfanonin sarrafa magunguna.
      • Bayar da bashi ga kamfanonin hada magunguna da suke da niyyar fadada ko bude kamfanoninsu a Najeriya, da kuma masu niyyar bude asibitoci.
      • Sannan da rage kudin ruwa kan basussukan da ke da alaka da shi daga kashi 9 cikin 100 zuwa kashi 5 cikin 100
      • Da dakatarwar wucin-gadi kan biyan bankin basussukan da yake bi.
      cbn

      Asalin hoton, Getty Images

    • Kanun labaran yau kan coronavirus

      Da farko dai ana gwajin wani maganin da ake sa ran zai magance coronavirus a Amurka.

      An yi wa wasu da suka ba da kansu don yin gwaji allurar gwaji. Amma zai dauki lokaci kafin a gane ko za ta yi aiki.

      A Turai kuwa Faransa za ta rufe kan iyakokinta na tudu daga tsakar ranar Talata, kasar dai ta kasance ba shiga ba fita.

      Can a Birtaniya kuwa mutanen da shekarunsu suka wuce 70 ne da mata masu ciki aka umarta su zauna a gida har tsawon wata uku.

      Can a Iran kuma daya daga cikin wuraren da cutar ta fi Kamari – fursunoni dubu 85,000 aka yi wa sakin wucin-gadi a wani mataki na dakie yaduwar cutar.

      Indiya kuma ta rufe shahararren wajen nan ne na yawon bude ido Taj Mahal, yayin da ita kuma Malaysia ta hana 'yan kasarta fita kasashen waje.

      Shawarar WHO

      Shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya ta yau dai ita ce, ku rufe fuskokinku idan za ku duba mai fama da Coronvirus ko kuma in kuna da alamun cutar kawai.

      coronavirus a yau

      Asalin hoton, Getty Images

    • Sanatoci sun bukaci gwamnati ta dakatar da masu shiga Najeriya da ba 'yan kasar ba

      Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta duba yiwuwar hana baki masu shiga da ba 'yan kasar ba, musamman daga kasashen da aka fi fama da coronavirus.

      Sanatocin sun yi wannan kira ne bayan zamansu na ranar Talata inda shugaban kwamitin lafiya na majalisar Ibrahim Oloriegbe, ya gabatar da bukatar.

      A ranar Talata ne kasar ta tabbatar da mutum na uku da ya kamu da cutar - kuma dukkan mutanen sun shigo ne daga Italiya da Birtaniya, inda cutar ke tasiri sosai a can.

      Kafin sanar da mutum ta uku mai dauke da cutar dai, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta hana shiga kasar ba.

      Kafar yada labaran The Cable ta ruwaito Sanata Oloriegbe na cewa bayan sanya haramcin shiga kasar, akwai bukatar a dauke wasu matakan daban na hana yaduwar cutar.

      ''Idan zai yiwu a hana mutane tafiya kasashen da cutar ta fi kamari musamman Turai inda kasashe da yawa suka kamu, har sai idan tafiyar ta kasance mai matukar muhimmanci.

    • Yawan masu coronavirus ya kai 400 a Afirka

      Yawan masu coronavirus ya kai 400 a fadin Afirka

      A yanzu haka akwai mutum 400 da ke dauke da coronavirus a fadin nahiyar, inda kasashe ke ta sanya matakan hana yaduwar cutar.

      Bayana baya-bayan nan na nuna kasashen da mutanen da suka kamau da cutar kamar haka:

      • Aljeriya- 60
      • Benin- 1
      • Burkina Faso- 15
      • Kamaru- 5
      • Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka- 1
      • Congo-Brazzaville- 1
      • Jamhuriyyar Dimkoradiyyra Congo- 2
      • Masar- 126
      • Eswatini- 1
      • Habasha- 5
      • Equatorial Guinea- 1
      • Gabon- 1
      • Ghana- 6
      • Guinea- 1
      • Ivory Coast- 3
      • Kenya- 3
      • Laberiya- 2
      • Mauritania- 1
      • Moroko- 37
      • Namibiya- 2
      • Najeriya- 3
      • Rwanda- 7
      • Senegal- 26
      • Seychelles- 4
      • Somaliya- 1
      • Afirka Ta Kudu- 62
      • Sudan- 1
      • Tanzaniya- 1
      • Togo- 1
      • Tunusiya- 24

      A yayin da kasashe da dama ke rufe makarantu da hana gudanar da manyan taruka da rufe kan iyakoki, a Kenya kuwa kamfanonin sadarwa sun rage farashin aikawa da kudi ta waya don karfafa wa mutane gwiwar rashin rike kudi a hannunsu.

