Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Coronavirus: Karin mutum biyu sun mutu a Masar

    Dan kasar Masar mai shekara 70 da 'yar Italiya mai shekara 78 sun mutu a wani asibitin da aka kebe su.

    Yanzu mutum shida ne suka mutu daga cutar a kasar ta Masar.

    Labarin ya zo ne yayin da aka gano mutum 30 suna dauke da cutar, abin da ya sa yawansu ya kai 196 a kasar.

    Sabbin wadanda suka kamun 'yan Masar ne wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar, in ji mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar kasar.

    Tun bayan bullar cutar a kasar mutum 26 sun warke sannan kuma an sallame su daga asibitocin da aka killace su, in ji shi.

  2. Na yi nadamar shigar da coronavirus kasata - 'Yar Tanzania

    Wata 'yar kasar Tanzania ta farko da ta shigar da coronavirus kasarta ta nemi afuwar 'yan kasar.

    Wani gidan rediyo na Cloud FM a Dar es Salaam ya ruwaito mara lafiyar tana cewa ''a yi mani afuwa kan wannan abu.''

    Isabella Mwampamba ta yi magana ne da gidan rediyon ta wayar tarho daga gidanta da ke Arusha, a arewacin Tanzania inda take killace.

    Ministan lafiya na kasar ne ya sanar da bullar cutar karo na farko a ranar Talata a kasar.

    Isabella ta koma kasar ne daga Belgium.

    Zuwa yanzu mutum uku ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar.

    Firai Ministan kasar Kassim Majaliwa ya ce sauran mutum biyun su ne wani dan Jamus mai shekara 24 da kuma wani dan Amurka mai shekara 61.

  3. Coronavirus ta shiga duka jihohin Amurka 50

    Cutar numfashi mai hatsari ta coronavirus ta bulla a dukkanin jihohin Amurka 50, yayin da jihar West Virginia ta bayyana rahoton bullar cutar a ranar Talata.

    Da yake bayar da sanarwar bullar tata, Gwamnan jihar Jim Justice ya ce: "Dama mun san tana kan hanya."

    Birnin New York City ya ce yana tunanin kulle birnin baki daya irin yadda yankin San Francisco Bay area ya yi.

    Ya zuwa yanzu mutum 108 ne suka mutu daga cutar, inda aka tabbatar sama da 6,300 sun kamu da ita.

    A duniya baki daya, sama da mutum 200,000 ne suka kamu sannan kusan 8,000 suka mutu.

  4. An dage taron Maulidin Sheikh Nyass saboda coronavirus

    Shugaban Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sanar da cewa an dage taron Maulidin Sheikh Nyass wanda da za a yi a Abuja da Sokoto saboda yaduwar cutar coronavirus.

    Sheikh Dahiru Bauchi ya ce saboda yadda cutar ke yaduwa a makwabtan Najeriya, kuma taron maulidin ba na 'yan Najeriya ba ne kawai, har da ma 'yan wasu kasashe.

    Ya ce ba za a yi taron ba har sai annobar ta lafa a duniya sannan a sanar da ranar da za a gudanar da taron.

  5. Labarai da dumi-dumi, An samu karin mutum 5 masu dauke da coronavirus a Najeriya

    Hukumar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta tabbatar da karuwar mutum 5 masu dauke da cutar coronavirus a kasar.

    Hukumar ta ce duka masu dauke da cutar suna dawo ne daga Burtaniya ko Amurka kwanan nan.

    Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su kwanatar da hankalinsu yayin da jami'an kiwon lafiya ke daukar dukkan matakan da suka dace don yaki da yaduwar cutar a kasar.

    Kawo yanzu mutum 8 ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya.

  6. Ana zargin malamin makaranta da coronavirus a Katsina

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban sakataren ma'aikatar lafiya a jihar Katsina , Dakta Kabir Mustapha ya ce ana zargin wani mutum da coronavirus a jihar Katsina.

    Haka kuma jaridar ta ce mutumin na killace a halin yanzu.

    Kakakin Kungiyar Likitoci ta jihar, Dakta Yahaya Sodangi ya bayyana wa BBC cewa mutumin malami ne a jami'ar Dutsinma ta jihar katsina, FUDMA, da ya dawo daga kasar Malaysia kwanan nan.

