Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. An kama wata mota makare da kudi a Sokoto

    An kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto.

    Hukumar yaki da cin hanci da zagon kasa tare da jami'an tsaro ne suka kama mota kirar Jeep makare da kudi da ake zargin za a yi amfani da su ne wajen sayen kuri'u a jihar Sokoto.

    An kama motar mai lamba ABC 924 LU a kan titin Garba Duba da ke Sokoto a daren Juma'a da karfe 10:30 inda aka kai motar hedikwatar 'yan sanda a jihar Sokoto.

    Daga nan ne aka fito da buhunhunan kudi domin yin bincike. An yi ta kokarin jin ta bakin kakakin 'yan nda kan lamarin, yayin da jami'an tsaron suka hana daukar hotunan kudin.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Za ku iya tuntubar sashen Yoruba da Igbo da Pidgin

    Muna shaida muku cewa takwarorinmu na Sashen Igbo da Yoruba da kuma Pidgin su ma suna kawo labarai da rahotanni da dumi dumi kan zaben gwamnonin Najeriya.

    Sai ku garzaya shafukansu na intanet bbcnews.com/yoruba da bbcnews.com/igbo da kuma bbcnews.com/pidgin don karin bayani.

    Kazalika suna sabunta shafukansu na sada zumunta a Facebook da Instagram da Twitter a @bbcnewsigbo, @bbcnewsyoruba da kuma @bbcnewspidgin.

  3. Jihar Gombe mazabar doma

    An kammala kai kayan aiki a mazabar Doma da ke jihar Gombe domin gudanar da zaben gwamna da na majalisar dokoki.

    Zaben Nigeria
    Zaben Nigeria
    Zaben Nigeria
  4. Muna gabatar da labarai kai tsaye a BBC Hausa Facebook

  5. Jihar Yobe ta shirya gudanar da zabe

    Yankin arewa maso gabashin Nijeriya a jihar Yobe, hukumomi ke cewa sun kammala shiri domin zaben na gwamna da na 'yan majalisar dokokin jihar a yau.

    Yobe dai na daya daga cikin jihohin da suka fuskanci hare-haren kungiyar Boko Haram, wayewar garin ranar zaben shugaban kasa mako biyu da suka gabata. Ko da yake, hakan bai hana gudanar da zabuka na ranar 23 ga watan Fabrairu ba.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki

    Nan da d'an lokaci ne za a sake bude rumfunan kada kuri'u a Nijeriya, don zabukan gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi.

    Za a gudanar da zaben gwamna a cikin jwasu daga ihohin Najeroiya ne, da kuma zaben 'yan majalisar dokoki a daukacin jihohi 36 na kasar, sannan da zaben kananan hukumomi na babban birnin tarayya Abuja.

  7. Zaben da za a yi a Abuja

    A babban birnin tarayyar Najeria Abuja, zaben shugaban karamar hukuma da na kansiloli za a yi.

    Saboda haka ne hukumar zabe ta tanadi akwatuna biyu da suka hada da mai murfi launin ja shi ne na shugaban karamar hukuma da mai launin baki shi ne na kansiloli.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Inec

  8. 'Yan takara 33 ne ke neman kujerar gwamnan Benue

    'Yan takarar kujerar gwamna a jihar Benue su 33 ne daga jam'iyu 33, yayin da wadan da ke takarar majalisar dokokin jihar su 432 ne.

    Kwamishinan zabe na jihar Binuwai Dokta Nentawe Yil-wada ya ce sun kammala shirin yadda za su yi amfani da motoci 5,102 don kai jami'an zabe su 22,000

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Inec

  9. Takarar majalisar dokokin jihar Gombe

    'Yan takaran kujerar majalisar jihar Gombe su 253 ne a kujera 24 da ake da ita, kuma yawancin 'yan takarar matasa ne har da mata 18 da suke son a zabe su zuwa majalisar dokokin jihar.

    Inec

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Wasu 'yan takarar gwamna a Gombe sun hade waje daya

    Hukumar zabe a Jihar Gombe tace yan takaran Gwamna 32 ne a jihar. Amma a yanzu hudu ne kawai zasu yi takara.

