Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Budewa, Rahotannin ranar Talata 17 ga watan Maris 2020

    Masu bin mu a wannan shafi assalamu alaikum. Halima Umar Saleh ce take muku fatan kun wayi gari lafiya.

    Yau ma kamar kullum za mu dora daga inda muka tsaya jiya wajen kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da duniya baki daya.

    Rahotannin namu za su fi mayar da hankali ne kan yaki da annobar coronavirus da ake fama da ita a duniyar.

    Kuna iya komawa kasan wannan shafi don karanta abubuwan da suka faru a a jiya Litinin idan har ba ksamu karanta su ba.

  2. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi a wannan gaba ce za mu yi sallama da ku.

    Kuna iya duba kasa don karanta labaran da muka wallafa muku a yau a wannan shafi da suka hada da rahotanni kan cutar coronavirus da sauran rahotanni da suka shafi duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah Ta'ala Ya kai mu za mu bude shafin da misalin 9.30 na safe.

    Ni Halima Umar Saleh nake cewa mu kwana lafiya.

  3. Jarumin fina-finan Hollywood na Amurka Idris Elba ya kamu da coronavirus

    Jarumin fina-finan Hollywood na Amurka Idris Elba ya kamu da cutar Covid-19.

    Shahararren dan wasan fim din ya sanar da hakan ne a shafinsa na sada zumunta, bayan gwajin da aka yi masa.

    "Ku zauna a gida ku nutsu. Zan dinga ba ku bayanai kan halin da nake ciki. Ina murmurewa. Kar ku ta da hankali.''

  4. Annobar coronavirus na iya ci gaba har watan Agusta a Amurka -Trump

    Ga wasu abubuwa da Shugaba Donald Trump ya fada a wani taron manema labarai kan coronavirus a Fadar White House ranar Litinin:

    • Annobar da ta shiga Amurka na iya ci gaba har watan Yuli ko Agusta ko ma fiye da haka, a cewar Trump
    • An shawarci mazauna kasar da su guji zuwa mashaya da gidajen cin abinci da wuraren taron jama'a da kuma dakatar da tafiye-tafiye
    • Mutane su guji zama a taron da ya fi na mutum 10
    • Amma Mr Trump ya ce babu wasu shirye-shirye na killace gabaki daya kasar - yana ba da shawara cewa tuni mazauna Amurka suka killace kawunansu a gidajensu
    • Mai kula da lamurran coronavirus a Fadar White House Dr Deborah Birx ta roki matasa da su guji cudanya da mutane. Ta ce ''su ne wadanda za su taimaka wajen hana yaduwar cutar.''
    • Dr Birx ta kuma yi gargadi kan cudanya ko da mutane suna jin lafiyarsu kalau. ''Mun san cewa akwai mutane da dama da ba sa nuna alamar cuta, kuma suna ci gaba da yada ta.''
    trump

    Asalin hoton, ge

  5. 'Masu coronavirus' sun lakadawa jami'an lafiya duka sun tsere

    Jami'an lafiya a arewacin Afghanitan sun ce gomman mutane da ake tsare da su da zaton cewa suna dauke da cutar Coronavirus sun gudu.

    Jami'an sun ce a kalla marasa lafiya 36 ne suka tsere tare da taimakon 'yan uwansu, bayan sun lakada wa ma'aikatan lafiya da ke tsare da su duka.

    Wakilin BBC ya ce kamar yadda ma'aikatan lafiyar suka tabbatar, wadanda suka gudun sun yi hakan ne bayan sun ci karfin jami'an da ke tsare dasu a yankin na Herat da ke makwabtaka da Iran.

    Shugaban ma'aikatar lafiya na Afghanistan Dr AbdulHakim Tamana ya ce dukan wadanda suka gudun sun dawo ne daga Iran.

    Kuma akwai mutun daya daga ciki da aka tabbatar da yana dauke da cutar ta Coronavirus.

    Daga farkon shekara zuwa yanzu mutun 80,000 ne 'yan kasar suka dawo daga Iran, kuma an tabbatar da cewa mutun 21 na dauke da cutar Covid-19 a Afghanistan kawo yanzu.

  6. Alamomin cutar coronavirus
  7. UAE ta tura jirage biyu da kayan agajin coronavirus zuwa Iran

    Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta tura jirage biyu dankare da safar hannu da takunkumin rufe baki da hanci da kuma suaran kayan aikin lafiya zuwa Iran, don taimaka wa wurin kawar da cutar Coronavirus.

