An gano maganin hana coronavirus yaduwa

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ra'ayoyin jama'ar Kano kan sauke Sarkin Muhammadu Sanusi II

    Bayanan bidiyo, Yadda wata mata ta ji bayan da aka sauke Sarki Muhammadu Sanusi II
    Bayanan bidiyo, Yadda wasu ke murna da cire Sarki Sanusi
  2. Labarai da dumi-dumi, An fitar da Sarki Sanusi daga Fadar Kano

    Rahotanni daga jihar Kano na cewa jami'an tsaro sun fitar da Sarki Sanusi daga fadar Sarkin Kano

    Sai dai babu wani cikakken bayani dangane da inda aka tafi da shi ko kuma halin da yake ciki

    .
  3. 'Yan daba fiye da 50 sun kutsa Fadar Kano

    Wakilan BBC kusan uku da ke wajen sun tabbatar da cewa sun ga wani baban jami'in gwamnatin Kano ya jagoranci 'yan daba fiye da 50 cikin Fadar Kanon.

  4. Kai tsaye abin da ke faruwa a fadar Kano

  5. Labarai da dumi-dumi, Jami'an tsaro na harba hayaki mai sa hawaye a gidan Sarkin Kano

    Rahotanni daga Fadar Sarkin Kano na bayyana cewa jami'an tsaro na harba hayaki mai sa hawaye a fadar sarkin Kano bayan tsige shi.

    Wakilan BBC sun ce jami'an tsraon sun kutsa har cikin gidan sarkin inda mata suke, sai dai matan sun yi ta mayar da martani da jifa da duwatsu.

  6. Coronavirus: Italiya na cikin mawuyacin hali tun bayan Yakin Duniya na biyu

    Italy Police

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Italiya ta yi alkawarin bayar da karin kudi don shawo kan tabarbarewar tattalin arzikin da ya shafi kasar dalilin annobar coronavirus.

    Kasar na cikin mawuyacin halin da bata taba shiga irinsa ba tun bayan Yakin Duniya na biyu.

    Mutane miliyan 16 ne a arewacin Italiya aka killace kuma suke bukatar izini kafin su yi tafiya wajen kasar.

    Kawo yanzu mutum 366 suka mutu a Italiya kuma ita ce kasar da annobar ta fi shafa bayan China.

  7. Jami'an tsaro sun rufe fadar Sarkin Kano

    Rahotannin da mu ke samu daga jihar kano na cewa jami'an tsaro sun rufe fadar sarkin Kano kuma sun hana shiga da fita.

    Fadar Sarkin Kano
    fadar Sarkin Kano
    Fadar sarkin Kano
    Sarkin Kano
  8. Coronavirus: Mutum 10 sun mutu a ginin otel din da ya rushe

    China Building Collapse

    Asalin hoton, Getty Images

    An tabbatar da mutuwar a kalla mutum 10 sai kuma har yanzu ana neman mutum 23 da gini ya rufto musu a wani otel da aka killace wadanda ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a birnin Quanzhou a China a ranar Asabar.

    Masu ceto ko bayar da agaji na ci gaba da neman wadanda ake nema a baraguzan ginin da ya rushe mai hawa biyar a kudancin lardin Fujian.

    Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai mutum 71 a cikin otel din a lokacin da iftila'in ya faru.

    Babu wasu cikakkun bayanai dangane da abin da ya jawo rugujewar ginin.

  9. Za a nada sabon Sarkin Kano

    Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za ta nada sabon Sarkin kano nan ba da dadewa ba.

    A wata sanarwa mai dauke da sa hannun, Sakataren Gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya yi kira ga jama'ar jihar Kano da su kwantar da hankalinsu kuma su zama masu bin doka yayin da za a fitar da sunan sabon sarkin da zai gaji Muhammadu Sanusi II.

    Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Ganduje ya sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

    Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai Salihu Tanko ya wallafa ta ce majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da a sauke sarkin saboda rashin biyayya.

    Sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce an sauke sarkin Kano ne saboda nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.

    Dama tun da safiyar Litinin Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Kanon kan yunkurin da majalisar ke yi na "ladabtar" da Sarki Muhammadu Sanusi II.

    Bayanan bidiyo, Sanarwar sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi
  11. An nada mace ta farko Birgediya Janar a Guinea

    Shugaban Guinea, Alpha Condé ya nada mace ta farko a matsayin birgadiya janar ta farko.

    An yi wa Mahawa Sylla karin girman ne ran 8 ga watan Maris, wanda ya yi daidai da Ranar Mata ta Duniya.