    Dalilin shi ne, yan takara 19 daga wasu jam'iyu sun ce suna goyon bayan Dan takaran APC, Alhaji Inuwa Yahaya, haka kuma jam'iyu 28 da dama can ba su da 'yan takara a Jihar Gombe, suma sun ce suna goyon bayan Alhaji Inuwa.

    Haka nan kuma 'yan takarar Gwamna a Jihar Gombe guda 15 sun ce suna goyon bayan Dan takaran Gwamna na PDP, Senata Usman Bayero Nafada. Hakanan kuma jam'iyun da basu da yantakara 39 sun ce suma suna bayan Senata Bayero.

    Yanzu dai jam'iyu hudu kawai keda 'yan takara, watau APC, PDP, PRP DA ABP. Haka nan kuma. Dan takaran PRP, Abdulganiy Bello da dan takaran ABP, Nehemiah Gado, sun ce sukam ba su janye daga neman zama Gwamna a Jihar Gombe ba.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Akwatunan zaben gwamna da na majalisar dokoki

    Da ya ke zabe biyu za a gudanar a jihohin Najeriya da ya hada da na gwamnoni da na majalisar dokoki, hukumar zabe ta tanadi akwatuna biyu.

    Daya yana da murfi launin ja shi ne wanda za a yi zaben gwamna, shi kuwa mai murfi launin baki shi ne na majalisar dokoki

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Inec

  12. Macen da ta fara bin layin zabe a karamar hukumar Jos

    Malama Hajara Sani mace mai kamar maza,da ta hau layin zabe tun karfe hudun dare a karamar hukumar Jos ta jihar Plateau..

    Zaben Nigeria
  13. Wasu tun da asuba suka bi layin zabe a Jos

    Sulaiman Muhammad tare da wasu masu kada kuri'a da suka hau layin zabe run karfe biyun dare a mazabar Jos Jarawa da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa.

    Zaben Najeriya
  14. Sojoji na binciken wasu bidiyo da ke yawo a Rivers

    Rudanar Sojin Najeriya ta ce tana binceken wasu bidiyo da ake watsa wa a kafar sada zumunta da ke nuna wasu sojoji da jami'an tsaro suna shiga gidan wasu 'yan siyasa a jihar Rivers.

    Rundunar ta sanar a shafinta na sada zumunta na tuwita cewar ba ta marawa wani dan siyasa baya.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Wannan daya daga bidiyon da ake yawa a jihar Rivers.

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  15. Barkanku da safiya

    Jama'a barkanmu da saduwa cikin shirin kai tsaye kan zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohin Najeriya da za a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris.

    Nine Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar muku da kashin farko na shirin.

    Za ku iya bayyana ra'ayinku a BBCHausa Facebook ko ta Tuwita ko ta Instagram a BBC Hausa.

    Mau'du'in mu shi ne #BBCNigeria2019, #NigeriaDecides2019

  16. Sai gobenku, Ku kasance da mu gobe

    A nan muka kawo karshen kawo maku bayanai da rahotanni kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

    Ku kasance da mu gobe inda za mu kawo maku bayanai da rahotanni da sharhi musamman a kan yadda ake gudanar da zaben a Najeriya. Sunana Mustapha Musa Kaita

    BBC
  17. Yadda 'yan sanda ke shirye-shiryen zabe a Kano

    Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano kenan Muhammad Wakili ke bayyana shirye-shiryen da suke gudanarwa gabannin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a ranar Asabar.

    Bayanan bidiyo, Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano
  18. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  19. Na'urar Card Reader 198 sun kone a Akwa Ibom

    Hukumar INEC a Najeriya ta ce a yanzu haka tana bincike a kan gobarar da ta afku a ofishiinta da ke karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar Akwa Ibom.

    Hukumar ta ce na'urar card 198 ne da kuma janareto 13 suka kone da wasu muhimman kayayyakin zabe suka kone a lokacin gobarar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Yadda ake sayayyar kayayyaki a kasuwar Muda Lawan dake Bauchi

    Bauchi
    Bauchi