    Dakta Yahaya ya ce an dauki samfurin jinin mutumin don yin gwaji kuma ana sa rai sakamakon gwajin zai fito a yau Laraba.

  7. Najeriya ta hana baki daga kasashe 13 shigowa

    Najeriya ta hana baki shigowa daga China da Italy da Amurka da Birtaniya da Iran da Italiya da Korea ta Kudu da Sufaniya da faransa da Jamus da ma wasu kasashen da coronavirus ta yi kamari.

    Hukumar hana kare yaduwar cututtuka ta kasar ce ta sanar da hakan a ranar Laraba a shafinta Twitter.

    Sauran kasashen da Najeriyar ta hana baki shiga cikinta sun hada Koriya Ta Kudu da Spaniya da Faransa da Jamus da Norway da Netherlands da kuma Switzerland.

    NCDC ta ce akwai masu dauke da cutar fiye da 1,000 a kowacce daga cikin kasashen nan.

    Haka kuma, Hukumar ta sanar da cewa za a killace duka matifiya da za su iso kasar daga wadannan kasashen.

    Sannan Najeriya za ta dakatar da ba da takardun shiga wato biza ga 'yan kasashen nan 13.

  8. Karin bayani kan coronavirus

  9. Kasashen Afrika 31 ne coronavirus ta shiga kawo yanzu

    Kawo yanzu kasashen Afrika 31 ne suka tabbatar da shigar cutar coronavirus, inda Gambia ta zama ta baya-bayan nan cikin kasashen.

    Kananan yara hudu sun kamu da cutar a Afrika ta Kudu, wadda kawo yanzu ita ce kasar da ta fi ko wacce a Afirka yawan masu dauke da cutar.

    Kasashen na kara tsaurara matakan shiga da fita.

    Kusan mutane 1000 ne aka killace a Habasha, wanda ake tunanin sun yi mu'amala da wasu masu dauke da cutar.

    A Najeriya, likitoci a asibitocin gwamnati 14 sun fara yajin aiki na sai Baba ta gani, bayan rashin biyansu albashi tsawon watanni.

    Yayin da a Rwanda rahotanni ke nuna cewa gwamnati ta saka tsayayyen farashi na kayan abinci don kada a samu hauhawan farashin.

    A Malaysia, jami'ai na kokarin lalubo wani bangare na wata tawagar mutum dubu goma sha shida da suka halarci wani taron addini na kwana hudu a watan jiya, inda kuma ake tunanin cutar ta yadu.

    An dai gano cewa wasu daga cikin mutanen sun halarci taron ne daga Afirka kuma akwai yiwuwar sun koma kasashensu dauke da cutar.

  10. An samu karuwar masu dauke da coronavirus a Ghana

    Ghana ta tabbatar da mutum na bakwai da ya kamau da coornavirus a kasar.

    Waannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan gano wasu mutum hudu masu dauke da cutar a Ghana.

    kawo yanzu, ana zargin cewa mutum 143 na dauke da cutar ta COVID-19 kamar yadda cibiyar bincike ta Noguchi Memorial Institute (NMIMR) da cibiyar bincike ta Kumasi (KCCR) suka ce.

  11. Coronavirus: An rufe sansanonin 'yan bautar kasa a Najeriya

    Ministan matasa da wasanni a Najeriya, Sunday Dare ya sanar da rufe sansanonin 'yan bautar kasa, NYSC, a kasar.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Dare ya ce za a dakatar da horon da ake ba su a sansanin amma za a tura su wuraren da za su yi aikin bautar kasa wato PPA kuma za a biya su a albashinsu yadda ya kamata.

    Ya ce wannan wani mataki ne da gwamnati ta dauka don hana yaduwar cutar COVID- 19.

  12. Masu dauke da coronavirus a Afrika ta Kudu sun karu

    Afirka ta Kudu ta fuskanci karuwar mutanen da suka kamu da coronavirus- inda yanzu suka kai mutum 116, yayin da kasar ta gabatar da sabbin matakan rufe iyakokinta da makarantunta.

    Sama da fasinjoji dubu daya ne suke killace a wani jirgin ruwan yawon bude ido a birnin Cape Town bayan da aka samu mutum daya da ake zargin yana dauke da cutar.

