Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Buhari ya yi zarra a Gombe

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashe zabe a jihar Gombe inda ya samu kuri'u 402,961 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu 138,484.

  2. Buhari ya doke Atiku a jihar Kogi

    Shugaban Najeriya kuma dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari ya lashe zabe a Kogi inda ya samu kuri'u 285,894 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 218,207.

  3. An dakatar da jihar Ondo sai an gama tantancewa

    An dakatar da gabatar da sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Ondo bayan da aka samu kura-kurai wajen karanto sakamakon da baturen zaben ya yi. A yanzu dai shugaban hukumar ya ce sai baturen zabe da kwamishanan zaben jihar ta Ondo sun gama tantancewa sai su dawo su karanta.

  4. Wasu ra'ayoyi daga shafin Twitter

  5. Al-Makura ya kai labari

    Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura ya lashe kujerar sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu da kuri'u 113,156.

    Abokin karawar tasa Sulaiman Adokwe na PDP ya samu kuri'u 104,595.

    Gwamnan dai ya lashe zaben da kuri'u 8,560.

  6. An tafi hutun minti 30 wajen kirga sakamakon zaben Nigeria

    An kirga kuri'un jihohi biyar da suka hada da Ekiti da Nasarawa da Kwara da Osun da baban birnin tarayya Abuja.

    Buhari ya lashe zabukan jihohi hudu, yayin da Atiku ya ci babban birnin tarayya Abuja.

  7. Buhari ya kai labari a jihar Nasarawa a karon farko

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashe zabe a jihar Nasarawa. Wannan ne karon farko da shugaban ya fara lashe zabe a jihar tun bayan da ya fara takara a shekarar 2003.

    Shugaban ya samu kuri'u 289,903 a karkashin jam'iyyar APC sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu 283,847.

    An samu matsalar soke wasu kuri'u a wasu rumfuna a jihar sakamakon hargitsi da kuma kada kuri'a fiye da rajistar masu zabe.

  8. Buhari ya doke Atiku a Kwara

    Buhari ya samu nasarar lashe zabe a jihar Kwara inda ya samu kur'u 308,984 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu 138,184. An samu soke kuri'u a jihar sakamakon kada kuri'a fiye da rajistar masu zabe (over voting) a wasu wuraren da kuma kananan yara da aka samu shaidar cewar sun jefa kuri'a.

  9. Atiku ya samu nasara a Abuja

    Atiku Abubakar ya samu nasarar lashe Abuja babban birnin kasar. Atiku Abubakar na PDP ya samu kuri'u 259,997 sai kuma Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya samu 152,224.

  10. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

  11. Me ke kawo tsaiko wajen bayyana sakamakon zaben shugaban kasa?, Daga Mustapha Musa Kaita

    Tun bayan da aka gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar, tuni 'yan kasar suka kosa domin su ji hukumar INEC ta bayyana sakamakon zabe.

    A wannan zaben akwai kusan jam'iyyu 73 da suke da 'yan takarar shugabancin kasa.

    Masana ko kuma masu sharhi na ganin cewa wannan na daga cikin dalilan da yasa ake samun jinkiri tun wajen tattara sakamakon zabe a matakin jiha zuwa matakin tarayya.

    Domin a duk lokacin da za a gabatar da sakamakon zaben shugaban kasa sai an lissafo sunan ko wace jami'iyya da abinda jam'iyyar ta samu.

    Wani abu da ke kara jawo tsaiko shine rikice-rikicen da aka samu a wasu sassa na Najeriya wanda hakan ya yi sanadiyar samun jinkiri wajen gudanar da zaben a ranar Asabar a wasu sassan kuma sai Lahadi aka gudanar da zaben.

    Wasu wuraren kuma an samu jinkiri wajen kai kayan zabe da ma'aikatan zabe wanda a tarihin siyasar dimokradiyyar Najeriya ba wannan ne karon farko ba.

    A wasu wuraren kuma, samun jinkiri a zaben ya samo asali ne tun matsalar da aka samu da na'urorin tantance masu kada kuri'a watau card readers, domin kuwa na'urorin sun kawo tsaiko wurin gudanar da zabe a wasu sassa na kasar.

  12. Buhari ya isa Abuja

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Abuja babban birnin Najeriya.

    A ranar Jumma'a ne shugaban ya tafi mahaifarsa Daura domin kada kuri'arsa a zaben da aka gudanar na shugaban kasa da kuma 'yan majalisun jihohi da kuma na tarayya.

    Shugaban ya koma babban birnin kasar ne a dai dai lokacin da hukumar zabe ta kasar ke tattara sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi a fadin kasar.

  13. Ba a kammala zaben sanata na Kogi ta gabas ba

    Hukumar INEC ta bayyana zaben kujerar sanata na Kogi ta gabas a matsayin zaben da ba a kammala ba sakamakon samun dumbin kuri'un da suka lalace da kuma tashin hankalin da aka samu. Amma tuni aka gama tattara sakamakon zaben shugaban kasa na jihar kuma ana hanyar kai sakamakon zuwa Abuja.

  14. Labarai da dumi-dumi, An tafi hutu

    Hukumar INEC ta tafi hutu na takaitaccen lokaci dangane da karba da kuma bayyana sakamakon zaben Shugaban kasa.

    Za a ci gaba da misalin karfe 2:30 na rana a agogon Najeriya.

  15. Kai tsaye daga shafin INEC na Twitter

  16. Sakamakon zaben kujerar Sanatan jihar Anambra

    Dr. Uche Lilian Ekwunife ta jam'iyyar PDP ta doke Victor Ume na jam'iyyar APGA a zaben Sanatan tsakiya a jihar Anambra, Ita kuwa Dr Stella Odua ta PDP ta lashe kujerarta ta Sanatar Arewa ta Anambra yayin da Dr Ifeanyi Ubah na YPP ya kayar da Andy Ubah na APC, ya kuma lashe kujerar Sanatan Kudancin Anambra.

  17. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya lashe zaben Osun

    Jami'iyyar APC ta samu kuri'a 347,634 a zaben shugaban kasa yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'a 337,377.

  18. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya doke Atiku a Ekiti

    Shugaban Najeriya Muhammadu na jam'iyyar APC ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na jihar Ekiti.

    Sakamakon zaben da hukumar zaben Najeriya ta bayyana a Abuja ranar Litinin, wanda shi ne na farko, ya nuna cewa Buhari ya samu kuri'a 219,231 yayin da Atiku ya samu kuri'a 154,032.

  19. Kun san sabon Sanata a Yobe?

    Jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujeru uku na 'yan majalisar dattawan jihar Yobe.

    'Yan takarar da suka yi nasara a zaben sun hada da Gwamna Ibrahim Geidam da Sanata Ahmed Lawan da kuma Ibrahim Bomai, wanda ya lashe kujerar siyasa karon farko.

  20. Za a soma bayyana sakamakon zaben Nigeria a Abuja

    Sakamakon zabe na isa babban dakin taro na International Comference Center da ke Abuja, inda za a fadi sakamakon wadanda suka yi nasara a kuri'un da aka kada a ranar Asabar.

    Za a dunga fadar sakamako jiha-jiha har 36 na Nigeria daga baya a hada lissafi sannan a fadi wanda ya zama zakara.