Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Yadda mutane ke murnar sake zabar Muhammadu Buhari

  2. Atiku zai kalubalanci Buhari a kotu

    Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce bai amince da sakamakon zaben da aka yi wa Muhammadu Buhari ba.

    Atiku ya ce abin kunya ne da zai kalubalanci zaben a kotu, amma haka ya zama wajibi domin ya ceto dimukaradiyyar Najeria ta ci gaba da dorewa.

  3. Yadda ake murna zaben Buhari a jihar Adamawa

  4. Eunice Atuejide ta yi murna da kuri'un da ta samu

    Eunice Atuejide 'yar takarar shugaban kasa Najeriya a jam'iyyar NIP ta samu kuria 2,248.

  5. Jawabin Muhammadu Buhari bayan lashe zabe

  6. Shugabannin Afirka na taya Buhari murna

    Wasu shagabannin Afirka na taya Muhammadu Buhari murnar lashe zaben Najeriya karo na biyu da zai yi.

    A wata sanarwa da mai bai wa shugaba Buhari shawara na musamman, Femi Adesina ya fitar ya ce Shugaban Ghana, Nana Koffi-Addo da na Niger, Mahamagou Issoufou da Macky Sall na Senegal sun mika sakon taya murna ga Shugaba Muhammadu Buhari.

  7. Kenyatta ya taya Buhari murnar lashe zabe

    Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya taya Muhammadu Buhari murnar zama shugaban kasar Najeria karo na biyu a jere.

    Kenyata ya ce cin zaben da Buhari ya yi alamace ta yadda 'yan Nageria suka amince da jagorancin Buhari domin ya dora kan ayyukan da yake musu domin ci gaban kasa.

    Buhari ya yi nasara ne a kan dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.

  8. Barkanmu da saduwa a shirinmu na kai tsaye

    Sunana Muhammed Abdu zan ci gaba da kawo muku yadda al'umma ke murnar lashe zaben da Muhammadu Buhari ya yi a karo na biyu da zai shugabanci Nigeria shekara hudu.

    Za ku iya bayyana ra'ayinku kan nasarar da Muhammadu Buhari ya yi a shafukanmu na sada zumunta a Facebook da Tuwita da Instagram a BBC Hausa.

  9. Sai an jima, Buhari ya lashe zabe

    A nan za mu dan jinkirta bayanan da muke kawo maku kai-tsaye zuwa har zuwa an jima inda za mu ci gaba.

    Da fatan za ku ci gaba da kasance wa da mu.

    Awwal Janyau ne ke maku sallama.

  10. Zan inganta tsaro da tattalin arziki - Buhari, Buhari ya lashe zabe

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce sabuwar gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta tsaro da bunkasa tattalin arziki.

    A lokacin da yake jawabi a ofishin yakin neman zabensa bayan sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben 2019, ya ce ya kasance mai kaskantar da kai ga sake zabensa da 'yan Najeriya suka yi.

  11. Buhari ya yi jawabi a hedikwatar APC, Buhari ya lashe zabe

    Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ga shugabannin jam'iyyarsa ta APC a ofishin yakin neman zabensa a Abuja bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.

    Nan gaba kadan ake sa ran zai yi wa 'yan kasa jawabi bayan samun nasararsa.

  12. Sanarwar shugaban hukumar INEC, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  13. Buhari na kallon yadda ya ci zabe, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  14. Yadda Buhari ya lashe zabe, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  15. INEC ta tabbatar da Buhari, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Hukumar zaben Najeriya ta tabbatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019

  16. Tinubu ya taya Buhari murna, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu har ya isa fadar shugaban kasa domin taya Buhari murna.

  17. Yadda ake bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  18. Jawabin shugaban INEC kai-tsaye, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  19. 'Matsaloli ba za su hana bayyana sakamako ba', Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Shugaban INEC ya ce matsalolin da aka fuskanta na satar akwatin zabe da tangandar na'urar card reader ba su kai dalilin da zai hana bayyana sakamakon da aka tattara ba na shugaban kasa daga dukkanin jihohin Najeriya 36 da Abuja.

  20. INEC ta dawo zauren bayyana sakamako, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya fara jawabi.

    Ya ce sun yi nazari kan sakamakon da suka tattara musamman korafin wakilan jam'iyyu da kuma matsalolin da aka ci karo da su a zaben.