Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Za a sallami wanda ya kawo Coronavirus Najeriya daga asibiti

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Jihar Legas za ta sallami dan kasar Italiyan nan da ya shigo da cutar coronavirus Najeriya bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa yanzu ba ya dauke da cutar.

    Kwamishinan lafiya na Legas, Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron manema labarai, inda ya ce maras lafiyar da aka bai wa kulawa a asibitin Yaba da ke Legas ya warke.

    Da yake bayyana labarin a matsayin ci gaba ga Najeriya, Abayomi ya ce ba za a sallame shi ba tukunna har sai an sake yin wani gwajin cikin awa 48 domin tabbatarwa.

    Ya kara da cewa idan aka sake ganin ba ya dauke da cutar a karo na biyu sai a sallame shi.

  2. Labarai da dumi-dumi, 'Yar gidan Buhari ta killace kanta saboda Coronavirus

    'Yar gidan shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ta killace kanta sakamakon fargabar kamuwa da cutar coronavirus.

    Hakan ya faru ne bayan ta koma Najeriya daga Birtaniya.

    Uwar gidan shugaban ce Aisha Buhari ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce 'yar tata ta yi hakan ne saboda shawarar da ma'aikatar lafiya ta bayar cewa duk wanda ya dawo daga kasashen da ake fama da cutar ya killace kansa.

    Sai dai Aisha Buhari ba ta bayyana sunan 'yar tata da ta kamu ba, sannan ta ce har yanzu ba ta nuna wata alamar kamuwa da cutar ba.

    "A yau (Alhamis) 'yata ta dawo daga Birtaniya, wadda take cikin kasashen da ke fama da Covid-19," Aisha ta wallafa.

    Ta kara da cewa: "Bisa shawarar da hukumar lafiya ta bayar da kuma hukumar NCDC, ta killace kanta ba don tana dauke dauke da cutar ba."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Majalisar Dattawan Najeriya ta rufe wa jama'a kofa kan Coronavirus

    Sanata Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Majalisar Dattawan Najeriya ta yanke shawarar rufe kofofinta ga jama'a wadanda ba 'yan majalisa ba a yunkurinta na guje wa yaduwar cutar coronavirus.

    A yau Alhamis ma'aikatar lafiya a Jihar Legas ta bayar da sanarwar karin mutum hudu da suka kamu da cutar ta coronavirus, abin da ya sa adadinsu ya kai 12 jumulla a Najeriya, duk da cewa daya daga ciki ya warke.

    Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ya bayyana matakin ne yayin zamansu na yau, inda ya bayyana matakai biyu na hana mutane shiga harabar majalisar.

    Mataki na farko shi ne na hana dukkanin wani taron jin ra'ayin jama'a kan al'amuran da suka shafi yin doka a kasar.

    Mataki na biyu kuwa ya shafi masu zuwa yawon bude ido ne, wanda ya hada da daliban manyan makarantu da kuma kungiyoyin farar hula.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Labarai da dumi-dumi, Za a dakatar da Premier League har zuwa karshen watan Afrilu

    Za a dakatar da wasannin kwallon kafa a Ingila har zuwa akalla 30 ga watan Afrilu sakamakon ci gaba da yaduwar cutar coronavirus.

    Dukkanin wasannin gasar Premier League da EFL da kwallon mata da wasannin gasar kasar Scotland da ta Wales da ta Northern Ireland an dage su.

    Hukumar FA ta Ingila ta kuma yanke shawarar cewa za a iya ci gaba da buga wasa a kakar bana "har illa masha'allahu".

    Bisa ka'ida, za a kammala kakar bana a ranar 1 ga watan Yuni.

    Wani bayani da hukumomin FA da Premier League da EFL suka fitar sun nuna "kokarinsu na nemo hanyoyin ci gaba da kakar 2019-2020" tare da kammala dukkanin wasannin gida da kuma na Zakarun Turai "da zarar an samu damar yin hakan".

  5. Coronavirus: Mutum 30,000 sun yi taron addu'a a Bangladesh

    Taron addu'a

    Asalin hoton, AFP

    Dubun dubatar mutane sun taru don yin wata addu'a a Bangladesh a ranar Laraba, a yayin da ake tsaka da fargabar cewa hakan zai jawo barkewar cutar.

