Ba ni da hannu a cire Sarki Sanusi II – Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai da hannu a tsige Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ne ya wallafa haka a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa duka maganganun da ake yadawa ba gaskiya bane kuma siyasa ce.
Ya bayyana cewa shugaban kasar bai taba katsalandan a cikin harkokin wata jiha a kasar ba sai dai idan hakan ya shafi tsaron kasar baki daya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X






























