Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019
Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu
Buhari ya lashe Kebbi, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya lashe zabe a jihar Kebbi da kuri'u 581,552, yayin da babban abokin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar ya samu kuri'a 154,282
Ana bayyana sakamakon Kebbi, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Yanzu jihohi biyu suka rage a kammala bayyana sakamakon na dukkanin jihohin Najeriya da Abuja
Buhari ya lashe Sokoto, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya lashe zabe a jihar sokoto.
Buhari ya samu kuri'a 490,333 yayin da Atiku ya samu kuri'a 361,604.
Jihohi hudu suka rage a kammala, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Yanzu jihohi hudu suka rage a kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar.
jihohin da ake dako sun hada da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Rivers.
Atiku ya doke Buhari a Bayelsa, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Atiku Abubakar na PDP ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Delta.
Atiku ya samu kuri'a 197,933 yayin da ya doke shugaba Buhari na APC wanda ya samu kuri'a 118,821
Atiku ta lashe jihar Delta, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Dan takarar PDP Atiku Abubakar ya doke Buhari a jihar Delta.
Atiku ya samu kuri'a 594,068 yayin da Buhari ya samu kuri'a 229,294
Buhari ya doke Atiku a Borno, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Buhari na jam'iyyar APC ya lashe jihar Borno da kuri'a 836,496, inda ya doke Atiku na PDP wanda ya samu kuri'a 71,788.
Atiku ya doke Buhari a Akwa Ibom, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya lashe jihar Akwa Ibom da kuri'a 395.832, yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC shugaba buhari ya samu kuri'a 175,429.
Atiku ya lashe Cross River, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya lashe Cross River da kuri'a 295,737 inda ya kada Buhari na APC da ya samu kuri'a 117,307
Shin Atiku zai iya kamo Buhari kuwa?, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Shugaba mai ci Muhammadu Buhari na Jam'iyyar APC ne ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya da aka bayyana kawo yanzu.
Bayan bayyana sakamakon jihohi 28 hadi da Abuja, Buhari ya samu sama da kuri'a miliyan 12, yayin da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya samu kuri'u sama da miliyan takwas da rabi.
Sakamakon ya nuna Buhari ya ba Atiku ratar kuri'u kusan miliyan hudu, yayin da ya rage a bayyana sakamakon jihohi tara.
Wasu na ganin yana da wahala Atiku ya iya kamo Buhari bayan bayyana wasu sakamakon manyan jihohin da ke da kuri'u da yawa da suka hada da Lagos da Kano da Kaduna da Katsina.
Ku kalli yadda jama'a ke lissafin alkalumman sakamakon zabe, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Hankalin 'Yan Najeriya ya karkata ga sakamakon zaben Najeriya.
PDP ta bukaci a dakatar da kirga kuri'u, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Jam'iyar PDP mai hammaya a Najeriya ta bukaci hukumar zabe INEC da ta tsayar da tattara sakamako da take yi har sai an nuna wa jam'iyu yawan alkaluman da na'urar da ta tantance jama'a a rumfunan da aka yi zabe.
A wata sanarwa da PDP ta fitar, ta yi zargin cewa an sauya alkaluman da na'urar tantance masu zabe ta nada tun farko domin yin magudi daga wasu jihohin da APC ke mulki.
Shugaban jam'iyar PDP, Prince Uche Secondus ya ce sun mika bukatarsu ga shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahnood Yakubu inda suke bukatar da a soke zaben jihar Yobe da Nasarawa da Borno, sannan suka bukaci a sake zabe a jihohin.
Atiku ya lashe jihar Taraba
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Taraba inda ya samu kuri'u 374,743 shi kuwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na APC ya samu 324,906.
Buhari ya lashe jihar Katsina
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na APC ya samu nasarar lashe jihar Katsina a zaben shugaban kasar Najeriya bayan da ya samu kuri'a 1,232,133 yayin da Dan takarar PDP Atiku Abubakar na PDP ya samu 308,056.
Buhari ya yi wa Atiku fintikau a Kano, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na APC ya samu nasarar lashe jihar Kano a zaben shugaban kasar Najeriya bayan da ya samu kuri'a 1,464,768, yayin da Dan takarar PDP Atiku Abubakar na PDP ya samu 391,593.
Atiku ne ya lashe jihar Plateau
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Plateau inda ya samu kuri'u 548,665 shi kuwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na APC ya samu 468,555.
Atiku ya doke Buhari a Benue
Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a jihar Benue da kuri’u 356,817 sai kuma Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 347,668.
Atiku ya lashe Edo
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya samu nasara a zaben shugaban kasa a jihar Edo inda ya samu kuri'u 275,691 sai kuma shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 267,842.
Buhari ya doke Atiku a Ogun
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a jihar Ogun inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'u 281,762 sai kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu 194,655.