Yadda wata tsohuwa ke jefa kuri'arta a Bayelsa
Wata tsohuwa kenan da aka goyo a baya don ta kada kuri'a a wata rumfa a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa.

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.
Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau
Wata tsohuwa kenan da aka goyo a baya don ta kada kuri'a a wata rumfa a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa.

Bidiyon yadda wasu a mazabar Garko da ke jihar Gombe suka koka kan yadda suka samu karancin kayan zabe a mazabarsu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar kuma wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar ya ce zai amince da sakamakon zabe idan ya ci ko ya fadi.


Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kuma dan takarar jam'iyyar APC a jihar a yayin da yake kokarin jefa kuri'arsa,
A kokarin da hukumar EFCC take yi na dakile sayan kuri'a, hukumar ta yi nasarar damke wani mai suna Abdulkareem Abdulsalam a ya yin da yake raba kudi a ranar zabe a jihar Kwara
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Wani fitaccen dan siyasa a Legas Segun Adewale ya wanke wakiliyar BBC da mari.
Wakiliyar ta BBC mai suna Ajoke da ke sashen turancin pidgin ta bayyana cewa dan siyasar ya kai mata hari ne bayan ta ganshi yana raba Naira dubu 1 ga masu zabe.
Bayan ya mare ta 'yan barandansa sun karbe mata waya a wannan lokaci, sai daga baya 'yan sanda suka kawo mata dauki.
Adewale dan siyasa ne a Legas da a baya ya yi kokarin zama gwamna a jihar Ekiti.
Kawo yanzu ba a ji ta bakin dan siyasar ba
Gidim Bogo akwati mai lamba 022, mazabar Garko, Akko, har yanzu ba a fara kada kuri'a sakamakon karancin kuri'u.
Mutum 705 za su yi zabe a akwatin amma takardar kuri'u 500 ne aka tanada.
Mallam Muhammadu Aji Ladan, yace sun dakata da zaben, domin katin zaben basu isa ba. Sama da mutum 20 ne suka fara zabe daga baya aka dakatar gudanar da aikin.


Ya'u Jibrin na sauraren labarai kan yadda ake gudanar da zabe a lokacin da yake kan layi zai kada kuri'a.

El Rufa'i na kan layi zai yi zabe a mazabarsa a unguwar Sarki a jihar Kaduna.

An soma kada kuri’a a rumfar zabe ta Makama Development Area dake birnin Bauchi


Rashin zuwan wakilan jam'iyu ya sa ba a fara tantance masu zabe a wata makarantar Firamari a birnin Lafiya a jihar Nasarawa.


Wasu masu kada kuri'a na jiran a fara zabe a mazabar Galadima a Birnin Kebbi.

Usman Adamu da wasu mutane na sauraren sashen Hausa na BBC a mazabar Ndabagi a Katungu a jihar, Makurdi.

Daya daga cikin jihohin da ba za a gudanar da zaben gwamna cikinta a yau ba, ita ce Kogi wadda ke yankin tsakiyar arewacin Nijeriya.
Ko da yake, jama'ar jihar ba za su yi zaben gwamna ba, amma za su fita rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin jihar.
Bayanai dai sun ce ana zabar 'yan majalisar jiha guda 25 a cikin kananan hukumomi guda 21, inda wasu kananan hukumomin kamar Lokoja ke fitar da 'yan majalisa guda biyu.