    Wani jami'in dan sanda a kasar Tota Miah ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Musulmai 10,000 ne suka taru a garin Raipur don yin addu'ar ''neman waraka'' daga Al-Kur'ani.

    Amma wasu ganau sun shaida wa BBC cewa yawan mutanen ya kai 30,000.

    Hakan na zuwa ne a yayin da aka ce wani taron addini ne ya jawo yaduwar cutar da mutum 500.

    Taron, wanda mutum 16,000 suka halarta, ya kuma jawo barkewar cutar a kasashe makwabta kamar su Brunei da Singapore da kuma Cambodia.

    Gwamnatin Malaysia daga baya ta hana duk wani taron jama'a a kasar tare da rufe iyakokinta don hana ci gaba da yaduwar cutar.

    Haka ma za a yi wani taron addinin mai kama da wannan a Indonesia a farkon makon nan, amma a yanzu an soke yin sa.

  6. Coronavirus: Tanzania ta hana kai ziyara gidajen yari

    Hukumar gidajen yari a kasar Tanzania ta haramta kai ziyara gidajen yari har sai baba ta gani a yunkurin kasar na yaki da yaduwar cutar coronavirus a gidajen yarin.

    Hukumar ta ce matakin ya zama tilas ne domin a kare rayukan mazauna gidan da kuma ma'aikata.

    Matakin na baya-bayan nan ya zo ne 'yan awanni bayan hukumar lafiyar kasar ta tabbatar da sabbin mutum biyu da suka kamu da cutar.

    Marasa lafiyar 'yan Tanzania ne 'yan shekara 40 da ke zaune a babban birnin kasar Dar es Salaam.

  7. Labarai da dumi-dumi, Sabbin mutum hudu sun kamu da coronavirus a Najeriya

    Ma'aikatar lafiya ta Jihar Legas ta tabbatar da cewa wasu sabbin mutum hudu sun kamu da coronavirus a jihar.

    Hakan yana nufin yanzu mutum 12 ne suka kamu a Najeriya, duk da cewa guda daya ya warke.

    Kwamishinan lafiya na Legas Akin Abayomi ya bayyana wa 'yan jarida hakan a yau Alhamis.

  8. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Sabbin mutum 800 sun kamu a Faransa

    Faransa ta sanar cewa yanzu mutum 4,499 ne suka kamu da coronavirus a kasar, inda wasu sabbin mutum 800 suka kamu, a cewar hukumomi.

    Mutum 91 ne cutar ta kashe a kasar, kari a kan 79 da suka mutu a ranar Juma'a.

  9. Mutum 30,000 sun taru don yin addu'a a Bangladesh yayin da ake fargababar yaduwar coronavirus

    Amma wasu ganau sun shaida wa BBC cewa yawan mutanen ya kai 30,000.

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Amma wasu ganau sun shaida wa BBC cewa yawan mutanen ya kai 30,000.

    Dubun dubatar mutane sun taru don yin wata addu'a a Bangladesh a ranar Laraba, a yayin da ake tsaka da fargabar cewa hakan zai jawo barkewar cutar.

    Wani jami'in dan sanda a kasar Tota Miah ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Musulmai 10,000 ne suka taru a garin Raipur don yin addu'ar ''neman waraka'' daga Al-Kur'ani.

    Amma wasu ganau sun shaida wa BBC cewa yawan mutanen ya kai 30,000.

    Hakan na zuwa ne a yayin da aka ce wani taron addini ne ya jawo yaduwar cutar da mutum 500.

    Taron, wanda mutum 16,000 suka halarta, ya kuma jawo barkewar cutar a kasashe makwabta kamar su Brunei da Singapore da kuma Cambodia.

    Gwamnatin Malaysia daga baya ta hana duk wani taron jama'a a kasar tare da rufe iyakokinta don hana ci gaba da yaduwar cutar.

    Haka ma za a yi wani taron addinin mai kama da wannan a Indonesia a farkon makon nan, amma a yanzu an soke yin sa.

