Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Facebook da Twitter sun cire shafukan bogi a Najeriya da Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shafukan na da alaka da Rasha amma a Ghana da Najeriya suke.
Twitter da Facebook sun ce sun dakatar da wasu kananan shafuka da ke da alaka da Rasha, a Ghana da Najeriya, saboda yunkurinsu na son hada husuma.
Kamfanonin sada zumuntar sun ce masu amfani da shafukan na neman Amurkawa ta hanyar yi masu maganganun da suka shafi wariyar launin fata da hakkin dan Adam.
An cire wasu shafukan daga Instagram, wanda kamfanin Facebook ya mallaka.
Kamfanin ya ce sama da mutum 260,000 na bin daya daga cikin shafukan a Instagram.
Coronavirus ta bulla a Gabon
Kasar
Gabon wadda ta rufe iyakarta da Kamaru tun wasu ‘yan kwanaki domin kare
al’umarta daga yaduwar da cutar Coronavirus take yi a duniya, ta bayyana bullar
cutar a kasar a karo na farko.
A
wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, sabanin yadda cutar take bayyana a
wasu kasashen Afirka, wani dan asalin kasar ne mai shekara 27 a duniya da ya
dawo daga birnin Bordeaux na kasar Faransa a ranar 8 ga watan Maris ya shigo
dauke da kwayar cutar.
Alhalin kuma sakamakon gwaji na farko da aka yi masa a
filin jirgin sama bai nuna cewa yana dauke da wannan kwayar cutar ba kamar
yadda sanarwar ta ci gaba da bayyanawa.
A
washe gari ne kuma ya fara tari, da ciwon makogwaro hakan kuma suka
dagula masa yanayin yadda yake nunfashi, tuni aka kai shi asibiti domin
bincike.
Sakamakon bincike da aka yi masa sun tabbatar cewa yana dauke da
kwayar cutar Covid-19.
Sai
dai kuma sanarwar ta gwamnati ta kammala da cewa maras lafiyar na murmurewa
kadan-kadan, sa’annan kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen da
ya yi cudanya da su.
Labarai da dumi-dumi, An dakatar da gasannin Champions League da Europa
An dage duka gasannin UEFA, har da wasannin da za a yi a gasannin zakarun Turai na Champions League da Europa ran 17 da 18 ga wannan watan na Maris, saboda barkewar coronavirus.
Haka kuma na dakatar da fitar da jadawalin wasannin da za a buga, wanda da za a yi a 20 ga watan Maris
An dage wasannin da za a yi tsakanin Manchester City da Real Madrid, da kuma Juventus da Lyon, da kuma Barcelona da Napoli da kuma tsakanin Bayern Munich da Chelsea a gasar Champions League a makon gobe.
An soke wasannin Manchester United da Wolves da Rangers a gasar Europa kamar yadda suka wallafa a shafinsu na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Bayanai kan yaduwar coronavirus a Afirka a yau Juma'a
Asalin hoton, b
Kotu ta umarci a bai wa Sarki Muhammadu Sanusi II damar walwala
Kotu ta umarci a bai wa Sarki Muhammadu Sanusi II damar shiga ko ina a Najeriya ban da Kano.
Haka kuma kotun ta ba da kwana uku a mika wannan hukuncin da aka yanke ga wadanda aka kai karar kuma su yi aiki da ita.
Wadanda aka kai karar sun hada da hukumar tsaro ta farin kaya, da sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kwamishinan shari'a na jihar Kano da kuma ministan shari'a na Najeriya.
An dage zaman kotun sai ranar 26 ga wannan watan na Maris.
Coronavirus ta sa al'amura na tsayawa cak a duniya
Asalin hoton, Reuters
Ana ta rufe makarantu, da soke gudanar da wasanni da rufe bangarorin al'adu a fadin duniya a kokarin da ake yi na dakile yaduwar coronavirus.
A Amurka an dakatar da duk manyan wasanni har tsawon wata daya.
Kuma Faransa na daya kasashen da a baya-bayan nan ta sanar da rufe makarantu, da jami'o'i da wuraren rainon yara.
Firai Ministan Canada Justin Trudeau ya killace kansa na tsawon kwana 14 bayan da aka samu matarsa da cutar. Sai dai shi bai fara nuna alamu ba.
