'Har yanzu APC ba ta cika jam'iyya ba'
Masu sharhi kan lamurran siyasa a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan rikicin shugabanci da ya addabi jam'iyya mai mulki a kasar.
Jam'iyyar ta APC ta kasance cikin rikici tun bayan da aka kammala manyan zabukan watan Fabarairun 2019 a kasar.
Rashin jituwa tsakanin wasu gwamnoni da kuma shugabancin jam'iyyar na kasa karkashin Adams Oshiomole ya janyo rarrabuwar kai tsakanin jiga-jigan jam'iyyar.
Wannan ta sa masharhanta irinsu Dakta Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja ke ganin har yanzu "APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba".
Ko a ranar Asabar rahotanni sun ambato kungiyar gwamnonin APC tana kiran kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa da ya sauke Oshiomole daga mukaminsa, inda suka goyi bayan hukuncin wata kotu a Abuja.
A ranar Larana ne wata kotu a Abuja ta yanke hukuncin korar Adams Oshiomole daga mukaminsa na shugaban jam'iyyar ta APC na kasa.
Wannan ya biyo bayan karar da wasu suka shigar cewa tuni aka dakatar da Mista Oshiomhole daga jam'iyyar APC a jiharsa ta Edo, abin da alkalin ya dogara da shi kuma ke nan yayin bayar da hukuncin.
Sai dai a daukaka karar da ya yi, wata kotu a Jihar Kano ta yi umarni da Oshiomhole ya ci gaba da zama a mukaminsa har sai bayan ta yi hukunci.

Asalin hoton, Getty Images
