Buhari ya kawo Legas
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai labari a zaben shugaban kasa a Legas.
Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 580,825 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 448,015.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai labari a zaben shugaban kasa a Legas.
Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 580,825 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 448,015.
Shugaban Najeria Muhammadu Buhari ya lashe zaben Shugaban kasa a jihar Bauchi inda ya samu kuri'u 798,428 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu 209, 313.
'Yar majalisar dattawa daya tal daga arewacin Najeriya daga jihar Adamawa ta sha kayen ne a hannun wani dan jam'iyyar PDP. Ita kuma ta yi takarar ne a jam'iyyar APC.
Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata George Akume ya sha kaye a kujerarsa ta Sanatan Benue, Arewa maso yamma.
Dan takarar PDP Orkev Jev ne ya yi nasara.
Orkev Jev na PDP: 157,776
George Akume APC: 115,422
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Adamawa inda ya samu kuri'u 410,078 sai kuma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na APC ya samu 378,078.
Atiku Abubakar dan takarar jam'iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a jihar Oyo inda ya samu kuri'u 366,690 sai kuma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 365,229.
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Anambra inda ya samu kuri'u 524,738 sai kuma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu 33,298.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya yi nasara a jihar Kaduna a zaben shugaban kasa inda ya samu 993,445, yayin da Atiku Abubakar kuma na jam'iyyar PDP ya samu 649,612.
Hukumar zaben Najeriya ta bayyana shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a jihar Jigawa inda ya samu kuri'u 794, 738, yayin da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 289, 895.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Naija da kuri'u 612,371 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu 218,052.
Hukumar zaben Najeriya ta dawo bakin aikin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar. A yanzu haka an gayyaci baturiyar zabe da kwamishinan zabe na jihar Naija domin gabatar da sakamakon zaben jihar na shugaban kasa.
Malam Mahmud Abubakar kenan daga jihar Adamawa inda ya kasa ya tsare dab da akwatin rediyonsa yana sauraren yadda hukumar zaben Najeriya, INEC ke karba da bayyana sakamakon zabe.
Hukumar zaben Najeriya ta ce ranar Talata za ta ci gaba da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.
Da daren Litinin ne shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da dakatar da tattara sakamakon zaben shugaban kasa zuwa Talata.
Ya ce za a sake bude cibiyar tattara sakamakon da misalin karfe 10 na safe.
Yanzu sakamakon jihohi 12 hadi da Abuja babbar birnin Tarayya aka sanar.
Dan takarar jam’iyyar APC Muhammadu Buhari ya yi nasara ajiha bakwai, yayin da abokin hamayyarsa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe jihohi biyar.
Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura da tsohon gwamnan jihar Sanata Abdullahi Adamu , dukkansu na jam'iyyar APC sun yi nasara a zaben majalisar dattawan jihar.
Baturen zaben yankin Farfesa Ahmed Yakubu Ashuku ya ce Tanko Almakura ya samu kuri'a 113,156 yayi da abokin hamayyarsa na PDP, Sulaiman Adokwe ya samu kuri'a 104,595.
Kazalika Sanaa Abdullahi Adamu ya samu kuri'a 115,298 yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Bala Ahmed Aliyu, ya samu kuri'a 85,615.
Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, na jam'iyyar APC ya sake yin nasara a zaben majalisar dattawa inda ya samu kuri'a 300, 637 yayin da abokin hamayyarsa na PDP, Kudla Haske, ya samu kuri'a 84, 608, kamar yadda baturen zaben yankin Farfesa Isa Hassan ya bayyana.
Wannan shi ne karo na uku da Sanata Ndume zai wakilci Kudancin Borno a majalisar dattawan Najeriya.
Hukumar zaben Najeriya reshen Zamfara ta ayyana gwamnan jihar Abdulaziz Yari Abubakar a matsayin mutmin da ya yi nasara a zaben kujerar dan majalisar dattawa a mazabar Yammacin Zamfara. Baturen zaben yankin ya ce Gwamna Yari na jam'iyyar APC ya samu kuri'a 153,626 yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Lawan Hassan, ya samu kuri'a 69,293.