    Yawan mutanen suka kamau da cutar a Afirka ta Kudu na karuwa.

    Mafi yawan mutanen da ke dauke da cutar sun koma kasar ne daga kasashen waje- musamman daga Burtaniya.

    Amma cutar ta yadu ga mutum 14 a tsakankanin 'yan kasar, kuma hakan ya kara jefa hukumomi cikin fargaba.

    An rufe duka makarantu a kasar daga yau kuma an haramta wa baki daga kasashen da cutar ta yadu sosai shiga Afrika ta Kudu.

  13. Kamaru ta tsaurara matakai kan coronavirus

      • Marubuci, Mohaman Babalala
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili daga Kamaru

    Gwamnatin Kamaru ta dauki wasu matakai 13 da za su fara aiki daga yau 18 ga watan Maris kan coronavirus

    An dauki matakan bayan wani taron gaggawa da Firaminista Joseph Dion Ngute ya shugabanta, wanda kuma daukacin majalisar Gwamnati ta halarta.

    Sakamakon wannan taron ya bayyana cewa za a rufe duka iyakokin kasar ta sama da ta ruwa da ta kasa. Sa’annan kuma za a daina ba da takardun izinin shiga Kamaru daga kasashen ketare.

    Za a rufe ajujuwa a makarantun boko ta kasa, na Gwamnati da masu zaman kansu daga firamare har izuwa jami’a tare da dakatar da yin karatu.

    Hakanan kuma an hana shirya duk wasu taruka da suka kunshi mutane sama da 50.

    Duka gidajen cin abinci da mashaya hadi da wasu wuraren nishadi za su kasance a rufe.

    Ya kamata kuma mutane su takaita yin zirga-zirgar da suke yi, wato su kiyayi yin balaguro ba tare da wasu kwararan hujjoji ba.

    Su kuma direbobin motocin haya na bas da na tasi za su daina cunkusa mutane a cikin ababan hawansu.

    Ma’aikatun Gwamnati kuma za su fi maida hankali wurin yin musayar sakwanni a tsakaninsu ta hanyar intanet.

    Sai dai kuma za a bar jiragen daukar kayan abinci da wasu kayan kasuwanci suna zirga-zirga.

    Hakanan ma duk wasu 'yan Kamaru da suke ketare, har idan akwai wata bukatar da suke dauke da ita a cikin kasa, na iya tuntubar ofishin jakadancin Kamaru a kasar da ta karbi bakwancinsu domin samun izinin shiga kasa.

  14. Nijar ta rufe iyakokinta na tudu da na sama don tsoron coronavirus

    Duk da cewa a Jamhuriyar Nijar ba a samu tabbacin bullar coronavirus ba, duk da haka Shugaba Mahamadou Issoufou ya ba da sanarwar rufe iyakokin kasar na sama da na tudu, tare da haramta tarukan jama'a da rufe makarantu daga ranar Juma'a.

    Da maraicen jiya ne shugaban ya yi wa al'ummar Nijar jawabi don sanar da su halin da ake ciki da kuma matakan da gwamnati ta dauka don kare kasar daga cutar Covid-19.

  15. Budewa

    Rahotannin ranar Laraba 19 ga watan Maris 2020

    Masu bin mu a wannan shafi assalamu alaikum. Halima Umar Saleh da Fauziyya Kabir Tukur ne suke muku fatan kun wayi gari lafiya.

    Yau ma kamar kullum za mu dora daga inda muka tsaya jiya wajen kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da duniya baki daya.

    Rahotannin namu za su fi mayar da hankali ne kan yaki da annobar coronavirus da ake fama da ita a duniyar.

    Kuna iya komawa kasan wannan shafi don karanta abubuwan da suka faru a jiya Talata idan har ba ku samu karanta su ba.

  16. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku game da coronavirus da wasu al'amuran da suka shafi kasashen Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.

    Ka tare mu ranar Laraba domin ci gaba da samun labaran da suka shafi rayuwarku.

    Amma kafin nan, za ku iya zuwa kasa domin karanta labaran da muka kawo muku yau.

    Kazalika, za ku iya karanta sauran labaranmu a bbchausa.com ko kuma shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

    Ni ne Nasidi Adamu Yahaya nake yi muku fatan alheri.