    • Ga wasu shawarwari da matakai na yadda za su kare kanku daga coronavirus

      Ga shawara ga mutanen da suke tunanin sun kamu da coronavirus
      Bayanan hoto, Ga shawara ga mutanen da suke tunanin sun kamu da coronavirus
      Ga alamomin coronavirus
      Bayanan hoto, Ga alamomin coronavirus
      Abin da kuke bukatar yi
      Bayanan hoto, Abin da kuke bukatar yi
      matakan coronavirus
      Dalar Gyada
    • Buhari ya dakatar da bikin wasanni na Najeriya na 2020 saboda coronavirus

      Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage bikin wasanni na kasar na shekarar 2020 a matsayin matakin hana yaduwar coronavirus.

      Shugaban ya dauki matakin ne bayan da minitsan lafiya da na wasanni sun gana da shi a fadarsa da ke Abuja ranar Talata da safe.

      Hakan na zuwa ne bayan da aka gano mutum na uku da ke dauke da cutar a kasar, wata mace da ta shigo daga Birtaniya ranar Juma'ar da ta gabata.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Coronvirus: 'Yan Iran na kutsawa wajen ibadar mabiya shi'a duk da hanin da aka yi

      Wasu 'yan kasar Iran na kutsawa da karfi don shiga wajen ibada na Fatima da ke Qom, bayan da aka rufe shi na wucin-gadi saboda annobar coronavirus.

      Wani dan majalisa Ali Motahhori ya yi kira da aka gurfanar da su gaban shari'a, yana mai cewa baya ga barazanar lafiya da hakan ke jawowa, suna kuma bata Musulunci.

      Sai dai kwararru sun bayyana damuwa tun farkon barkewar annobar kan matakin rufe wajen da aka dauka, inda miliyoyin mutane ke zuwa don ibada duk shekara.

      Babban mai kula da wajen ibadar Ayatollah Mohammed Saeedi, tun a lokacin ya ce ya kamata a bar wajen a bude saboda ''waje ne na samun waraka'' kuma ''ya kamata a karfafa wa mutane gwiwar zuwa wajen.''

      Mace-mace a Iran sakamakon coronavirus sun kai 853, sannan wadanda suka kamu da cutar sun kai 14,991, inda ta zamo ta uku bayan China da Italiya.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Saudiyya

      An samu karin mutum 15 masu dauke da coronavirus a Saudiyya, inda yawan mutanen da ke dauke cutar suka kai 133 yanzu haka a kasar.

      Kamfanin dillancin labaran kasar ne ya ruwaito ma'aikatar lafiya na fadar hakan a ranar Litinin da yamma.

      Sai dai tuni aka samu mutum shida da suka warke daga cikin wadanda suka kamu a baya, yayin da sauran masu dauke da cutar ke killace a cibiyoyin lafiya daban-daban a fadin kasar.Majiyoyin yada labarai sun ambato minsitan lafiyar kasar Tawfiq Al-Rabiah yana hasashen cewa za a samu karuwar masu dauke da coronavirus nan gaba a kasar.

      Minsitan lafiyar Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah

      Asalin hoton, SPA

      Bayanan hoto, Minsitan lafiyar kasar Tawfiq Al-Rabiah ya yi hasashen cewa za a samu karuwar masu dauke da coronavirus nan gaba
    • Ana ci gaba da binciken maganin coronavirus

      Ana ci gaba da binciken maganin warkar da annobar coronavirus.

      Wasu Kamfanonin samar da magunguna na Sanofi da Regeneron na gudanar da gwaji kan kwayar maganin Kevzara ga mutum sama da 400 da ke fama da cutar inda aka fara gwajin a New york.

      Masu bincike a Spain kuma na amfani da wani maganin na daban, wanda aka taba amfani da shi wajen warakar da cutar HIV kan mutum 200, da nufin rage lokacin da suke dauke da cutar.

      Akwai kuma maganin zazzabin maleriya na chloroquine da ake amfani da shi ga wasu mutum 3,000 da ke fama da coronavirus, wanda ake fatan zai hana wa cutar hayayyafa.

    • Mutum biyu sun warke daga coronavirus a Kamaru

      Mutum biyu na farko da suka fara kamuwa da Coronavirus sun warke, a war daraktan kula da cututtuka masu yaduwa a ma'aikatar kiwon lafiya ta Kamaru.

      Sai dai kuma ya ce za su ci gaba da zama a asibiti har zuwa wani lokaci.

      Daraktan ya ce mutum na uku da ya kamu da cutar na fuskantar 'yan wasu matsaloli saboda yawan shekarunsa.

      Ragowar mutum biyu kuma suna ci gaba da samun kula a asibiti.

      A yanzu haka hukumomin sun dada karfafa aikin cibiyar bincike da ake kira "Centre Pasteur" domin a samu sakamakon gwajin coronavirus a cikin sa'a hudu.

    • Labarai da dumi-dumi, An samu wata mace mai dauke da coronavirus a Najeriya, Ta zamo ta kuku da aka gano da cutar a kasar

      An samu wata mace dauke da coronavirus a Najeriya, wadda ta zama ta uku da aka samu da cutar a kasar.

      Mai bai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

      Matar mai shekara 30 ta dawo ne daga Birtaniya ranar 13 ga watan Maris - wadda bayan isowarta sai ta killace kanta, inda ta dinga ganin alamun cutar.

