Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

  2. Ana shirin ci gaba da sanar da sakamakon zaben Kano

    Hukumar zabe ta jihar Kano na shirin ci gaba da sanar da sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar.

    Tun a ranar Lahadi aka fara sanar da sakamakon zaben da aka yi zuwa tsakar dare daga baya aka samu hatsaniya kan sakamakon karamar hulkumar Nasarawa.

    Hakan ne ya sa hukumar ta yi taro da masu ruwa da tsaki suka cimma matsaya kan yadda za a kirga kuri'un na karamar hukumar.

    Kawo yanzu cikin kananan hukumomin jihar Kano 44, karamar hukumar Nasarawa ce ta rage, sannan a bayyana wanda ya zama zakara.

  3. Shin 'yan sanda sun saki mataimakin gwamnan jihar Kano?, Zaben gwamnan Kano

    Har yanzu mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, yana hannun 'yan sanda, kamar yadda kakakin rundunar a jihar ya tabbatarwa BBC.

    'Yan sanda sun kama Gawuna mataimakin gwamnan Kano da kuma kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo.

    Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar ne bayan da suka yi kokarin tayar da rikici a Nasarawa, karamar hukumar da ta rage a kammala tattara sakamakon zaben gwamna a Kano.

  4. Yaushe INEC za ta sanar da sakamakon zaben Kano?, Sakamakon zaben gwamnan jihar Kano

    Mai magana da yawun hukumar INEC a jihar Kano, Farfesa Garba Lawal, ya shaida wa BBC cewa suna ci gaba da tattaunawa a halin yanzu kuma za su sanar da manema labarai lokacin da za a koma don tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa da ta Ajangi wadan da suka rage.

    Daga nan ne kuma ake sa ran za a sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar a karshe.

  5. Muna kawo muku labarai kai tsaye a BBC Hausa Facebook

  6. An yaga sakamakon zaben jihar Imo

    A ranar Litinin ne hatsaniya ta barke a dakin bayyana sakamakon zaben gwamna da na majalisu a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

    A lokacin da ake tsaka da bayyana sakamakon wasu kananan hukumomi ne wani wakilin jam'iyya ya tashi ya je teburin da takardun da ake karanta sakamakon zabe, nan da nan ya damka ya kuma yaga su.

  7. Zaben jihar Adamawa bai kammala ba - INEC

    Jami'in zabe na jihar Adamawa Farfesa Andrew Haruna ya ce zaben jihar Adamawa bai kammala ba.

    Baturen zaben ya ce an soke wasu zaben da aka yi a rumfuna 44 ko kuma ba a kada kuri'u a wasu wuraren ba.

    Ya kuma kara da cewar sun yi hakan ne saboda kuri'un da aka soke suna da yawa hakan zai yi tasiri ga masu yin takara.

  8. Za a bayyana sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa ta Kano

    Babban jami'in zabe na jihar Kano, Farfesa Shehu Riskwa ya ce za a sanar da zaben karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano idan an kirga kuri'un mazabun karamar hukumar daya bayan daya.

    An cimma hakan ne bayan da aka kammala taron masu ruwa da tsaki, inda suka amince da hukuncin da zai kai a bayyana sakamakon zaben karamar hukumar ta Nasarawa.

  9. Za a sake tattara sakamakon Nasarawa a Kano, Sakamakon zaben gwamna a Kano

    Shugaban hukumar zabe na jihar Kano Farfesa Shehu Riskwa ya ce za su yi kokarin tattara sakamakon karamar hukumar Nasarawa da ake zargin bangaren gwamnati da yaga takardun zaben ta hanyar tattara sakamakon mazabu.

    Yanzu haka shugaban hukumar zaben na Kano da Babban jami'in tattara sakamakon zaben jihar suna ganawa da jami'an tsaro kan batun.

  10. INEC ta ce ba a kammala zaben Adamawa ba, Sakamakon zaben gwamna a Adamawa

    Hukumar zabe a jihar Adamawa ta bayyana sakamakon zaben Adamawa a matsayin wanda ba a kammala ba bayan soke zaben wasu mazabu inda ta bukaci a sake zaben.

    PDP ce kan gaba da yawan kuri'u fiye da jam'iyyar APC da ke mulki a jihar.

  11. Zaben Jihar Filato bai kammala ba - INEC

    Baturen zabe na jihar Filato ya bayyana zaben gwamna a matsayin wanda ba a kammala ba saboda adadin kuri'un da APC ta wuce PDP da su, ya gaza adadin kuri'un da aka soke.

    Yanzu za a gudanar da sabon zabe a duk rumfunan zaben da aka soken a cikin kwanaki 21.

  12. INEC ta ce ba a kammala zabe a Sokoto ba, Sakamakon zaben gwamnan Sokoto

    Hukumar zabe ta bayyana zaben Sokoto a matsayin wanda ba a kammala ba bayan soke zaben mazabu 136 da ke da yawan masu kada kuri'a sama da 75,000.

    Sakamakon da aka bayyana, Gwamna mai ci Aminu Tambuwal na PDP ne ke kan gaba da kuri'a 489,558, yayin da Ahmed Aliyu na APC ya samu kuri'a 486,145, kusan ratar kuri'a 3,413 a tsakaninsu.

  13. Tambuwal ya sha kaye a Shagari da Illela, Sakamakon zaben gwamnan Sokoto

    Jam'iyyar APC mai hamayya ta lashe zabe a Shagari da kuri'a 19,414 yayin da PDP mai mulki a jihar ta samu kuri'a 17,959

    Haka ma APC ta lashe karamar hukumar Illela da kuri'u 25,908, yayin da PDP ta samu kuri'a 20,370.

  14. 'Yan sanda sun kama mataimakin gwamnan Kano, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    'Yan sanda sun kama Gawuna mataimakin gwamnan Kano da kuma kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo.

    Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar ne bayan da suka yi kokarin tayar da rikici a Nasarawa, karamar hukumar da ta rage a kammala tattara sakamakon zaben gwamna a Kano.

  15. Jami'an EFCC a wajen tattara sakamakon Kano

  16. Karamar hukumar Nasarawa ta rage a Kano, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Yanzu karamar hukumar Nasarawa ce ta rage a kammala bayyana sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

  17. An dakatar da bayyana sakamako a Kano, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Hukumar zabe a Kano ta tafi hutu daga bayyana sakamakon zaben gwamna da take tattarawa daga kananan hukumomi har sai zuwa karfe hudu na safe za'a dawo.

  18. Ganduje ya sha kaye a Fagge, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Dan takarar PDP ya doke Ganduje a karamar hukumar Fagge a Kano.

    PDP ta samu kuri'a 27,344, yayin da APC ta samu kuri'a 18,370.

  19. Abba Kabir na kan hanyar zama gwamnan Kano, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Dan takarar PDP Abba Kabir Yusuf ya sha gaban gwamna Ganduje na APC yayin da ya rage a bayyana sakamakon kananan hukumomi guda biyu.

  20. Ganduje ya sha kaye a Kano Municipal, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP ya doke Ganduje na APC a karamar hukumar Kano Municipal.

    Jam'iyyar PDP ta lashe zaben ne da kuri'a 57,781, yayin da APC ta samu kuri'a 32,394