  17. APC ta yafe wa 'ya'yanta laifin da suka yi

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dage haramcin wata shida da ta yi wa wasu daga cikin manyan 'ya'yanta.

    Shugaban jam'iyyar, Mr Adams Oshimohle, wanda ya bayyana wannan mataki a wurin taron koli na jam'iyyar ranar Talata, ya ce an dage haramcin da aka yi wa mataimakin shugaban jam'iyar a yankin arewa maso yamma Senata Lawal Shu'aibu da kuma mataimakinsa Abdulkadir Inuwa domin samun zaman lafiya a jam'iyyar.

    “A yunkurinmu na yin sulhu, kwamitin koli ya yi nazari kan batun mataimakin shugaban jam'iyyar a yankin arewa maso yamma Senata Lawal Shuaibu, da kuma abubuwan da muke ganin ya yi na musguna wa jam'iyya, wanda ya sa aka dakatar da shi, inda ya janye haramcin.

    “Haka kuma an yi nazari kan batun Inuwa Abdulkadir, wanda aka dakatar kuma mun janye dakatarwar da aka yi masa", in ji Oshimohle.

    Sai dai ya ce an bukaci jami'an biyu sun janye dukkan kararrakin da suka kai jam'iyyar kotu.

    Ya kara da cewa 'yan jam'iyyar hamayya za su yi bakin cikin wannan sulhu da aka yi.

    Jam'iyyar ta APC dai ta fada cikin rikici inda a kwanakin baya bayan nan wata kotu ta cire Mr Oshimohle daga shugabancin jam'iyyar ko da yake daga bisani kotun daukaka kara ta yi uamarnin ya ci gaba da shugabancinta.

    Har yanzu dai batun yana gaban kotu.

  18. Coronavirus: Farashin sinadarin wanke hannu ya yi tashin gwauron zabi a Ghana

    Wasu 'yan kasar Ghana na ci gaba da kokawa a kan yadda farashin sinadarin wanke hannu, wato hand sanitizer ya yi tashin gwauron zabi tun bayan barkewar cutar coronavirus a kasar.

    Tuni dai al`umma suka fara Allah wadai da masu sayar da sindarin wanke hannun bayan sun kara farashin da kaso sama da dari cikin dari.

    Wakilin BBC a Accra, Muhammad Fahd Adam ya ce tunu wasu 'yan kasar ta Ghana suka fara amfani da wata giya mai zafi a maimakon sinadarin wanke hannu ko hand sanitizer wanda shi ma yake dauke da sinadarin giya a ciki.

  19. Labarai da dumi-dumi, Saudiyya ta dakatar da yin sallah a masallatai

    Hukumomi a Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, idan ban da masallacin Ka'abah da kuma na Madina, a cewar kamfanin dillacin labaran kasar.

    A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuewa aikin Umrah da na Hajji siga kasar saboda yaduwar cutar coronavirus.

    An dauki matakin ne makonni kadan kafin azumin watan Ramalana inda Musulmi kan yi tururuwa zuwa kasar domin gudanar da ayyukan ibada.

    Ya zuwa yanzu, mutum 133 aka tabbatar sun kamu da cutar a Saudiyya.

  20. Coronavirus: El-Rufai ya dakatar da taron zuba jari a Kaduna

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce ta dakatar da taron zuba jari da za a yi a jihar a yunkurin ta na kare lafiyar baki da 'yan jihar.

    Gwamnatin jihar ce ta bayyana haka ranar Talata a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

    "A wani mataki na rigakafi domin kare lafiyar bakinmu da sauran jama'a, gwamnatin Kaduna ta jinkirta gudanar da taron zuba jari na biyar sai abin da hali ya yi.

    "Za a sanar da lokacin gudanar da taron da zarar an ci karfin cutar coronavirus," in ji sanarwar.

    Ranar ta Talata ce dai hukumomin lafiyar Najeriya suka ce an samu wata mace dauke da coronavirus a kasar, wadda ta zama ta uku da aka samu da cutar a Najeriya.

    Matar mai shekara 30 ta kowa kasar ne daga Birtaniya ranar 13 ga watan Maris - kuma ta killace kanta bayan isowar ta, amma daga bisani ta dinga ganin alamun cutar.