    A yanzu Iran ce kasar da ta fi fuskantar bala'in cutar Covid-19 a duniya, inda mutun 14,000 suka kamu kuma tuni 850 sun mutu.

    Dama Iran ta yi kira ga kasashen da ba sa ga maciji da ka da su bari siyasa ta hana su gudanar da aikin agaji.

    Tun farko dai sauran kasashen Larabawa kamar Saudiyya sun zargi Iran din da baza coronavirus a fadin duniya ta hanyar barin 'yan kasar ta Saudiyya shiga Iran ba tare da an rattaba wa fasfo dinsu hannu ba.

    Sarkin UAE

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Gwamnatoci ba sa abin da ya kamata don dakile coronavirus - WHO

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce gwamnatoci ba sa yin yadda ya kamata wurin ganin an dakile cutar Coronavirus.

    Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ya kamata a fito da wasu hanyoyin gwaji, kuma duk wanda aka tabbatar na dauke da cutar dole ne a killace shi a kuma gano duk wani wanda ya yi hulda da shi.

    Haka ma Dr Tedros ya bukaci da kasashe su kwaikwayi salon kasashe kamar China da Koriya Ta Arewa, inda ya ce sun nuna cewa za a iya cin karfin cutar gama-gari.

    Tedros Adhanom Ghebreyesus

    Asalin hoton, Getty Images

  9. An kama mai wallafa labaran karya kan coronavirus

    'Yan sanda a Kenya sun kama wani mutum mai shekara 23 da ke wallafa labaran karya kan yaduwar coronavirus a kasar.

    An kama Elijah Muthui Kitonyo ne a garin Mwingi da ke gabashin Kenya kan ikirarin da yake yi cewa gwamnati tana bayar da bayanan da ba sahihai na kan mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar a kasar.

    Wani sakon Twitter da aka wallafa a shafin karya da aka yi ta yada wa a shafukan sada zumunta a karshen makon nan, ya yi ikirarin cewa mara lafiyar ya shiga kasar ne daga birnin Rome na Italiya, ba ta Amurka daga Landan ba kamar yadda gwamnatin ta fada.

    Hukumar bincike kan masu aikata miyagun laifuka ta kasar ce ta tabbatar da batun kamun nasa a shafin Twitter.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Wata cuta da ba a san kanta ba tana barna a Habasha

    Abiy Ahmed

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata cuta da ba a san kanta ba ta bulla a yankin Somali da ke gabashin kasar Habasha.

    A 'yan shekarun da suka gabata cutar ta hallaka daruruwan jama'a, wadanda yawancinsu makiyaya ne da ke kiwo a yankin Tafkin Ogaden, inda kamfanonin kasashen waje ke aikin neman mai da gas.

    Wani jami'in yankin ya ce sama da mutum dubu biyu suka mutu sakamakon cutar da ba a san ko mece ce ba.

    Sannan akwai wasu da ba a iya gano adadinsu ba yanzu haka na kwance.

    Juwaira Ali wata ce data shafe watannin tana bincike kan cutar, ta ce alamomin ciwon abin ta da hankali ne.

    ''Jini na fitowa ta hanci, idon mutum na juyewa ya koma launin ruwan dorawa, tsananin zazzabi, yawaita suma da kuma kisa,'' in ji ta.

    Juwaira ta ce watakil cutar na da alaka da ayyukan da ake yi ko gurbatar muhalli da mai ko iskar gas ke haifarwa - ko daya ta ce akwai bukatar masana kimiya su tabbatar da hakan.

    ''Mazaunan yankin sun bayyana cewa akwai kamfanoni d ake gurbata muhalli da wani sinadari kamar hoda idan aka yi ruwa, hodar sai ta hade da ruwan kogi, wanda mutane ke sha -kullum abin da ke wakana kenan.''

    Kamfanonin da ke aiki a yankin sun ki cewa Uffan kan gurbata muhalli da sinadarin ke yi, haka nan ma hukumomin Ethiopia, duk da karuwar da ake samu na mutanen da wannan annoba ke yi wa illa.

    ''Jami'an gwamnati a Addis Ababa sun musanta akwai matsalolin muhalli da ke shafar lafiya.

    ''Akwai ma wani jami'i guda da ya musanta cewa mutane na rayuwa a yankin, kalaman da tabbas ya saba abin da muka sani.''

    Firai Minista Abiy Ahmed ya ce man fetur da iskar gas su ne makomar Ethiopia nan gaba da za su samar da karin ayyukan yi.

