Saraki bai taya dan APC murna kayar da shi ba
Jami'in da ke kula da watsa labarai na Shugaban majalissar dattijai Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya yi watsi da labarin da ake yada wa a kafafen sada zumunta cewar Saraki ya taya dan takarar APC murna kan kayar da shi da ya yi.
A sanarwar da Yusuph Olaniyonu ya fitar a ranar Litinin ta ce nan gaba Saraki zai yi wa jama'a bayani kan dalillinsa na kin taya abokin hamayyarsa murna.