Wata cuta da ba a san kanta ba ta bulla a yankin Somali da ke gabashin kasar Habasha.
A 'yan shekarun da suka gabata cutar ta hallaka daruruwan jama'a, wadanda yawancinsu makiyaya ne da ke kiwo a yankin Tafkin Ogaden, inda kamfanonin kasashen waje ke aikin neman mai da gas.
Wani jami'in yankin ya ce sama da mutum dubu biyu suka mutu sakamakon cutar da ba a san ko mece ce ba.
Sannan akwai wasu da ba a iya gano adadinsu ba yanzu haka na kwance.
Juwaira Ali wata ce data shafe watannin tana bincike kan cutar, ta ce alamomin ciwon abin ta da hankali ne.
''Jini na fitowa ta hanci, idon mutum na juyewa ya koma launin ruwan dorawa, tsananin zazzabi, yawaita suma da kuma kisa,'' in ji ta.
Juwaira ta ce watakil cutar na da alaka da ayyukan da ake yi ko gurbatar muhalli da mai ko iskar gas ke haifarwa - ko daya ta ce akwai bukatar masana kimiya su tabbatar da hakan.
''Mazaunan yankin sun bayyana cewa akwai kamfanoni d ake gurbata muhalli da wani sinadari kamar hoda idan aka yi ruwa, hodar sai ta hade da ruwan kogi, wanda mutane ke sha -kullum abin da ke wakana kenan.''
Kamfanonin da ke aiki a yankin sun ki cewa Uffan kan gurbata muhalli da sinadarin ke yi, haka nan ma hukumomin Ethiopia, duk da karuwar da ake samu na mutanen da wannan annoba ke yi wa illa.
''Jami'an gwamnati a Addis Ababa sun musanta akwai matsalolin muhalli da ke shafar lafiya.
''Akwai ma wani jami'i guda da ya musanta cewa mutane na rayuwa a yankin, kalaman da tabbas ya saba abin da muka sani.''
Firai Minista Abiy Ahmed ya ce man fetur da iskar gas su ne makomar Ethiopia nan gaba da za su samar da karin ayyukan yi.
Sai dai kokarin da aka yi a baya na amfani da albarkatun yankin Ogaden ya haifar da rikici - an yi wata zanga-zanga da ta tilastawa Sarki Haile Selassie yin watsi da aiki.
'Yan tawaye sun jima suna rigima a yankin.
A shekara ta 2007 sun far wa wani kamfanin matatan man China, inda suka kashe mutum 74.
Don haka mai yiwuwa wannan cutar ta yi tasiri wajen jinkirta habbaka albarkaun wannan yanki a yanzu.