    Sai dai kokarin da aka yi a baya na amfani da albarkatun yankin Ogaden ya haifar da rikici - an yi wata zanga-zanga da ta tilastawa Sarki Haile Selassie yin watsi da aiki.

    'Yan tawaye sun jima suna rigima a yankin.

    A shekara ta 2007 sun far wa wani kamfanin matatan man China, inda suka kashe mutum 74.

    Don haka mai yiwuwa wannan cutar ta yi tasiri wajen jinkirta habbaka albarkaun wannan yanki a yanzu.

  11. Buhari ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC a Abuja

    Buhari da APC governors

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Tawagar gwamnonin ta gana da shugaban kasar ne karkashin jagorancin gwamnan Kebbi Abubakar Bagudu
    Buhari da APC governors

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, A ranar Litinin ne gwamnonin suka je Fadar Shugaban Kasar don ganawa da shi
    Buhari da APC governors

    Asalin hoton, State House

    Buhari da APC governors

    Asalin hoton, State House

  12. Coronavirus: Kasashen Afirka sun tsaurara matakai domin rage yaduwar cutar

    Yawancin kasashen Afirka sun sanya matakai a wani yunkuri na rage yaduwar cutar coronavirus.

    Kasar Afirka Ta Kudu ta ayyana dokar ta baci tare da sanar da dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen da cutar ta fi kamari.

    Kenya kuwa ta dakatar da tafiye-tafiye tare da rufe makarantu domin gudun yaduwar cutar.

    Kasashen Liberia da Somaliya da kuma Tanzania sune na baya-bayan nan da aka samu bullar cutar.

    Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce ya zuwa yanzu mutum 350 ne suka kamu da cutar a sassan kasashen Afirka inda mutum bakwai daga cikinsu sun mutu, 42 kuma sun warke tas.

    Yawancin wadanda suka kamu da cutar a Afirka dai sun dawo ne daga kasashen nahiyar Turai ko kuma kasashen yankin arewacin Amurka.

    Cutar coronavirus ta bulla kasashen Afirka 27 ya zuwa yanzu.

    Coronavirus

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Coronavirus
  13. Coronavirus: Za a rufe wuraren wanka da masallatai a Moroko

    Ministan cikin gida na Moroko ya sanar da cewa za a rufe dukkan wuraren wanka na jama'a da aka fi sani da Hammams domin rage yaduwar cutar coronavirus.

    Kazalika ministan ya ce za a rufe wuraren shan shayi da gahawa da wajen cin abinci da sinima da kuma masallatai.

    Ministan ya ce kasuwanni da shaguna da kuma wuraren da ake sayar da abubuwan bukata na yau da kullum ba sa cikin wuraren da za a rufe.

    Ya zuwa yanzu dai akwai mutum 29 da suka kamu da cutar a kasar.

  14. 'Yan kasuwar Nijar sun soma yajin aiki

    'Yan kasuwar Jamhuriyar Nijar sun fara yajin aiki na kwanaki biyu saboda kisan 'yan uwansu da suka zargin jami'an tsaro sun yi.

    'Yan kasuwar sun ce za su nuna rashin jin dadinsu kan abin da ya faru a kasuwar Tagabati dake Yamai inda wasu 'yan kasuwa uku da mace daya da ta je sayen kaya suka mutu sanadiyar tashin gobarar da suka yi zargin hayaki mai sa hawayen da aka harba ne ya haddasa.

    Tuni gwamnati ta tabbatar da faruwar lamarin tana cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu.

    Kazalika gwamnatin kasar ta dora alhakin faruwar lamarin kan kungiyar farar hula da ta fito taron da gwamnati ta haramta musu, domin nuna kin amincewa da aniyar gwamnatin ta ci gaba da rufe wadanda suka yi badakalar kudin ma'aikatar tsaron kasar.

    Tuni gwamnati ta tabbatar da faruwar lamarin tana cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tuni gwamnati ta tabbatar da faruwar lamarin tana cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu.
  15. An dakatar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano

    Majalisar dokokin jihar Kano da ke Najeriya ta dakatar da 'ya'yanta biyar zuwa wata shida bayan an zarge su keta dokokin majalisar.

    Shugaban majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da dakatar da Garba Ya'u Gwarmai da Labaran Audu Madari da Isyaku Ali Danja da Bello Muhammad da kuma Salisu Ahmad Gwangwazo

    Ya ce sun dauki matakin ne saboda yunkurin da 'yan majalisar suka yi na dauke sandar majalisar a makon jiya.

    'Yan majalisar dai sun yi yunkurin dauke sandar ne saboda zargin da suka yi cewa gwamnatin Abdullahi Ganduje ta hada baki da wasu 'yan majalisar domin yin amfani da majalisar wurin sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II.