Haka kuma an kwantar da Ministan Harkokin Cikin Gida na Australia Petr Dutton a asibiti bayan an gano yana dauke da ita.
Fiye da mutum 125,000 ne aka gano suna dauke da cutar ta Covid-19 a kasashe 118 a fadin duniya, a cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya.
Yawan wadanda suka mutu ya haura 4,600.
An fara zaman sauraren karar Muhammadu Sanusi II yau
An fara zaman sauraren karar da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai bisa tsare shi da aka yi a jihar Nasarawa bayan sauke shi da aka yi daga mulkin sarautar Kano.
Malam Muhammadu Sanusi ya shigar da karan ne a gaba wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya.
Tsohon sarkin yana karar mutum hudu ne da suka hada da supeto janar na 'yan sandan Najeriya, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kwamishinan shari'a na jihar Kano da kuma ministan shari'a na Najeriya.
Ya bukaci mutanen da ya shigar kara su biya shi diyyar naira miliyan 50 saboda keta masa mutunci da kuma take hakkokinsa da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi.
Bayanan hoto, Harabar babban kotun da ake zaman
Bayanan hoto, Lauyoyin Muhammadu Sanusi II
Bayanan hoto, Daya daga cikin 'ya'yan tsohon sarkin Ummi Sanusi (a tsakiya) tare da wasu
Coronavirus: Firanministan Canada da matarsa sun kebe kansu
Asalin hoton, Reuters
Sophie Grégoire Trudeau, matar Firanministan Canada, Justin Trudeau ta kamu da cutar coronavirus, in ji wata sanarwar ofishin firanministan.
"Za a ci gaba da kebe ta a yanzu. Ta samu sauki kuma tana daukar matakan kariya," a cewar sanarwar.
A halin yanzu, Firanministan da matarsa sun kebe kansu.
Ofishin Mista Trudeau sun fitar da sanarwar cewa Firanministan na cikin koshin lafiya kuma ba shi da wasu alamu na cutar, amma zai ci gaba da keba kansa tsawon mako biyu.
Amma ba za a yi wa Mista Trudeau gwajin cutar ba tukuna.
Kawo yanzu a kalla mutum 103 ne suke dauke da cutar a Canada.
El-rufa'i na hanyarsa ta kai wa Muhammadu Sanusi II ziyara
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i na hanyarsa ta zuwa garin Awe don ganawa da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Gwamnan ya wallafa wani sako tare da hotonsa a shafinsa na Twitter ne yana bayyana hakan.
Dama dai a'yan kwanaki bayan sauke tsohon sarkin daga karagar mulki ne Gwana El-rufa'i ya ba shi mukamai har guda biyu a jihar Kaduna, wato Uban jami'ar jihar Kaduna da kuma Mataimakin Shugaban kwamitin gudanarwa a hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kaduna, (KADIPA).
An samu mutum na farko da coronavirus a Kenya
Kenya ta tabbatar cewa wata mata 'yar kasar ta kamu da cutar Covid-19.
Ministan lafiya na kasar Mutahi Kagwe ya ce ta shiga kasar ne daga Amurka ran 5 ga watan Maris kuma na gano tana dauke da cutar ranar Alhamis.
Daga Amurka ta tsaya a Landan amma iyakarta filin jirgi ba ta shiga cikin garin ba.
Ministan ya ce a yanzu marar lafiyar ba ta cikin mawuyacin hali kuma tana cin abinci sosai, sannan kuma zazzabinta ya sauka.
Za a ci gaba da kebe ta har sai ta warke, a cewarsa.
Haka kuma, gwamnatin kasar ta sanar da haramta wa duk ma'aikatan gwamnati fita kasar ba a bisa wani dalili mai kwari ba don gudun kamuwa da cutar coronavirus.
Asalin hoton, Getty Images
Coronavirus ta shiga Ghana
Ghana, ta zama kasa ta baya-bayan nan da aka tabbatar da bullar cutar coronavirus a nahiyar Afirka.
Da maryacen jiya ne, hukumomi suka tabbatar da gwajin samfurin jinin da aka yi wasu mutane da suka je kasar daga ketare.
