Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Afirka
Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta duniya reshen Afirka ta ce ana samun karuwar yaduwar coronavirus a nahiyar.
Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter ya ce ya zuwa yanzu mutum 795 ne suka kamu da cutar a kasashe 36. Kasashen su ne: Algeriya (82), Benin (2), Burkina Faso (27), Kamaru (16), Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (1), Chadi(1), Congo(1), Ivory Coast (6), Djibouti (1), Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo (14), Masar (256).
Sai kuma Equatorial Guinea (4), Eswatini (1), Habasha (9), Gabon (3), Gambiya (1),Ghana (7), Guinea (2), Kenya (7), Liberiya (2), Mauritius (7), Mauritaniya (2), Maroko (63), Namibiya (2), Nijar (1), Najeriya (12), Rwanda (11), Senegal (38), Seychelles (6), Somaliya (1), Afrika ta Kudu (150), Sudan (1), Tanzaniya (6), Togo (1), Tunisiya (39), da kuma Zambiya (2).
Kazalika hukumar ta ce akwai kasashe takwas da aka samu wadanda suka warke daga cutar. Kasashen su ne: Algeriya(32), Kamaru(2), Masar (28), Morocco 2), Najeriya(2), Senegal(5), Afirka ta kudu (12), da kuma Tunisia(1).