An gano maganin hana coronavirus yaduwa

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Yadda kasashen Afirka ke kara matsa kaimi kan coronavirus

    Hukumar Lafiya ta Duniya a jiya ta ayyana cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus a matsayin annobar duniya.

    Shugaban hukumar, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a tsakanin kasashen da ba China na ya ninka har sau 13 cikin mako 2.

    Ga yadda wasu kasashen duniya ke daukar wasu matakai don hana yaduwar cutar:

    • Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ta killace mutum 109, wadanda ake tunanin sun yi mu'amala da mutum na farko da ya kamu da cutar covid-19.
    • Afirka ta Kudu ta tabbatar da karuwar mutum 6 da suka kamu da cutar a jiya Laraba. Kawo yanzu, mutum 13 ne ke dauke da cutar a kasar.
    • Makwabciyarta Botswana kuwa, ta ba da tabbacin cewa ba ta rufe iyakarta da Afirka ta Kudun ba kuma ba za ta rufe ba. Kusan 'yan Afirka ta Kudu 100 ne a birnin Wuhan na China ake sa rai za su dawo kasarsu gobe Juma'a.
    • Burkina Faso, wacce take da mutane biyu masu dauke da cutar, ta haramta duk wani taron jama'a, yayin da makwabciyarta Nijar ta dakatar da duka tarukan kasa da kasa da aka sa lokaci za a yi a Yamai, babban birnin kasar.
    • Uganda ta tsaurara dokokinta na tafiye-tafiye zuwa kasashe 9 ciki har da Burtaniya da Amurka kuma za ta fesa wa mutane magungunan kashe kwayoyin cuta a lokacin da suka iso kasar.
    • Ma'aikatar lafiya a Eritrea ta bukaci matafiya masu shiga da fita kasar su soke shirye-shiryensu "don kansu" saboda barkewar cutar covid-19 a fadin duniya.
    • A Mauritius, ma'aikatar lafiya ta tabbatar wa al'umar kasar cewa tana da isassun magunguna ko da cutar ta barke a kasar.
    • Gwamnatin tsibirin Seychelles ta sanar da cewa ta rufe tsibirin ga jiragen ruwan yawon bude ido.
    • Jaridar New Times mai goyon bayan gwamnatin Rwanda ta ruwaito cewa, kasar na neman wata hanyar shigo da kayayyaki yayin da wasu kasashen Afirka ke kokawa kan karewar da wasu kayan China suka yi saboda annobar.
  2. Trump ya haramta wa 'yan kasashen Turai shiga Amurka

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramta wa kasasshen Turai shiga kasar na kwanaki 30 a wani kokari na hana yada cutar Coronavirus.

    Mista Trump ya ce kungiyar kasashen Turai ba ta dauki matakan da suka dace ba cikin gaggawa, don hana yaduwar cutar, da haramta shiga kasashensu daga China kamar yadda Amurka tayi.

    Ya ce kasarsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wurin daukar matakai da za su kare rayuwa da lafiyar Amurkawa.

    Shugaban ya kuma bukaci majalisa ta amince da tsare-tsare yakar wannan annoba a cikin gaggawa.

    Kwararru a fadin duniya dai na ganin wannan mataki na Donald Trump na iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya baki daya.

  3. Yau ce Ranar Koda ta Duniya

    World Kidney Day

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau ce ranar tunawa da cutar koda ta duniya, wadda aka kebe domin fadakar da al’umma da yunkurin rage yawan masu kamuwa da cutar da sauran dangoginta a fadin duniya.

    Akan tuna da ranar ce duk Alhamis ta biyu na watan Maris shekara.

    A Najeriya wani rahoton kungiyar masu kula da lalurar Koda ya ce ‘yan kasar miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ciwo, abin da kan sa kodar ba ta aiki yadda ya kamata har sai an rika zuwa wanki.

    Kididdigar da kungiyar ta fitar ta nuna cewa akasarin masu fama da cutar matasa ne.

    Likitoci sun ce cutar ta fi kama masu fama da cutuka kamar hawan jini da ciwon suga da kuma masu yawan shan magungunan gargajiya.

  4. Marabanku!

    Barkanku da sake kasancewa da mu a wannan shafi, inda muke sanar da ku wainar da ake toyawa a Najeriya da makwabtanta kamar Nijar da Ghana da Chadi da Kamaru da ma wasu kasashen duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu a yau Alhamis domin sanin abubuwan da ke faruwa a duniyar.

  5. Sai da safenku

    Karshen rahotannin kai-tsaye kenan.

    Fauziyya Kabir da Nabeela Muktar Uba da Mustafa Musa Kaita da Umar Mikail ne suka yi ta dawainiya da shafin tun safe.

    Mu hadu da ku gobe Alhamis a wannan shafi domin ci gaba da sanin abin da duniya ke ciki.

  6. 'Aminu Ado Bayero ne sabon Shugaban Majalisar Sarakunan Kano'

    .

    Asalin hoton, AMINU ADO BAYERO/INSTAGRAM

    A yayin taron mika takardar aiki ga sababbin sarakunan Kano da na Bichi, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kano.

    A halin yanzu Mai Martaba Aminu Ado bayero ne zai rinka jagorancin taron majalisar sarakuna ta jihar Kano inda ake sa ran sarakunan Gaya da Karaye da Bichi da kuma Rano za su rinka halarta.