An gano suna da cutar ne bayan da aka yi masu gwaji a wani dakin gwaji na Noguchi Memorial Institute ean 12 ga wannan watan na Maris.
Ma'aikatar lafiyar kasar ce dai ta tabbatar da cewa an samu mutum biyu da suka je kasar daga Turkiyya da kuma Norway da wannan cuta da ta zama annoba gama-duniya.
Rahotanni sun nuna cewa an kebe mutanen biyu a wani bangare na asibiti.
Ma'aikatar lafiyar kasar ta bude wani asibiti mai gado 100 a wani yanki da ke nesa da gari don killace masu ke dauke da cutar.
Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce marasa lafiyar ba sa cikin mawuyacin hali.
Marabanku!
Marhabin lale da masu bibiyarmu a wannan shafi, wanda lke kawo maku labarai daga Najeriya da makwabtanta da ma sauran kasashen duniya.
Da fatan za ku kasance da mu a yau Juma'atu babbar rana don sanin abubuwan da ke faruwa a duniyar.
Mu kwana lafiya
Karshen rahotannin kai-tsaye ke nan.
Jama'a mu kwana lafiya.
Sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu.
Muhammadu Sanusi yana Awe har yanzu, bai koma Lagos ba
Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II yana garin Awe har yanzu bai koma Lagos ba kamar yadda wasu rahotanni ke cewa a Najeriya.
BBC ta samu tabbacin cewa sarkin yana can kuma an kara tsaurara matakan tsaro a kofar goidan da sarkin ke zaune.
Rahotanni sun nuna sojoji ne suke tsaron gidan, inda suka maye gurbin 'yan sanda da suka kasance tare da shi tun farkon komawarsa garin daga kauyen Loko da aka kai shi tun farko.
Kazalika wasu fitattun mutane a jihar ta Nasarawa sun ziyarci sarkin a yau Alhamis da suka hada da Sarkin Lafiya, Sidi Dauda Bage da Gwamna Abdullahi Sule da kuma Sarkin Garin Awe.
Duk mai tari da zazzabi ya killace kansa na tsawon kwana bakwai - Boris Johnson
Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Birtaniya ta umarci duk wanda ya san yana tari ko zazzabi ya killace kansa a gida tsawon mako guda, a wani mataki da kasar ke dauka don hana yaduwar coronavirus.
Daga ranar Juma'a kuma za a hana tafiye-tafiye na makarantu zuwa kasashen waje, sannan an shawarci tsofaffi da wadanda suka san ba su da isasshiyar lafiya da ka da su je shawagi na jiragen ruwa.
Firai Minsita Boris Johnson ya ce ''wannan annoba ce mafi muni a zamanin nan.''
Zuwa yanzu mutum 10 ne suka mutu a Birtaniya sakamon cutar.
Akwai masu dauke da cutar 596 a fadin kasar.
Da yake jawabi kan matakan a wani taron gaggawa, Mista Johnson ya ce ''Wasu mutanen na kwatanta cutar da irin murar da aka saba ta yanayi, amma ba haka ba ne.
''Rashin ingantacciyar garkuwar jiki na sa cutar ta zama mai hadari.''
''Za ta ci gaba da yaduwa, amma ina tare da ku, ina tare da al'ummar Birtaniya, iyalai da yawa za su rasa masoyansu kafin lokacinsu ya yi.''
Yawan masu dauke da cutar a Birtaniya sun karu da mutum 100 a ranar Alhamis daga 456 a ranar Laraba - Ingila na da 491, da 60 a Scotland da 20 a Arewacin Ireland da kuma 25 a Wales.
Ra'ayoyin mutanen Awe kan Sarki Sanusi II
Bayanan sautiSaurari ra'ayoyin al'ummar Awe bayan da aka mayar da Sarki Sanusi II jihar Nassarawa
Matakin da
hukumomi a Najeriya suka dauka na mayar da tsohon Sarkin Kano Muhammadu
Sanusi II zuwa garin Awe da ke jihar Nasarawa a Najeriya na ci gaba da daukar
hankulan ‘yan kasar.
