Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Bidiyon Tambuwal a yayin da yake jefa kuri'arsa

    Bayanan bidiyo, Tambuwal 9/3/2019
  2. Za a fara kidaya kuri'u a Benue

    Ana shirye-shiryen fara kidaya kuri'u a rumfar zaben gidan gwamnatin jihar Benue.

    A
  3. Atiku Abubakar ya kada kuri'a

    Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a garin Yola na jihar Adamawa ranar Asabar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. An fara kidaya kuri'u a Kano

    An fara kidaya kuri'u a wata mazabar da ke unguwar Shagari Quarters a jihar Kano, kamar yadda wakilinmu Mansur Abubakar ya tabbatar mana.

    Kano
  5. Abba Kabir Yusuf ya kada kuri'arsa

    Dan takarar jam'iyyar PDP a Kano Abba Kabir Yusuf ya kada kuri'arsa a Kano.

    Bayanan bidiyo, Dan takarar jam'iyyar PDP Abba K Tukur
  6. Ba kasuwa ga masu talla a rumfunan zabe a Abuja

    Zaben shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya na 23 na shugaban kasa ya sha bamban da na gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi da ake yi a halin yanzu.

    A wannan karon an samu karancin fitowar jama'a a birnin tarayyar Najeriya Abuja inda ake zaben kananan hukumomi.

    Masu sana'o'i daban-daban na kokawa kan yadda suka fito da kayan talla amma ba kasuwa.

    BBC
  7. Rumfar zabe a fadar shugaban kasa

    An samu karancin fitowar mutane a rumfunan zabe a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

    VILLA
    VILLA
  8. Wani mai bukata ta musamman a rumfar zabe

    Wani mai bukata ta musamman kenan mai suna Atsen Azi a rumfar zaben Zarazo da ke karamar Hukumar Jos ta Gabas.

    Atsen Azi
    Bayanan hoto, Atsen Azi
  9. Yadda ake cinikin gurasa a rumfar zabe

    Bidiyon yadda mai sayar da gurasa ke sana'arsa a wata rumfar zabe a Kano.

    Bayanan bidiyo, Gurasa 9/3/2019
  10. Tambuwal ya kada kuri'arsa

    BBC
  11. Mata na sassaka a Gezawa a jihar Kano

    Bayanan bidiyo, Mata na sassaka a Gezawa 9/3/2019
  12. Masallatai na kira a fito zabe a Jos

    Masallatai a Dogon karfe da ke Jos sun yi amfani da lasifikarsu domin kiran mutane a fito a kada kuri'a.

    Sun yi hakan ne sakamakon karancin fitowar mutanen da aka samu a ranar zabe.

    Rahotanni dai sun bayyana cewa bayan kiran da masallatan suka yi, jama'a da dama sun yiu tururuwa domin zuwa rumfunan zabe su kada kuri'arsu.

    BBC
    Bayanan sautiMasallacin Jos 9/3/2019
  13. Yadda wasu ke hidimarsu a ranar zabe a Legas

    Bayanan bidiyo, Yadda wasu ke hidimarsu a ranar zabe a Legas 9/3/2019
  14. Saraki ya kada kuri'arsa

    Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya kada kuri'arsa a rumfar zabe mai lamba 005/006 da ke Agbaji a karamar hukumar Ilorin ta yamma a jihar.

  15. Bola Tinubu ya kada kuri'a

    Tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyyar APC Bola Tinubu ya kada kuri'a.

    Zaben Nigeria
  16. Wamakko ya kada kuri'arsa

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma jigo a jam'iyyar APC Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kenan a lokacin da ya ke kada kuri'arsa.

    BBC
  17. Yadda Sanwo-Olu ya kada kuri'arsa

    Dan takarar gwamna a jihar Legas na jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu a lokacin da yake kada kuri'arsa.

    Zaben Nigeria
  18. Jonathan da Patience sun kada kuri'unsu

    Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da matarsa Patience sun kada kuri'a a mazabar Otuoke da ke jihar Bayelsa.

    Zaben Nigeria
  19. Bidiyon yadda EFCC ta kama makudan kudade a jihar Benue

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Bidiyon yadda Buhari ya kada kuri'arsa

    Shugaban Najeriya kenan Muhammadu Buhari a yayin da yake kada kur'arsa a mazabarsa da ke Kofar Baru a Daura