  10. Coronavirus: Senegal za ta rufe sararin samaniyarta

    Gwamnatin kasar Senegal ta sanar da rufe sararin samaniyarta daga karfe 11:59 na yammacin ranar Jumma'a agogon kasar.

    Abin dai zai shafi jiragen da ke zirga-zirga ne tsakanin kasar da sauran kasashen duniya, amma ban da jiragen da ke zirga-zirga a cikin kasar.

    Sanarwar wadda ministan yawon bude idanu da sufuri na kasar ya sanya hannu, ta ce an dauki matakin ne saboda takaita ci gaba da yaduwar cutar coronavirus a kasar.

    Ya zuwa yanzu dai akwai mutum 36 da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda biyu daga cikinsu sun warke, 34 kuma suna asibiti suna karbar magani.

  11. Coronavirus: Rwanda ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama

    Kasar Rwanda ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga waje da kuma cikin kasar bayan an samu mutum uku da suka sake kamuwa da cutar coronavirus abin da ya kawo adadin wadanda suka kamu a kasar ya kai 11.

    Dakatarwa za ta fara aikine daga daren Jumma'a.

    Wadanda suka sake kamuwa da cutar sun hadar da wata mata 'yar kasar India da ta je kasar a ranar 8 ga watan Maris din nan ta kuma auri wani mutum ne da aka yi mishi gwaji aka tabbatar yana dauke da ita.

    A cikin wani sakon twitter da ya fitar, kamfanin jiragen sama na RwandaAir ya ce zai mayarwa wadanda suka sayi tikitinsa kudadensu.

    RwandaAir

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, RwandaAir
  12. Me yake faruwa a Afirka yau kan coronavirus?

    Zuwa yanzu dai annobar na ta yaduwa a Afirka sannan WHO ta yi gargadi cewa nahiyar ta shirya tunkurar bala'in da zai same ta.

    A ranar Laraba, aka samu mutuwa ta farko a Burkina - inda Rose-Marie Compaore mataimakiyar shugaban kasa a majalisar dokoki wadda dama tana fama da ciwon suga ta mutu.

    Kasashen AFirka da dama sun dauki matakai da suka hada da:

    • Afirka Ta Kudu ta umarci dukkan mashayu su rufe, ko su rage yawan masu shiga zuwa 50, ko su fuskanci barazanar zama a gidan kaso ku kuma biyan tara, sannan ta dakatar da yawon bude udo a cikin jirgin ruwa a gabar tekunta.
    • Kenya kuwa, kasar da aka sani da bin addini kamar sauran kasashen nahiyar, ta dakatar da ayyukan ibada a coci-coci da masallatai, kuma gwamnati ta ce za ta fara samar da man goge hannu kyauta don magance karancinsa da ake yi
    • Uganda da Botswana kuwa sun rufe makarantu
    • Chadi ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama ta kuma rufe iyakokin kan tudu
    • Laberiya, wadda ta tabbatar da mutum daya da ya kamu ta dakatar da bayar da fasfo ga matafiya don hana bulaguro don gudun shiga da cutar kasar
    • Mauritius, ma ta sanar da bullar cutar karon farko a kasar, inda mutum uku suka kamu
  13. Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a masallatanta a Najeriya

    Ansaruddin

    Asalin hoton, Ansaruddin Facebook

    Kungiyar Addinin Musulunci ta Ansar-ud-deen a Najeriya ta dakatar da Sallar Juma'a da manyan taruka a masallatanta a fadin kasar sakamakon annobar coronavirus.

    A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Alhamis ta ce ta dauki wannan mataki ne cike da nauyin zuciya da kuma duba halin da ake ciki na dakatar da sallar Jum'a da kuma duk wani taro da ya wuce na mutum 50.

    Ta ce dakatarwar za ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba har sai abin da hali ya yi.

    Matakin ya zama wajibi ne don hana yaduwar annobar coronavirus kamar yadda Kungiyar Malamai ta Duniya ta riga ta bayar da fatawa a kai, a cewar sanarwar.

    Sannan ta ce kungiyar za ta bi umarni da shawarwarin da gwamnati da bayar amma za a sanar da jama'a duk wani ci gaba da ake samu dangane da matakin.

    ''Mun san cewa jama'a da dama ba lallai su ji dadin wannan labari ba, amma ya kamata su san cewa saboda ceton al'umma aka yi hakan.

    ''Don haka muna shawartar mutane da su ci gaba da yin sallolinsu a gidajensu su dinga bin matakan tsafta da sauran ayyukan ibadah,'' kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Tun bayan da aka samu karin mutum biyar masu dauke da cutar a Najeriya ake ta daukar matakai daban-daban da suka hada da rufe makarantu a wasu jihohin.

  14. Nahiya daya tal da ba a samu bullar coronavirus ba a duniya...

    ... wannan nahiya ita ce Antarctica. Baya ga dumbin tsuntsayen penguins da ke wajen, akwai kuma tawagogin bincike daban-daban a wannan nahiya. Amma har yanzu babu mai dauke da cutar ko alamunta acan.

    Masu bincike 'yan Birtaniya sai da suka shafe kawana 14 a killace kafin ma su tafi yankin da ke kudancin duniya, kuma an dauki matakai da dama ko da wani abu zai taso da zai shafi aike musu da kayayyaki.

    A kan samu masu bincike har kusan 1,000 duk shekara daga kasashe daban-daban da ke zuwa Antarctica.

    Asibiti mafi kusa da yake yankin yana da nisan dubban mil daga kasar Chile

    Antarctica

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Ana musgunawa fararen fata'yan kasashen waje a Habasha kan coronavirus

    fararen fata

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Rahotanni sun ce ana kai wa bakin hari da duwatsu da hana su shiga ababen hawa na haya da tofa musu yawu

    Ofishin jakadancin Amurka a Habasha ya yi gargadi cewa ana kai hari tare da musgunawa fararen fata 'yan kasashen waje a biranen da ke fadin kasar, bayan zargin su da ake da yada cutar Covid-19.

    A wata sanarwa ta tsaro da ya wallafa a shafinsa na intanet, ofishin ya ce yana ''ci gaba da samun rahotannin kan yadda ake nuna wariya da kyama ga 'yan kasashen waje'' tun bayan da aka gano bullar cutar a kasar a makon da ya gabata.

    Ana amfabi da kalamai kamar ''China da ferengi'' (da ake nufin baki 'yan kasashen waje) ana alakanta su da ''corona'', wanda hakan ke nuna cewa al'ummar Habasha na ganin barkewar cutar a kasar na da alaka da 'yan kasashen wajen,'' a cewra sanarwar.

    ''Rahotanni sun ce ana kai wa bakin hari da duwatsu ana hana su hawa ababen hawa na haya, ana tofa musu yawu, ana bin su da gudu idan suna tafiya da kafa, ana zarginsu da cewa su suka yada Covid-19,'' kamar yadda ofishin jakadancin ya kara.

    Tuni dai an samu masu dauke da cutar har shida a Habasha - na farkon wani dan Japan ne da ya je kasar daga Burkinsa Faso.

  16. Kasashen Afirkar da ba su samu bullar coronavirus ba

    A yanzu dai coornavirus ta tashi daga matakin barazana ga Afirka ta zama zahiri, don kuwa tuni aka samu mau dauke da ita a mafi yawan kasashen nahiyar.

    Sai dai akwai wasu kasashen da har yanzu ba ta kai can ba.

    Kasashen sun hada da:

    • Angola
    • Burundi
    • Cape Verde
    • Chadi
    • Camoros
    • Eritrea
    • Guinea-Bissau
    • Lesotho
    • Madagascar
    • Malawi
    • Mali
    • Mozambique
    • Jamhuriyyar Nijar
    • Sao Tome and Principe
    • Saliyo
    • Sudan Ta Kudu
    • Swaziland
    • Uganda
    • Zimbabwe.
  17. WHO ta gargadi Afirka ta shirya wa 'mummunan abin da zai faru'

    coronavirus kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta gargadi kasashen Afirka da su shirya wa mummunan abin da zai faru kan annobar coronavirus.

    A jumulla dai an samu mace-mace 16 a Afirka a kasashen da suka hada da shida a Masar da biyu Moroko da daya a Sudan da kuma daya a Burkina Faso.

