APC ta lashe sakamakon zaben kujerun majalisa 21 a Kogi
Hukumar INEC ta bayyana sakamakon kujerun 'yan majalisa 21 cikin 25 na jihar Kogi inda jam'iyyar APC ta lashe kujeru 21 sai kuma kananan hukumomi uku ba a kammala ba.
Kananan hukumomin da ba a kammala ba sun hada da Lokoja 1 da Igalamela-Odolu da Omala. A yanzu haka ana tattara sakamakon karamar hukumar Mopamuro wace ita ce ta rage.








