Ana ganin amsa shan kaye daga dan takarar babbar jam'iyyar hamayya zai kara tabbatar da ci gaban dimokuradiyya a Najeriya.
Sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben bayan kammala tattara sakamakon.
Shugaban mai shekara 76 ya kayar da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u kusan miliyan hudu.
A zaben 2015 da ake ganin mafi zafi a tarihin siyasar Najeriya inda a karon farko aka kada shugaba mai ci, an kawo karshen zaben cikin ruwan sanyi.
Tun kafin sanar da sakamakon zaben ne tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya kira Muhammadu Buhari mai ci na yanzu ya taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa.
A zantawa da suka yi ta wayar tarho, Jonathan ya amsa shan kaye a zaben 2015 tare da taya Buhari murnar nasarar lashe zabe.
Ana ganin yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da aka sanya wa hannu a lokacin ita ce ta yi tasiri har shugaban kasa mai ci nan take ya amsa shan kaye.
A zaben 2019 yanzu hankali zai koma kan dan takarar jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, kan ko zai amsa shan kaye kamar yadda Jonathan ya yi a zaben 2015.
Ko da yake, Jam'iyyar adawa ta PDP, wacce Atiku ya yi wa takara, ta yi watsi da sakamakon zaben.
Tun a sakamakon farko-farko da aka fara bayyanawa jam'iyyar ta yi zargin cewa akwai kura-kurai da aka tafka tare da zargin jam'iyya mai mulki ta APC da yin magudi.
Amma zai zo da mamaki tare da rufe bakin jam'iyyar PDP idan har Atiku ya amsa shan kaye tare da taya abokin hamayyarsa shugaba Buhari murna.