    A lokacin sanarwar, Shugaba Condé ya yi alkawarin taimakawa wa mata da karfafa masu gwiwa.

    Janar Sylla ta yi karatu a kasar China kuma ta samu shaidar kammala difloma a 2014.

    An nada ta a matsayin mataimakiyar sakatare-janar na Majalisar Tsaron Kasa a shekarar 2017.

    Ta kuma yi aiki da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast.

    Wani mai amfani da shafin Twitter ya wallafa sakon murna fa Janar Sylla.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Rikici ya barke a majalisar Kano kan 'tsige' Sarki Sanusi

    Rahotanni daga jihar Kano na cewa rikici ya barke a zauren majalisar dokokin jihar kan bukatar mataimakin shugaban majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari na son gabatar da rahoton kwamitin bincike kan sarkin Kanon, Sarki Muhammadu Sanusi II.

    Majalisar ta kasu gida biyu- wato da masu goyon bayan jam'iyyar APC wanda kuma sune suke goyon bayan a gabatar da rahoton, da kuma 'yan bangaren jam'iyyar PDP da ke ikirarin cewa rahoton wani yunkuri ne na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na son a tsige sarkin.

    Bangarorin biyu sun tsunduma gardama kan wannan batu kuma bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya, inda har shugaban marasa rinjaye a majalisar, Isyaku Ali Danja ya yi kokarin dauke sandar majalisar.

    Wannan ya sa 'yan majalisar suka shiga kokawa da juna.

    Rahotanni sun nuna cewa an karbe sandar daga hannunsa kuma an fita da ita daga zauren.

    Sarkin Kano

    Asalin hoton, Getty Images

  13. An sa ranar zaben kananan hukumomi a Borno

    Hujumar zabe mai zaman kanta a Borno ta sanar da sanya ranar yin zabukan kananan hukumomin jihar, bayan da Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da hakan.

    Za a yi zabukan na shugabannin kananan hukumomi da kansiloli ne a ranar Asabar 13 ga watan Yunin 2020 a kananan hukumomi 27 na jihar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamann kan yada labari Malam Isah Gusau ya fitar ranar Litinin, ya ce a shirye Gwamna Zulum yake ya bayar da duk wasu kudade da hukumar zaben ke bukata don shirya sahihin zabe.

    Ya kuma ce za gudanar da zaben ne a dukkan kananan hukumomi 27 da mazabun jihar 312, sannan

    Bagabana Zulum

    Asalin hoton, BABAGANA UMARA ZULUM/FACEBOOK

  14. Coronavirus ta kashe mutum na farko a Afirka

    Egypt

    Asalin hoton, AFP

    Wani mai yawon bude ido dan Jamus ya mutu sanadiyyar Coronavirus a Masar.

    Hakan ya sa ya zamo mutum na farko da cutar COVID-19 ta kashe a nahiyar Afirka.

    Mutumin mai shekara 60 ya isa Masar a makon da ya gabata kuma da isarsa ya fara zazzabi.

    An kai shi asibitin Red Sea a wani wurin shakatawa a Hurghada inda ka agano yana dauke da cutar.

    Marigayin ya mutu ne bayan da ya ki yarda a killace shi.

    ranar Asabar ne ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa an samu karin mutum 45 da ke dauke da cutar ciki har da matafiya a cikin wani jirgin ruwan yawon bude ido.

    • Coronavirus: Farashin man fetur ya fadi 'warwas' a kasuwannin duniya
    • An samu mutum na biyu da ya kamu da coronavirus a Najeriya
  15. 'Toshe layukan intanet keta hakkin dan Adam ne'

    Habasha ta toshe hanyoyin intanet a kalla sau takwas tun da Firayim ministan Abiy Ahmed ya hau mulki a shekarar 2018.

    An rufe intanet a kasar a lokacin zanga-zanga da lokacin da daliban makarantar sakandire ke zana jarabawa.

    Kusa tsawon wata biyu kenan da aka rufe hanyoyin intanet din a yammacin yankin Oromia, yanki mafi girma a kasar.

    A wasu wuraren, an yanke layukan wayar salula.

    A bara ne wani babban jami'in gwamnati ya shaida wa BBC cewa an yi hakan ne don kokarin shawo kan matsalar tsaro da sojoji ke yi.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, kungiyar sa ido kan hakkin dan Adam, Human Rights Watch ta ce toshe hanyoyin waya da intanet ya keta hakkokin dan Adam kuma ya kamata a gyara.