      An yi mata gwaji aka kuma tabbatar ta kamu da Covid-19, inda a halin yanzu take wata cibiyar lafiya a Legas.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Ivory Coast ta hana 'yan Amurka da Faransa shiga kasarta

      coronavirus ivory coast

      Asalin hoton, AFP

      Bayanan hoto, Dakatarwar ta shafi kasashen da suke da masu dauke da cutar fiye da 100 ne kawai

      Ivory Coast ta bi sahun kasashen Afirkar da suka dakatar da shigar baki 'yan kasashen waje daga wuraren da coronavirus ta fi tsanani.

      A wata sanarwa da hukumomi suka fitar ranar Litinin, sun ce dakatarwar ta shafi kasashen da suke da masu dauke da cutar fiye da 100 ne kawai, kuma ta wucin-gadi ce.

      Kasashen sun hada da Amurka da Faransa da Birtaniya da kuma yawancin yankin Turai.

      Nan da kwana 15, 'yan asalin kasar ne kawai da masu zama dindindin a cikinta za a bari su shiga daga wata kasar, su din ma sai an killace su na tsawon mako biyu a lokacin da suka shiga kasar.

      Hukumar tsaro ta kasar da Shugaba Alassane Ouattara ke jagoranta, ta kuma bayar da umarnin rufe makarantu da jami'o'i daga yau Talata har tsawon kwana 30.

      Sannan za a rufe mashaya da wuraren shakatawa daga tsakar daren Laraba, har tsawon kwana 15, amma akwai yiwuwar sake duba matakin.

      An kuma hana duk wani taro da ya wuce na mutum 50, kamar wasanni da tarukan al'adu, daga tsakar daren Laraba har tsawon kwana 15.

      Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce an samu masu dauke da cutar uku a Ivory Coast, sai dai babu mutuwa zuwa yanzu.

    • Likitoci na zabar wanda zai rayu da wanda zai mutu saboda corona

      coronavirus italy

      Asalin hoton, Getty Images

      Likitocin da ke gaba-gaba wajen yaki da coronavirus a Italiya sun ce suna fuskantar wani mummunann hali na zabar wanda zai rayu ta hanyar yi musu magani da wanda za su kyale ya mutu ga masu fama da cutar.

      A yayin da ake samun karuwar daruruwan masu dauke da cutar a kowace rana, Italiya na ta kokarin samar da isassun gadajen asibiti da za sau duba marasa lafiya.

      Shugaban sashen kulawa ta musamman a asibitin Bergamo da ke yankin arewacin Lambordia, Dr Christian Salaroli, ya shaida wa jaridar Corriere della Sera cewa: "Idan mutum ya kai tsakanin shekara 80 zuwa 95 kuma yana cikin tsananin yanayi na cutar, to watakila ba za ka iya ci gaba da ba shi kulawa ba.

      "Akwai kalamai masu matukar tayar da hankali, amma kuma a zahiri su ne gaskiyar magana. Ba za mu iya yin abin da za ku kira mu'ujiza ba".

      Coronavirus ta yi muni sosai a Italiya - an samu mace-mace har 1,000 daga cikin mutum 15,000 masu dauke da cutar a ranar Juma'ar da ta gabata, wato 12 ga watan Mairs 2020, kusan kashi uku na yawan mace-macen da aka samu a China.

    • Babban limamin Ghana ya bukaci Musulmai su bi umarnin daina zuwa masallaci kan coronavirus

      Ofishin limamin-limamai na kasar Ghana Dr Osman Nuhu Sharubutu, ya bukaci al'ummar musulman kasar da su bi umarnin shugaba Nana AKufo Adoo wanda ya umurci dakatar duk wani taron jama'a da suka hada da haduwa a masallatai da coci-coci da zaman makoki da jana'iza da aure da da duk wani taron da ke hada jama'a har zuwa mako hudu don dakile yaduwar coronavirus.

      Ghana dai na cikin kasashen Afirka da cutar coronavirus ta bulla.

      Shiekh Armaya'u Shu'aib shi ne kakakin ofishin babban limamin na kasar Ghana, ga kuma karin bayanin da ya yi.

      Bayanan sautiHira da Shiekh Armaya'u Shu'aib na Ghana kan coronavirus
    • Eu za ta hada kudi don yakar rushewar tattalin arzikin da coronavirus za ta haifar

      Tutocin EU

      Asalin hoton, Getty Images

      Ministocin kudi na Tarayyar Turai sun yi alkawarin hada karfi domin yakar tabarbarewar tattalin arziki da annobar coronavirus za ta haifar.

      Kowace kasa ce za ta yanke shawara kan irin matakan da za ta dauka a kasarta, amma hukumar Tarrayyar Turai ta ce sama da dala biliyan 130 aka yi alkawarin samarwa kawo yanzu.

      Tuni gwamnatin Birtaniya ta yi alkawarin dala biliyan 15 a matsayin tallafi don bunkasa kasuwanci.