Karin mutum 4 sun kamu da coronavirus a Najeriya

An wallafa

Sabbin mutum hudu sun kamu da coronavirus a Lagos a cewar kwamishinan lafiya na jihar.

Wannan adadin ya sa yawan masu dauke da cutar a Najeriya sun zama 12.

Kwamishinan lafiya na Legas Akin Abayomi ya bayyana wa 'yan jarida samun sabbin mutanen da ke dauke da cutar ne a sakatariyar jihar ranar Alhamis.

Ya ce an yi wa mutum 19 da ake zargi na dauke da cutar gwaji inda aka sanar da biyar da suka kamu a ranar Laraba.

Daga cikin mutanen akwai wadda ta koma Najeriya daga Faransa, da wani da bai yi tafiya ko ina ba amma aka gano yana dauke da cutar.

Sai kuma wani dan Najeriya da ya koma kasar daga Jamus ranar 13 ga watan Maris.

Kwamishinan ya ce a yanzu ana bin sawun mutum 1,300 da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar Covid-19.