  16. An samu mutum na biyu da coronavirus a Najeriya

    Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter a ranar Litinin da misalin karfe 10.30 na safe.

    NCDC ta ambato minsitan lafiya na kasar yana mai tabbatar da samun mutum na biyu mai dauke da cutar ta Covid19 a kasar.

    An gano mai dauke da cutar ne a jihar Ogun cikin mutanen da aka kebance tun tuni, "kuma an gano cutar a jikinsa ne a kokarin da muke na gano duk wadanda suka yi alaka da mai dauke da cutar na farko dan kasar italiya."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. An kai wa Firayim ministan Sudan hari da bom

    Firayim ministan Sudan Abdullah Hamdok ya tsallake rijiya da baya, a lokacin da aka yi yunkurin kashe shi a Khartoum, babban birnin kasar.

    Gidan talabijin na kasar da wata majiya a gwamnatin Sudan sun ce an kai wa jerin gwanon motocin Firayi Ministan hari.

    Babban mai taimaka wa Mista Hamdok, Ali Bakhit ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Wani abun fashewa aka jefa wa motar da Firayim Ministan ke ciki amma mun gode wa Allah babu wanda ya samu rauni."

    Rahotanni sun ce Mista Hamdok ba samu rauni ba kumaa halin yanzu an killace shi wani wuri mai tsaro.

    Abdallah Hamdok

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Abdallah Hamdok ya zama Farayim minista a watan Agustan bara
  18. Wasu hare-hare 'yan aware sun kashe jami'an tsaro a Kamaru

    Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da kisan da aka yi wa wasu mutane 8 sojoji da ’yan sanda da fararen hula a wasu hare-hare biyu da aka kai a birnin Galim na yammacin kasa da Bamenda a yankin renon Ingila.

    A wata sanarwar da Kakakin Gwamnati Minista Rene Emmanuel Sadi ya sa hannu a kai, ya yi Allah wadai da wadannan hare-haren da tuni ya dora alhakinsu a kan masu fafutuka na yankin renon Ingila masu yunkurin kafa kasar Ambazoniya.

    Harin na birnin Bamenda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da bikin ranar mata, a lokacin da jama’a suka hallara a titin “Commercial Avenue” kuma Gwamna Lele Lafrique na yin jawabi.

    Wasu abubuwan fashewa da aka tayar da su daga nesa sun tarwatse kimanin mita 100 da inda ake gudanar da bikin.

    Hakan ya yi sanadiyyar mutuwar soja guda yayin da mutane 7- sojoji 4, ‘yan sanda 2 da farar hula 1 suka ji rauni.

    A harin birnin Galim kuma, Gwamnati ta ce masu fafutuka na yankin renon ingila, a kan babura da aka kiyasta yawansu sama da 20 sun yi kutse a cikin dare, inda suka nufi sansanin ‘yan sanda da na Jandarma suka kai farmaki a lokaci guda.

    Hakan ya sa aka yi ta yin musayar harbe-harbe tsakanin bangarorin biyu har na tsawon sa’a guda da rabi.

    A wannan karon kuma, Jami’an tsaro na Jandarma 2 dukkansu mata ne suka mutu, hadi da wasu ‘yan sanda biyu da wasu fararen hula. Har ila yau kuma akwai wasu da suka ji rauni.

  19. 'Yan bindiga sun kai hari sansanin soji a Nijar

    Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari wani sansanin sojoji a arewa maso gabashin Nijar ranar Lahadi.

    Harin ya raunata sojoji da dama kuma irinsa ne na farko cikin makonni.

    Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa mayakan dauke da manyan makamai, sun shiga sansanin da ke kauyen Chetima Wangou a yankin Diffa ne cikin motoci.

    A shekaru biyar da suka gabata, Boko Haram ta sha kai hari yankin.

    Sojin Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Shugaba ya killace kansa saboda coronavirus

    Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa

    Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa na Portugal ya dakatar da ayyukansa na gwamnati har na tsawon mako biyu a matsayin rigakafi ga cutar coronavirus.

    An ba shi shawarar ya killace kansa a gida domin a kula da lafiyarsa bayan wata tawagar daliban makaranta ta ziyarci fadarsa ranar Talata, inda daga baya aka gano daya daga cikin daliban ya harbu da cutar coronavirus.

    Yaron dai ba zai iya tattance sauran daliban da suka kai wa shugaban ziyara fadarsa ba. Yanzu an rufe makarantar da ke arewacin Portugal.

    Shugaban na Portugal wanda za a iya cewa shi ne shugaba na farko a nahiyar Turai da ya killace kansa, bai nuna alamun cutar ba.