El Rufa'i ya lashe Lere, Sakamakon zaben gwamnan Kaduna
Jam'iyyar APC ta gwamna El Rufa'i ta lashe zabe a karamar hukumar Lere da kuri'a 71,056, yayin da jam'iyyar hamayya ta PDP ta samu kuri'a 45,215.
Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.
Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau
Jam'iyyar APC ta gwamna El Rufa'i ta lashe zabe a karamar hukumar Lere da kuri'a 71,056, yayin da jam'iyyar hamayya ta PDP ta samu kuri'a 45,215.
Abba Kabir Yusuf ya na Jam'iyyar PDP ya yi nasara a karamar Hukumar Minjibir da kuri'a 17,952, yayin da Gwamna Ganduje na APC ya samu kuri'a 17,707.

Tambuwal ya ci zabe a karamar hukumar Sokoto ta arewa da kuri'a 35,030, yayin da APC ta samu kuri'a 31,230.
Sokoto na jan hankali, yayin da PDP me mulki ke fuskantar barazana daga babbar jam'iyyar hamayya APC.

Jam'iyyar APC ta yi nasara a karamar Wamakko da kuri'a 34,834, yayin da PDP ta samu kuri'a 26,171.

Jam'iyyar APc ta lashe karamar hukumar Lafia da kuri' 70,451, yayin da PDP ta samu 18,827.
Dan takarar APGA, Labaran Maku shi ne na biyu da kuri'u 35,844.
Jam'iyyar APC ta lashe zabe a karamar hukumar Gada a jihar Sokoto da kuri'a 25,433, yayin da PDP ta samu kuri'a 20,262.

Asalin hoton, @AWTambuwal
Jam'iyyar APC ta lashe karamar hukumar Birnin Gwari da kuri'a 32,292, yayin da PDP ta samu kuri'a 16,901.
APC ce kuma ta lashe Sabon Gari da kuri'a 57,655, yayin da PDP ta samu kuri'a 25,519.
Kawo yanzu jam'iyyar PDP ke kan gaba a jihar Kaduna, yayin da ya rage a bayyana sakamakon kananan hukumomi shida daga cikin 23 a jihar. Zaria da Kaduna ta kudu na cikin kananan hukumomin da ba a bayyana sakamakonsu ba.

Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukumar Dawakin Kudu da kuri'a 30,901, yayin da APC ta samu kuri'a 25, 657.

Jam'iyyar APC ta lashe karamar hukumar Doguwa da kuri'a 20,696, yayin da PDP ta samu kuri'a 12,642.
Jam'iyyar APC ta lashe karamar hukumar Goronyo da kuri'a 20,867, yayin da PDP ta samu kuri'a 19,915.

Jam'iyyar APC ta lashe zabe a karamar hukumar Ganye da kuri'a 19,063, yayn da PDP ta samu 17,809.
PDP ce ta lashe Karamar hukumar Jada da kuri'u 20,076, yayin da APC ta samu 18,006
Jam'iyyar APC ta fadi a karamar hukumar Zangon Kataf inda ya samu kuri'u 13,448, yayin da kuma PDP ta samu kuri'u 87,546
APC ta kuma fadi a karamar hukumar Sanga da kuri'a 20,806, jam'iyyar hamayya kuma ta PDP ta samu kuri'a 21,226
Jam'iyyar APC ta lashe karamar hukumar Tudun Wada da kuri'u 27,917, yayin da PDP ta samu kuri'u PDP 21,556.

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai
Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukumar Gwale a Kano inda ta samu kuri'u 41,591 sai kuma jam'iyyar APC ta samu kuri'u 23,871.
Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukumar Warawa da ke jihar Kano da kuri'u 15,114 inda jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta samu kuri'u 14,599.

Asalin hoton, Instagram/ @ademolaniran
Dan takarar gwaman jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP Jimi Agbaje ya yi wa dan takarar APC Sanwo-Olu murna ta waya bayan ya lashe zabe