Mai Mala Buni ya lashe zabe a Yobe, Sakamakon zaben gwamnan Yobe
Hukumar INEC ta tabbatar da Maimala Buni na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Yobe inda ya doke abokin hamayyarsa Omar Iliya na PDP.
Maimala Buni ya samu jimillar kuri'a 444,013 yayin da Iliya na PDP ya samu yawan kuri'u 95,703 daga jimillar kuri'a 560 ,492 da aka kada.













