Tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya John Mikel Obi ya bar kungiyar Trabzonspor bisa amincewar bangarorin biyu 'yan sa'o'i bayan ya ce ya kamata a soke wasanni a gasar Turkish Super Lig ta kasar Turkiiyya saboda coronavirus.
Gasar Super Lig na daya daga cikin 'yan kalilan da ba su soke buga wasanni ba a Nahiyar Turai saboda yaduwar cutar, duk da cewa babu 'yan kallo ake buga wasannin.
Mikel mai shekara 32, ya bayyana ra'ayin da ya ci karo da na hukumar a shafinsa na Instagram.
A wani bayani da kulob din ya fitar ranar Talata ya ce dan wasan ya katse kwantaraginsa, sannan kuma ya hakura da albashinsa domin ya zama ba shi da kulob.
A ranar Asabar ne Obi ya rubuta a Instagram "akwai sauran abbubuwa a rayuwa fiye da kwallon kafa, sannan ya ce: "Ba na sha'awa kuma ba zan buga wasa a irin wannan yanayin ba.
"Ya kamata a ce kowa yana gida tare da iyalansa a wannan yanayin mai hadari. Ya kamata a dakatar da wasannin kakar bana yayin da duniya ke fuskantar tashin hankali."
Ra'ayin na Mikel Obi ya jawo martani na goyon daga tsofaffin 'yan kwallon da suka taka leda a Turkiyya: Radamel Falcao wanda ya ce "haka yake John", sai kuma Didier Drogba da ya ce "tabbas ka yi hangen nesa".
Mutanen da suka kamu da cutar a Turkiyya guda shida ne a lokacin da Mikel ya yi batun, duk da cewa yanzu sun kai 47.