    BBC ta yi yunkurin jin ta bakin dukkan bangarorin amma bata yi nasara ba.

    An dakatar da 'yan majalisar ne tsawon wata shida

    Asalin hoton, Facebook/ Kano state assembly

    Bayanan hoto, An dakatar da 'yan majalisar ne tsawon wata shida
  16. Coronavirus: An dakatar da kwallon kafa a Ghana

    An dakatar da dukkan harkokin kwallon kafa a Ghana saboda barkewar coronavirus.

    Hukumar kwallon kafar Ghana ta dauki matakin ne ranar Lahadi da almuru bayan shugaban kasar Nana Akufo-Addo, ya bayar da umarnin dakatar da dukkan tarukan jama'a, ciki har da wasanni.

    "Sakamakon umarnin da shugaban kasar ya bayar, hukumar kwallon kafar Ghana ta dakatar da dukkan gasar kwallon kafa da ake yi nan take,"a cewar sanarwar da ta fitar.

    Hukumar kwallon kafar ta Ghana na fatan za a ci gaba da buga tamaula, yayin da suke bin umarnin hukumomin lafiya, tana mai cewa amma umarnin gwamnati ya zarta na hukumomin lafiya.

    Ghana ta bi sahun kasshe da dama da suka dakatar da harkokin kwallon kafa sakamakon fargabar cutar coronavirus.

    An dauki matakin ne bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An dauki matakin ne bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar
  17. An samu bullar coronavirus a Somaliya da Tanzania

    An samu mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a Somalia.

    Ministan lafiya na kasar, Fowsiya Abukar, ya ce mutumin da ya kamu da cutar dan kasar ne da ya dawo daga daga kasar waje a kwanan nan.

    Tuni dai mahukuntan kasar suka sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen waje nan da makonni biyu.

    A wani labarin kuma, Tanzania ta sanar da cewa an samu wata mata da ta kamu da cutar a karon farko a kasar.

    Matar dai ta yi tafiya ne daga Belgium inda ta bi ta filin jirgin saman Kilimanjaro sannan suka tsaya a Sweden da Denmark sannan ta karaso Tanzania.

    Ministar lafiya ta kasar, Ummy Mwalimu, ta ce da farko da aka gwada zafin jikin matar bayan sun sauka a kasar babu alamar zafin jiki.

    Amma daga bisani sai ta ce bata jin dadi daga nan ne a kai ta asibiti har aka gano cewa cutar coronavirus ce ke damun ta.

    Yanzu haka dai matar na wani asibiti a Arusha tana karbar magani kuma tana samun sauki.

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Coronavirus
  18. Mutum 8,744 sun kamu da coronavirus a Spain

    Mutanen da suka kamu da coronavirus a Spain sun kai 8,744, yayin da mutum 297 suka mutu, a cewar Fernando Simon, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar.

    Ya zuwa ranar Lahadi an samu mutum 7,753 da suka kamu da cutar, inda mutum 288 suka mutu.

    A highway highway at the border with Portugal in Badajoz, Spain.

    Asalin hoton, EPA

  19. An samu karin mutum 172 da suka kamu da Covid-19 a Belgium

    An samu karin mutum 172 da ke dauke da coronavirus a kasar Belgium inda masu dauke da cutar suka kai 1,058.

    A halin yanzu akwai mutum 252 da ke asibiti a Belgium inda 53 daga ciki ke karkashin kulawa ta musamman.

    Mutum biyar sun mutu a kasar sakamakon cutar.

    Mutum biyar sun mutu a kasar sakamakon cutar

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutum biyar sun mutu a kasar sakamakon cutar
  20. Coronavirus: Ina aka kwana a Najeriya?

    Cibiyar yaki da cututuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce ministan lafiyar kasar ya yi karin haske game da matsayin da ake ciki kan coronavirus a kasar.

    Sanarwar da ta walafa a shafinta na Twitter ranar Litinin ta ce minista a ma'akatar lafiya, Dr Olorunnimbe Mamora, da shugaban cibiyar yaki da cututuka masu yaduwa ta kasar, Chikwe Ihekweazu sun yi wa 'yan jarida jawabi a ranar ta Litinin kan cutar ta COVID 19.

    A cewar sanarwar, ya zuwa ranar 15 ga watan Maris, mutum biyu ne suke dauke da cutar a Najeriya, an gano mutum daya kuma ba ya dauke da ita inda aka sallame shi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X