    Afirka ce nahiyar da abin bai shafa ba sosai, amma kwararru a fannin lafiya sun yi gargadi cewa tsarin bangaren lafiyar nahiyar na iya munana lamarin.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus yana cewa, ''Ya kamata Afirka ta farka... mun ga yadda cutar ta kai kololuwa a wasu kasashen.''

    Burkina Faso ta sanar da mutuwa ta farko da aka samu a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka a ranar Laraba - inda wata mata mai shekara 62 kuma mai fama da ciwon suga ta rasu.

    Hukumomi sun ce matar ita ce Rose Marie Compaoré, mataimakiyar shugaban kasa a majalisar dokoki.

    A Afirka Ta Kudu kuwa, an samu karin masu dauke da cutar har 116 a ranar Laraba, mafi yawansu kuma mutanen da suka koma kasar daga Turai ne.

    A cikin mutanen akwai 14 da suka kamu a cikin kasar daga wadancan.

  18. Jihar Lagos ta rufe makarantu

    Gwamnatin jihar Legas a kudancin Najeriya ma ta sanar da rufe makarantu na gwamnati da na kudi daga ranar Litinin 23 ga watan Maris, 2020.

    A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, kwamishinan ilimi na jihar Folashade Adefisayo ya ce an yi hakan ne don kokarin dakatar da bazuwar annobar coronavirus.

    Jihar Legas ce inda aka fara samun bullar cutar a Najeriya mako biyu da suka gataba.

    Sanarwar ta ce: ''Hakan ya zama dole don kare 'ya;yanmu da malamansu daga kamuwa da wannan annoba.''

    Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar 'ya'yansu na kauce wa mu'amala cikin taron mutane a yayin da suke gida ba makaranta, da kuma sa ido kan tsaftarsu musamman wajen wanke hannaye akai-akai.

    A yanzu kusan jihohi 10 ne suka rufe makarantu a fadin kasar bayan da aka samu karin mutum biyar da ke dauke da cutar a ranar Laraba.

    Lamarin da ya sa masu dauke da ita a najeriya suka zama takwas.

  19. Maganin HIV ba ya taimaka wa mai dauke da coronavirus

    Wani gwaji da aka yi a China, kasar da annobar coronavirus ta fara bulla ya nuna cewa magungunan kwayar cutar HIV ba sa kara wa mai dauke da coronavirus kwarin jiki ko rage mace-mace ko kuma rage kaifin kwayar cutar a jikin mara lafiyar.

    An dai yi gwajin kan marasa lafiya kusan 200 a wani asibiti da ke Wuhan.

    Wakilin BBC a can ya ce ba lalle ba ne magungunan su yi wata fa'ida a jikin mara lafiyar sai dai ana fatan magungunan za su taka rawa wajen yakar cutar ta coronavirus.

  20. 'Yan Brazil sun juya wa shugaban kasarsu baya kan coronavirus

    Bolsanaro Brazil

    Asalin hoton, Getty Images

    Jama'a a Brazil na nuna bacin ransu kan yadda Shugaba Jair Bolsonaro yake tafiyar da batun cutar coronavirus da ta zamewa duniya annoba a daya daga cikin zanga-zangar adawa da gwamnatinsa mafi girma da aka taba yi.

    An dai fara zanga-zangar lokacin da shugaban ke jawabi ta kafar talabijin jiya Laraba.

    Mutane a fadin kasar sun shafe 'yan mintuna suna fasa tukwane tare da neman shugaban ya yi murabus.

    Wakilin BBC ya ce mutane sun soki shugaban kasar saboda ayyana annobar coronavirus a matsayin wani kirkirarren labari, amma mutane sun fara juya masa baya, bayan da dandazon masu goyon bayansa suka taru a wajen fadarsa kafin ya karbi sakamakon gwajin da aka yi masa kan coronavirus.

    Shugaban ya ce gwajin ya nuna baya dauke da cutar.

    Sama da mutum 500 ne suka kamu da cutar a Brazil ciki har da ministoci biyu. Mutum hudu kuma sun mutu.