Bayan sauya masa gari da aka yi, an kuma jibge jami’an tsaro
a gidan da aka kai shi, kuma sun hana shi ‘yancin walwala har ma da na ganawa
da mutanen da suka rika isa garin domin duba halin da yake ciki.
BBC ta ziyarci garin na Awe kuma wasu mutanen garin sun bayyana yadda suka ji bayan da aka mayar da tsohon sarkin
can.
Firai Ministan Canada ya killace kansa saboda coronavirus
Firai Ministan Canada Justin Trudeau ya killace kansa saboda fargabar cutar coronavirus, a cewar ofishinsa.
Mai dakinsa, Sophie Gregoire-Trudeau ta fara nuna alamun rashin lafiya ranar Laraba.
Mr Trudeau dai bai fara nuna wata alama ta rashin lafiya ba.
Bisa shawarar da likitansa ya ba shi, zai ci gaba da ayyukansa na yau da kullum yayin da zai rika sa ido kan lafiyarsa amma kuma yanzu yana aiki ne daga gida, a cewar sanarwar.
Tuni dai aka dage wasu taruka da aka tsara Firai Ministan zai gudanar nan da kwana biyu masu zuwa.
Asalin hoton, REUTERS
An gayyaci alarammomin makarantun allo zaman Majalisar Wakilan Najeriya
Asalin hoton, Twitter/House of Reps
Wani dan majalisar wakilan Najeriya Dr Balarabe Kakal ya gayyaci alarammomi na makarantun allo zaman majalisar da aka yi yau Alhamis.
An gayyaci alarammomin ne don su saurari muhawarar da aka fara yau kan yunkurin da ake na kawo maslaha ga barace-barace da kuma inganta karatun tsangaya.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Bodinga/Dange-Shuni/Tureta ne ya gabatar da kudirin a zauren majalisar.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman tafka muhawarar har da alarammomi na tsangaya daga sassa daban-daban na arewacin jihohin kasar.
Kalubalen da masu cutar koda ke fuskanta
Bayanan sautiSaurari hirar Raliya Zubairu da Malam Wali Ado Rano Shugaban masu fama da ciwon koda a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya
Yayin da ake Ranar Koda ta duniya yau Alhamis da nufin wayar da kan al'umma game da aikin kodar da ciwonta da kuma kariya daga ciwon, Shugaban masu fama da ciwon koda a jihar Kano Malam Wali Ado Rano ya ce akwai kalubale da dama da ke tattare da masu dauke da wannan cuta.
Ya ce ana wankin kodar akalla sau biyu a sati wasu ma sau uku sannan kuma akwai allura da ake yi tsakanin naira dubu shida zuwa naira dubu takwas.
Ya kara da cewa masu fama da cutar na shan magani ne na tsawon rayuwarsu sannan maganin ba a Najeriya ake sayarwa ba.
A cewarsa, ''wadanda muka rika yin wankin koda kusan mu 160 a lokacin, kusan ba mu fi mu 10 ba wadanda muka rayu.''
Coronavirus: Shugaban Algeria ya ba da umarnin rufe makarantu a fadin kasar, Daga Ahmed Rouaba BBC News
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune ya bayar da umarnin rufe makarantu a fadin kasar a kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus da ta zama annoba a duniya.
Umarnin ya fara aiki nan take kuma zai ci gaba da aiki har sai 5 ga watan Afrilu, a cewar wata sanarwa da ofishin shugaban ya fitar.
Makarantun da za a rufe sun hada da na firamare da na bayar da horon sana'oi da jami'oi da na Kur'ani.
Matakin ya biyo bayan tabbatar da mutum na farko da ya mutu saboda cutar a kasar. Mutumin mai shekara 67 ya mutu a asibiti a Bilda da ke kudu da birnin Algiers.
A ranar Alhamis ne Algeria ta tabbatar da mutum biyar da suka kamu da coronavirus - a yanzu adadin masu cutar a kasar ya kai 24.
Hukumomin kasar sun kuma ce mutum takwas sun warke daga cutar.
A sakon da ya wallafa a Twitter, shugaban kasar ya bukaci 'yan kasa da ke da niyyar tafiya kasashen da cutar ta bulla da su jinkirta tafiyar domin kare yaduwar cutar.