Yadda aka kwace sakamakon karamar hukumar Nasarawa - Baturen zabe
Baturen zabe na karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ya bayyana abubuwan da suka faru har aka kwace sakamakon karamar hukumar Nasarawa.
Jami'in ya shaidawa taron tattara sakamakon zaben gwamnan jihar cewa wasu ne suka kai masu hari lokacin da suke jiran sakamakon mazabar Gama.
Ya bayyana cewa yana zaune kawai ya ji an dake shi ta baya sannan aka dauke sakamakon, abinda ya kawo hargitsi a dakin tattara sakamakon.
Ya ce hakan ya sa dole suka gudu domin tsira da ransu.
Ya kara da cewa, sakamakon mazabar Gama ne ya haifar da tsaiko wajen hada sakamakon karamar hukumar Nasarawa a Kano.











