Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ganduje ne ya bukaci na karbi Sarki Sanusi na II - Gwamnan Nasarawa

    Gwamnan jihar Nasarawa da ke Najeriya, Abdullahi Sule, ya ce takwaransa na jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya kira shi a wayar tarho inda ya bukaci ya amince a kai tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II can idan an sauke shi daga kan mulki.

    Ranar Litinin din makon jiya ne gwamnatin Kano ta sauke sarkin daga gadon sarauta bayan ta zarge shi da laifin kin yi wa Gwamna Ganduje biyayya.

    A ranar ce kuma aka dauke shi a jirgin mai saukar unguwa zuwa kauyen Loko da ke jihar Nasarawa inda ya kwana daya, ko da yake washe gari an mayar da shi garin Awe na jihar ta Nasarawa.

    Jaridar Daily Trust ta ambato Gwamna Sule yana shaida wa wasu 'yan jarida cewa: "Jim kadan bayan an sauke shi [Sanusi na II], gwamnan Kano ya kira ni inda ya ce 'yanzu muka sauke Sarki kuma muna tunanin kawo shi jihar Nasarawa; Idan za ka amince ka karbe shi. Na shaida masa cewa zan yi matukar farin ciki na karbe shi.”

    Batun kai tsohon sarkin jihar Nasarawa dai ya jawo ce-ce-ku-ce inda kungiyoyi da jama'a daban-daban suka ce gwamnati ba ta da hurumin tura shi gudun hijira bayan ta sauke shi.

    Lauyoyin Sarki Sanusi na II sun gurfanar da jami'an tsaro da gwamnatin jihar Kano a gaban kotu, wacce ta yanke hukuncin sakin sarkin da ba shi damar zama a duk inda yake so.

  2. Ana ci gaba da aikin ceto a gobarar da ta tashi a Lagos

    Hukumomi a jihar Lagos da ke Najeriya na ci gaba da aikin ceto da kokarin dakile duk wata hanya da gobara za ta kara tashi kamar yadda ta yi da misalin karfe 5:00 na asuba ranar Litinin bayan an kashe ta da misalin 11:30 na daren Lahadi.

    A safiyar Lahadi ne aka samu fashewar wani abu a jihar ta Lagos da ake zargin bututun mai ne wanda ya jawo mahaukaciyar gobara da rushewar gidaje da kuma asarar rayukan mutum 15.

    A ranar ta Lahadi, hukumomi da kungiyoyin bayar da agajin gaggawa sun yi ta kai dauki domin kashe gobara da kuma ceto wadanda gine-gine suka rufta a kansu.

    Tun bayan faruwar lamarin, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross da kuma hukumar baya da agaji ta gaggawa ta tarayya da ta jihar Legas tare da hadin gwiwar jami'an tsaro ke ta kokarin kai dauki.

    Babu tabbacin asalin abin da ya kawo karar da aka ji ta abin fashewa wanda hakan ya jawo gobara, sai dai ana zargin cewa bututun mai ne ya fashe.

  3. Kasashen Afirka da ke fama da coronavirus

    Ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya reshen Afirka ya ce kawo yanzu kasashe 27 ne a nahiyar ke fama da cutar coronavirus.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ofishin ya ce kasar Masar ce ta fi yawan masu fama da coronavirus inda take da mutum 110, yayin da kasashen Togo da Gabon da Guinea da E. Guinea da Congo da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mauritania da Eswatini da Liberia da Sudan suke da mutum daya kowacce.

  4. Mutum hudu sun sake kamuwa da coronavirus a Ghana

    Hukumomin lafiya a Ghana sun tabbatar da karin mutum hudu da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a kasar.

    Ma'aikatar lafiyar kasar ce ta bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Litinin domin sanar da `yan kasar halin da ake ciki tun bayan barkewar cutar a Ghana.

    Yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum shida.

    Lamarin da ya sa kenan a karo na biyu tun bayan barkewar cutar coronavirus a Ghana shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya yi wa al`umma jawabi inda ya bayar da izinin dakatar da dukkan taruruka da suka hada da na makoki da jana`iza da na coci-coci da masallatai da aure zuwa makonni hudu.

  5. Coronavirus: Kasashen Afirka na daukar matakai masu tsauri

    Kasashe da dama na Afirka na ci gaba da daukar matakai masu tsauri da zummar hana yaduwar cutar coronavirus.

    Tuni Afrika ta Kudu ta rufe iyakokinta kuma ta haramta gudanar da manyan taruka.

    Ita ma kuma Kenya ta saka dokar hana tafiye-tafiye.

    An dauki matakan ne domin dakile yaduwar cutar a nahiyar ta Afirka wadda ke da rauni ta fannin kiwon lafiya.

    Akalla kasashen Afirka 26 ke dauke da wannan cuta.

    Akasarin wadanda aka samu da cutar a kasashen Afirka sun zo ne daga Turai da kuma Arewacin Amurka.

    Amma Afirka ta Kudu ita ce kasar da ta saka doka mafi tsauri ga 'yan kasarta.

  6. Aisha Buhari ta bi sahun masu fadakarwa kan coronavirus

    Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta bi sahun wasu iyalan shugabannin kasashen duniya da ke fadakarwa kan yadda za a kauce wa cutar coronavirus.

    Wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter a karshen mako, ya nuna wani mawaki yana waka kan matakan da mutane za su dauka wurin kauce wa kamuwa da cutar.

    Matakai shida ne, wadanda suka hada da yawaita wanke hannu da daukar matakan rufe baki lokacin da mutum yake yin atishawa.

    Najeriya dai na cikin kasashen da aka samu bullar coronavirus, ko da yake hukumomi sun ce suna daukar matakan dakile yaduwarta.

  7. An sake samun mutumin da ya kamu da coronavirus a Kamaru

    Hukumomi a Kamaru sun bayyana cewa an samu karin mutum guda da ya kamu da cutar coronavirus.

    Hakan ya kai ga adadin mutane 5 kenan da suke dauke da cutar daga ranar 6 ga watan Maris zuwa yanzu.

    Kamar sauran mutane hudu na farko, shi ma wannan mutum na 5 wanda dan asalin Kamaru ne ya shigo da cutar ne daga kasar Faransa.

    Ministan kiwon lafiya ya gayyaci daukacin fasinjojin kamfanonin jiragen sama na Air France da Brussels Airlines wadanda suka shigo Kamaru a ranakun 6 da 7 na watan Maris su tuntubi hukumomin kiwon lafiya a wasu lambobin da aka wallafa domin a binciki lafiyarsu.

    Ya ce mutane biyar din da suka kamu da coronavirus na samun kula a wasu asibitoci biyu na birnin Yaoundé.

    Sai dai har yanzu babu wani dan Kamaru mazaunin cikin gida da ya kamu da wannan cutar.

  8. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanmu da wannan rana ta Litinin, wannan shafin zai kawo muku rahotanni da kuma labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya, musamman game da cutar coronavirus da ta addabi duniya. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu.