Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Yadda aka kwace sakamakon karamar hukumar Nasarawa - Baturen zabe

    Baturen zabe na karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ya bayyana abubuwan da suka faru har aka kwace sakamakon karamar hukumar Nasarawa.

    Jami'in ya shaidawa taron tattara sakamakon zaben gwamnan jihar cewa wasu ne suka kai masu hari lokacin da suke jiran sakamakon mazabar Gama.

    Ya bayyana cewa yana zaune kawai ya ji an dake shi ta baya sannan aka dauke sakamakon, abinda ya kawo hargitsi a dakin tattara sakamakon.

    Ya ce hakan ya sa dole suka gudu domin tsira da ransu.

    Ya kara da cewa, sakamakon mazabar Gama ne ya haifar da tsaiko wajen hada sakamakon karamar hukumar Nasarawa a Kano.

  2. Ba mu saba doka ba wajen hada sakamakon Nasarawa- INEC

    Shugaban hukumar INEC a Kano na bayani kan abubuwan da suka faru a karamar hukumar Nasarawa wajen tattara sakamako.

    Shugaban hukumar Farfesa Shehu Riskwa ya ce ala tilas suka yi amfani da wata hanya wajen tattaro sakamakon karamar hukumar Nasarawa bayan da wasu suka yaga takardar sakamakon daya tilo.

    Bayanin nasa ya biyo bayan korafin da wasu wakilan jam'iyya suka yi a wajen tattara sakamakon kan wani kuskure da suke zargin an yi.

    Ya kalubalancin duk wadanda suke zauren tattara sakamakon da su kawo inda aka saba doka.

  3. An ci gaba da karbar sakamakon zaben Kano

  4. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

  5. A sanar da sakamakon zaben Kano kafin Sallar Isha'i - Wakili

    Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano Mohammed Wakili ya ce a sanar da sakamakon zaben jihar Kano kafin Sallar Isha'i.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun kwan gaba kwan baya dangane da bayyana sakamakon zaben jihar.

  6. An hana daukar tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa kai tsaye

    Ku yi hakuri da katse kawo muku ci gaban sakamakon jihar Kano. Hakan ya faru ne saboda an hana kowa yada abun da ke faruwa a dakin tattara sakamakon a yanzu haka. Amma za mu dawo da zarar an fara bayyana sakamakon.

  7. ''Aiki ya kawo ni sai dai ku kashe ni''- kwamishinan zaben Kano

  8. Labarai da dumi-dumi, INEC ta bayyana zaben Benue a matsayin wanda ba'a kammala ba

    Hukumar INEC ta bayyana zaben gwamna na jihar Benue a matsayin zaben da ba a kammala ba.

    Wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta bayyana zaben jihohin Sokoto da Adamawa da Filato da Bauchi a matsayin zaben da ba a kammala ba.

    An dai gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 29 na kasar a ranar 9 ga watan Fabrairu.

  9. Me ke faruwa da sakamakon zaben Kano ne?

    Har yanzu dai ana ci gaba da jiran sakamakon zaben jihar Kano tun bayan da aka samu tsaiko wajen gabatar da sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa da ke jihar.

    A safiyar yau Litinin ne dai mai magana da yawun hukumar INEC a jihar Kano, Farfesa Garba Lawal, ya shaida wa BBC cewa suna ci gaba da tattaunawa kuma za su sanar da manema labarai lokacin da za a koma don tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa.

    Sai dai har zuwa yanzu babu wani karin bayani dangane da cikakken sakamakon zaben jihar da kuma lokacin da za a ci gaba da bayyana shi.

  10. An ci gaba da karbar sakamako a Taraba bayan takaitaccen hutu

  11. Rundunar sojojin Najeriya ta nisanta kanta bisa zargin da ake yi mata

    Rundunar sojojin Najeriya ta nisanta kanta da wani labari da wata kafar yada labarai ta intanet ta wallafa inda kafar ta zargi rundunar sojin kasar da yin katsalandan a zaben jihar Ribas.

  12. An saki mataimakin gwamnan Kano

    An saki mataimakin gwamnan jihar Kano bayan an kama shi ranar Lahadi da dare bisa zarginsa da yunkurin tafka magudin zabe.

    A yanzu dai an sake shi ne sakamakon kariya da yake da ita a matsayinsa na mataimakin gwamna.

    Sai dai sauran mutanen da aka kamasu tare na nan tsare.

  13. Kwamishinan 'yan sandan Kano kan kama mataimakin gwamnan

  14. Yadda ake murnar lashe zaben jihar Nasarawa

  15. Ana zanga-zanga a Fatakwal

  16. El Rufa'i ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna

    Farfesa Muhammad yahuza Bello kenan a lokacin da yake bayyana zaben gwamnan jihar Kaduna.

    Nasiru El Rufa'i na jam'iyyar APC shi ne ya lashe zaben da kuri'a 1,045,427, yayain da Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 814,168.

  17. Ko kun san jihohin da ba a kammala zabe ba?

  18. Ana taya zababben gwamnan Gombe murna

    Zababben gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya da mataimakinsa Dakta Manaseh Jatau ke karbar sakon taya murna daga 'yan uwa da abokan arziki a kan lashe zabe.

  19. Kwankwaso ya yi kira a zauna lafiya

    Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga jama'ar jihar da su zauna lafiya.

    Ya bayyana haka ne ta wani sakon murya da ya fitar inda ya ja hankalin 'yan jam'iyyarsa da kuma sauran jama'ar jihar da idan aka sanar da sakamakon zabe cewar dukannin al'umma su zauna lafiya.

    Kuma ya ce bayan sanar da sakamakon kada magoya baya su fito su yi abin da zai cutar da su, musamman masu wasa da abin hawa ko kuma abin da zai cutar da su.

  20. Ganduje ya yi kira da a zauna lafiya

    Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga jama'ar jihar da a zauna lafiya.

    Ya bayyana haka ne a wata sanarwa ta kafar yada labarai ta kwamishinan watsa labarai na jihar Malam Muhammad Garba.

    Gwaman ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al'ummar jihar da su sa ido kan 'ya'yansu da jama'arsu, su kuma tsawatar yayin da aka ga suna kokarin aikata ba daidai ba ko kuma daukan doka a hannunsu.