Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. An fara karbar sakamako a jihar Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    An soma karbar sakamako. Karamar hukuma ta farko ita ce Bogoro.

    A jawabinsa gabanin soma karbar sakamako, Kwamishinan hukumar zabe a jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bukaci wadanda suka samu nasara da wadanda suka fadi da magoya bayansu da su nuna sanin ya kamata kuma su kiyaye doka bayan bayyana sakamakon. ‘Masu nasara su nuna karimci, wadan da suka fadi su nuna juriya”, in ji shi.

    Ya kara da cewa a ganinsu wannan zabe na daga cikin wadan da aka fi samun nasara da kwanciyar hankali wajen gudanar da shi.

    Zaben Nigeria
  2. Isa ya sha kaye a Makarfi

    Dan takarar PDP a jihar Kaduna Isa Ashiru ya sha kaye a karamar hukumar Makarfi inda ya samu kuri'u 22,301 shi kuwa da takarar APC Nasir El-Rufai ya samu kuri'u 34,956.

    Wadan da aka yi wa rijistar zabe 104,458, yayin da wadan da aka tantance sune 58,774.

  3. El-rufai ya sha kaye a Kaura

    Dan takarar PDP a jihar Kaduna Isa Ashiru ya lashe karamar hukumar Kaura inda ya samu kuri'u 38764 sai kuma dan takarar APC Nasir El-Rufai ya samu kuri'u 8342.

  4. An bude zauren tattara sakamakon zabe a Bauchi

    Yanzu aka bude zauren tattara sakamako a ofishin INEC dake jihar Bauchi domin fara karbar sakamako daga jami’an zabe na kananan hukumomi

    Zaben Nigeria
    Zaben Nigeria
    Zaben Nigeria
  5. Ba a bude zauren tattara sakamako a Bauchi ba

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Jami’an zabe na wasu kananan hukumomi sun fara isowa ofishin hukumat zabe ta INEC dake Bauchi domin mika sakamakon zabe na yankunansu.

    Amma har yanzu ba a bude zauren tattara sakamakon ba, bare a soma aikin tattarawar.

    Zaben Nigeria
    Zaben Nigeria
    Zaben Nigeria
  6. Abba ya fadi a Kunchi

    Dan takarar APC Abdullahi Umar Ganduje ya lashe karamar hukumar Kunchi a jihar Kano inda ya samu kuri'u 16157 sai kuma Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 13171.

  7. Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Kano

    An fara tattara sakamakon zaben gwaman jihar Kano. Za ku iya garzayawa shafinmu na Facebook, idan kuka latsa nan.

  8. Bindow ya sha kaye a Jada

    Dan takarar gwama a jihar Adamawa karkashin jam'iyyar PDP Umar Ahmadu ya lashe garin Jada da kuri'u 20076 sai kuma dan takarar APC Mohammed Umar Jibrilla ya samu kuri'u 18006.

  9. Tambuwal ya sha kaye a garin Sardauna

    Dan takarar APC a jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya lashe karamar hukumar Rabah a jihar da kuri'u 16,535 inda dan takarar PDP Aminu Waziri Tambuwal ya samu kuri'u 13,232.

  10. PDP ta lashe karamar hukumar Bebeji a Kano

    Jam'iyyar PDP a Kano ta lashe karamar hukumar Bebeji inda ta samu kuri'u 18533 sai kuma jam'iyyar APC ta samu kuri'u 17418.

  11. APC ta lashe karamar hukumar Makoda a Kano

    Dan takarar APC a Kano Abdullahi Umar Ganduje ya lashe karamar hukumar Makoda inda ya samu kuri'u 22788 sai kuma dan takarar PDP a jihar Abba Kabir Yusuf ya samu kuri'u 9253.

  12. APC ta ci karamar hukumar Madobi a Kano

    Jam'iyyar APC ta lashe karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano inda APC ta samu kuri'u 24491 sai kuma PDP ta samu kuri'u 24309.

  13. Har yanzu ba a fara tattara sakamako ba a Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Har yanzu ba a bude zauren tattara sakamako ba a ofishin hukumar zabe ta INEC dake Bauchi. Manema labarai na zaman jira.

    BBC
  14. An fara tattara sakamakon zaben jihar Kano

    An fara tattara sakamakon zaben gwaman jihar Kano. Za ku iya garzayawa shafinmu na Facebook, idan kuka latsa nan.

  15. Duba samakon zabe a wuri guda!

    Me kuke son sani game da sakamakon zabe? Domin samun sakamako kai-tseye da zarar INEC ta bayyana ku ci gaba da kasance da mu.

    BBC

    Asalin hoton, BBc

  16. Me yasa har yanzu jihohin arewacin Najeriya basu fara fitar da sakamako ba?

    A yayin da jihohin kudancin Najeriya tuni suka fara tattara sakamakon zabe da kuma bayyanawa, har yanzu ana samun tsaiko wajen fara tattara sakamako a jihohin arewacin kasar.

  17. An fara tattara sakamakon zaben jihar Abia

    An fara tattara sakamakon zaben gwaman jihar Abia. Za ku iya garzayawa shafin Facebook na BBC Igbo, idan kuka latsa nan.

  18. An fara korafi a Kano

    BBC

    Wakilin jam'iyyu da sauran jama'ar da ke cibiyar tattara sakamakon zabe sun fara korafi saboda tsaiko da ake samu na rashin fara tattara sakamakon a kan lokaci.

    A yanzu haka akwai sakamako na kananan hukumomi 20 na jihar ana jiran a gabatar dasu.

    An bayyana cewa za a fara tattara sakamakon ne da misalin karfe tara na safe.

    A yanzu haka an shafe sa'o'i biyu a kan lokacin da aka saka za a fara tattara sakamakon.

  19. An fara tattara sakamakon zaben jihar Legas

    An fara tattara sakamakon zaben gwaman jihar Legas. Za ku iya garzayawa shafin Facebook na BBC Yoruba, idan kuka latsa nan.

  20. An kai sakamakon zaben kananan hukumomi shida na Benue

    Kananan hukumomi shida ne suka kai sakamakon zabe dakin da za a kirga kuri'u a birnin Makurdin jihar Benue.

    Kananan hukumomin sun hada da Ogbadibo da Gwer ta yamma da Gwer ta Kudu da Oju da Ohimini da kuma Agatu.

    Zaben Nigeria