  7. Duka jama'ar Kano na cikin farin ciki a yau – Ganduje

    .

    Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

    Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce yau rana ce ta tarihi kuma ta farin ciki a Kano.

    Ya bayyana haka ne a yayin bikin mika takardar kama aiki ga sababbin sarakuna a jihar Kano.

    Gwamnan ya bayyana cewa yana cikin jin dadi a wannan rana kuma jama'ar Kano gaba dayansu suna cikin farin ciki.

  8. Kai -tsaye daga Facebook: Taron mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kano

  9. Tuni aka mika wa Sarki takardar kama aiki

    Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi takardar kama aiki daga Gwamna Abdullahi Ganduje.

  10. Sarkin Kano ya taso don karbar takardar aiki

    Sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taso domin karbar takardar aiki daga Gwamna Ganduje.

    Tuni aka mika wa Sarkin Bichi tasa takardar.

  11. Ana ta yi wa Sarkin Bichi mubaya'a

    Masu sarauta daga Masarautar Bichi na ci gaba da kai wa sarki gaisuwa tare da yin mubaya'a gare shi.

  12. An bai wa Sarkin Bichi takardar kama aiki

    Gwamna Abdullahi Ganduje ya bai wa Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero takardar kama aiki.

    Hakan yana nufin Nasiru Ado Bayero ya zama sarki na biyu a sabuwar Masarautar Bichi bayan dan uwansa Aminu Ado, wanda ya zama Sarkin Kano.

  13. Sarakuna 'yan uwan juna

    Kar a manta cewa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da kuma na Bichi wato Alhaji Nasiru Ado Bayero 'ya'yan Marigayi Sarki Ado Bayero ne, wanda ya shafe sama da shekara 50 a kan karagar Sarautar Kano.

  14. Sakataren Gwamantin Kano na jawabi

    Yanzu haka Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ne Alhaji Usman Alhaji yake jawabi.

  15. Har da Sarkin Bichi ake bai wa takardar kama aiki

    Yayin taron, za kuma a bai wa Nasiru Ado Bayero takardar kama aiki a mastayin sabon Sarkin Bichi.

    Ana iya ganin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da Sarki Aminu Ado Bayero (a damansa ) da kuma Mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ( a hagunsa), sai kuma Sarlkin Bichi daga gefen mataimakin gwamna.

  16. Kai-tsaye daga Facebook: Taron mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kano

    Muna kawo maku taron bai wa sabon sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero takardar kama aiki kai-tsaye a Facebook.

    Ana iya ganin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da Sarki Aminu Ado Bayero (a damansa ) da kuma Mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ( a hagunsa), sai kuma Sarlkin Bichi daga gefen mataimakin gwamna.

  17. Hotunan gidan da Muhammadu Sanusi yake a garin Awe

    Hotunan gidan da Muhammadu Sanusi yake a garin Awe
    Hotunan gidan da Muhammadu Sanusi yake a garin Awe
    Hotunan gidan da Muhammadu Sanusi yake a garin Awe
  18. Coronavirus: Mutum 63 sun mutu a kwana guda a Iran

    Ma'aikatar lafiya a Iran ta tabbatar da mutuwar mutane 63 masu dauke da cutar Covid-19 a cikin kwana guda- mutane mafi yawa da suka mutu a kwana guda a kasar.

    Wani kakakin ma'aikatar, Kianoush Jahanpour ya ce ce kawo yanzu mutum 354 ne suka mutu tun da annobar cutar ta barke a cikin watan jiya.

    Mista Jahanpour ya kara da cewa an tabbatar da mutane 958 sun kamu da cutar ta coronavirus, inda yanzu gaba daya mutanen da ke dauke da cutar a kasar yawansu ya kai 9,000.

  19. Nijar: Ana zargin tafka almundahana a ma'aikatar tsaro

    A jamhuriyar Nijar hadin gwiwar kungiyoyin fararen hular kasar na ci gaba da matsa wa hukumomi lamba kan su dauki mataki game da jami’an da ake zargi da cin hanci da rashawa a ma’aikatar tsaro.

    Wani bincike da kwamitin gwamnati ta yi, ya gano an yi almundahana da makudan kudade a ma’aikatar ta tsaro a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fama da matsalar tsaro musamman ayyukan masu tayar da kayar baya wadanda ke da nasaba da kungiyoyin Boko Haram da Al-Qaeda da IS.

    Sun yi kira ga jama’ar kasar baki daya su fito ranar 15 ga wannan watan su yi gagarumin gangami da fatan kara matsa wa hukumomi lamba su gurfanar da jami’an da ake zargi a gaban kuliya.

    Mahamadou Issoufou

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Labarai da dumi-dumi, El-Rufai ya bai wa Sanusi mukami a Jami'ar Kaduna

    .

    Asalin hoton, Muhd Photography

    Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bai wa Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukamin Uban Jami'ar jihar Kaduna.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a shafin Twitter na gwamnatin jihar Kaduna inda ya ce tsohon sarkin zai kawo ci gaba a jami'ar jihar.

    Ko a ranar Talata sai da gwamnan Kadunan ya bai wa tsohon sarkin mukami a hukumar bunkasa zuba jari ta jihar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X