Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. EFCC na duba kayayyakin zabe

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Jami'an hukumar EFCC a Najeriya kenan ke duba kayayyakin zabe a filin jirgin sama dake Maiduguri a jihar Borno a yunkurin da suke yi na yaki da sayan kuri'a a zaben da za a gudanar a ranar Asabar.

  2. Kayan zabe a mazabar Jos Jarawa dake jihar Filato

    Kayayyakin zabe suna ta isa a mazabu dake fadin Najeriya. Yanzu haka wadannan wasu daga cikin kayayyakin zabe ne da ke mazabar Jos Jarawa dake jihar Filato.

    BBC
    BBC
  3. Daurin shekaru biyu ga barawon kayan zabe- INEC

    Hukumar INEC ce ta wallafa a shafinta na Twitter domin tuni a kan cewa duk wanda aka kama ya saci kayan zabe zai fuskanci shari'a inda ake sa ran zai sha dauri na shekaru biyu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Ra'ayoyi daga shafin Facebook

  5. 'Yan sanda sun musanta zargin musguna wa 'yan adawa

    BBC

    Rundanar ’yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta musanta zargin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi cewa jami’anta na musguna wa ’yan adawa a jihar gabanin zaben gwamna da na ’yan majalisar jiha. Kwamishinan ’yansanda na jihar, Ali Janga, ya shaida wa wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar dake Bauchi cewa zargin ba gaskiya ba ne. Tun farko dan takarar gwamna na jam’iyyar ta PDP, Sanata Bala Muhammad Kaura ya shaida wa BBC cewa jami’an tsaro da hadin bakin gwamnatin APC a jihar, sun kama magoya bayan ’yan adawa fiye da 300 da nufin gallaza masu. To amma kwamishinan ’yan sandan ya ce mutanen da yan sanda suka kama ba su kai 300 ba. ’Mun kama mutane fiye da 100 ne’ inji shi. Ya kara da cewa wadanda aka kama ba magoya bayan PDP ba ne kadai, sun hada da na wasu jam’iyyun ciki har da APC da kuma ’yan Sara-suka. Ana zarginsu ne da laifuka da suka shafi keta doka da yunkurin tayar da zaune tsaye.

  6. Jihar Benue

    Yadda wasu mazauna jihar Benue ke fatan yin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki lafiya da za a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris.

    Bayanan bidiyo, Zaben gwamnoni: fatan masu zabe daga jihar Benuwe
  7. An bai wa masu yi wa kasa hidima horo a jihar Ogun

    Yadda aka yi wa 'yan horon kasa bita kan zaben gwamna da za a gudanar a jihar Ogun da na 'yan majalissar dokoki.

    An kuma ba su bitar kan yadda ya kamata su gudanar da aikinsu, an kuma bukaci da su kaucewa duk wasu abubuwan da za su jawo hayaniya.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Inec

  8. Yadda 'yan siyasa ke raba kayan masarufi ran jajiberin zaben gwamna

    Wakilan BBC da ke sassa daban-daban a Najeriya sun shaida mana cewa sun ga yadda 'yan siyasa ke ta faman raba kayayyakin masarufi ga masu kada kuri'a gabanin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki da za a yi gobe Asabar.

    A jihar Kwara an ga yadda ake raba wa mutane kananzir da taliya da sikari.

    A Legas kuma an fi raba shinkafa ne mai dauke da hoton 'yan takara.

    Kananzir zabe
    Kazanzir zabe
    Bayanan hoto, A jihar Kwara kuwa mutane sun buga layin don karbar kananzir
    shinkafa zabe

    Asalin hoton, b

    Bayanan hoto, Wannan shinkafar mai hoton dan takarar gwamna na APC Sanwolu a Legas ake rabonta
  9. Yadda ake tantance kayayyakin zabe a Benue

    Yadda ake tantance kayayyakin zabe kenan a ofishin hukumar zabe da ke Makurdin jihar Benue gabannin zaben gwamna a ranar Asabar

    Bayanan bidiyo, Rarraba kayan zabe a Najeriya
  10. Labarai da dumi-dumi, Wani Ofishin hukumar zabe a Akwa Ibom ya kone

    Ofishin hukumar zabe na karamar hukumar Ibesikpo Asutan da ke jihar Akwa Ibom ya kone, kuma kawo yanzu ba a san musabbabin gobarar ba.

    Jami'in zabe na jihar Mike Igini ya ziyarci ofishin domin ganin barnar da gobarar ta yi.

    Ana ta cin karo da kalubale a jihar Akwa Ibom musamman a zaben gwamna da Udom Emmanuel na PDP ke son yin tazarce.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Cletus Ukpong

    zaben Nigeria

    Asalin hoton, Cletus Ukpong

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Cletus Ukpong

    Zaben Najeria

    Asalin hoton, Cletus Ukpong

  11. Za ku iya bibiyar shirin a shafukan BBC Yoruba da Igbo da kuma Pidgin

  12. Jihar Benue

    Dogon layi a sakatariyar APC a Makurdi, jihar Benue inda mutane ke karbar sukari da taliya da sauran kayayyakin amfanin gida.

    Tun a ranar Alhamis aka fara raba kayayyakin.

    Zaben Nigeria
  13. Jihar Cross River

    Hukumar zabe ta jihar Cross Rivers ta ce ta kammala shirin fara zaben gwamna da na 'yan majalissar dokoki a jihar da za a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris.

    'Yan takara 25 ke neman kujerar gwamnan, yayin da 'yan takara 265 ke neman kujerun majalissar dokokin jihar.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Inec