Za a sallami wanda ya kawo Coronavirus Najeriya daga asibiti
Gwamnatin Jihar Legas za ta sallami dan kasar Italiyan nan da ya shigo da cutar coronavirus Najeriya bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa yanzu ba ya dauke da cutar.
Kwamishinan lafiya na Legas, Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron manema labarai, inda ya ce maras lafiyar da aka bai wa kulawa a asibitin Yaba da ke Legas ya warke.
Da yake bayyana labarin a matsayin ci gaba ga Najeriya, Abayomi ya ce ba za a sallame shi ba tukunna har sai an sake yin wani gwajin cikin awa 48 domin tabbatarwa.
Ya kara da cewa idan aka sake ganin ba ya dauke da cutar a karo na biyu sai a sallame shi.